Showing 39001 words to 42000 words out of 95753 words

Chapter 14 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

hankslinka wannan duk sharrin jama'a ne kar ka manta kana tare
da mahassada ko su zasu aikata maka wannan Abu."



Mik'ewa yayi yana kai wa da kawo wa a farlor yace." Kaje ka tsaurara bunkice ka gano gaskiyar
abun shin abunda na karanta jikin jaridar nan hakane Mimi Bata da uba shegiya ce kamar
yanda suka fad'a shin hakane wannan gida dasu ke ciki na company ne kaje ka tsaurara
bunkice ka gano wane company mahaifin Asma'u yayi a aiki a sharada." Rambo yace." Insha Allahu Sir ka kwantar da hankalinka duk sharrine domin da d'aga maka
hankali kuma a tozarta ka a don duniya. " Wayar shi tayi kara Rambo ya mik'o masa da sauri,
kunnenshi ya kara wayar a dake yace." Salamu alaikum. " Kawu Yunsu Ya amsa cike da tashin
hankali yace." Yaro mai halin manya na bugo ne in kwantar maka da hankali kan abunda
jama'ar gari da kafafan yad'a labarai suke shela a kai, ina so in tabbatar maka da cewar mu 'yar
mu Asma'u tsarkakkiya ce da Ubanta kuma muna da nasaba me kyau duk fadin koki da cikarta
babu Wanda bai san mahaifinmu Malam Sulaiman mai ishiriniya ba, idan kana so kattabar da

haka ka sanya ayi maka bunkice."" Muryar shi a sama yace." Babu bunkice da zan sanya ayi
min akan Asma'u na yadda da ita Dari bisa Dari, kokwantona yanzu akan Mimi yake shin da
gaske ne mahaifin ta ya gudu ya barta ko kuwa."?


Kawu Yunusa yace." Hakane tun bayan haihuwar ta ya gud ..... Katse shi kafin ya karasa
yace." Tabbata kenan abunda nake zargi." Kawu Yunusa har yayi niyyar cewa gaskiya ne sai
kuma ya fasa tunowa da yayi da maganar Asma'u inda take fadin bata har indai Mimi bata aure
shi ba itama baza ta aure shi ba, yayi saurin cewa." Yarinyar 'yar sunna ce sai dai ubanta ya
hofintar da ita ne shine mahaifiyar Asma'u ta dauke ta ta raine ta.

Amjadu ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin"Yau saura kwana nawa d'aurin aure."? Kawu yace."
Kwana shida ne." Shiru na minti biyu sannan yace." Yau muna laraba ko."? Kawu yace.'k'warai
kuwa" Yace. "Idan Allah ya kaimu jibi d'aurin aure insha Allahu Ku zauna cikin shiri daga yanzu
a fara shiri duk wani Abu da ake bukata kayi min magana kar ka samu damuwa. Kawu yaji wani irin sanyin dad'i ya shiga ransa yace."Insha Allahu komai za a yi kamar yanda
kake so Allah ya kara arziki da wadata." Amjad yace." Ameen suma Ameen ina so in zauna da
Waliyin ita Mimi domin akwai wasu muhiman tambayoyi da zanyi mishi." Kawu yace." Ai babu
damuwa yana aiki ne a babbar makarantar ta PCE nan kofar famfo." Gyada kansa yayi yace."
Insha Allah zan same shi a ofis din." Nan suka yi sallama da juna.


Wanka ya shiga a gurguje ya kimtsa jikinsa ya futo sai zabga kamshi yake kamar ko da yaushe
, fuskar sa a daure ya futa, abun mamaki da daure kai can ya hango 'yan jarida suna rigima da
masu gadi gurin wai lallai sai sun shigo Estate din."

Mota ya nufa zuciyarsa nayi masa suya wato yanzu za a sanya shi a bakin duniya kenan
Saboda ana zargin zai auri Shegiya mata uba, shi yarinyar da suke maganar ta ba su San ba
sonta yake ba, kaddara ce kawai auran su, da ita zasu sashi a duniya duk Wanda yayi masa
tunon asiri nan bai kyauta masa ba.

Ganin shi ya futo yasa suka dinga kokawar shiga cike da b'acin rai yace." Doh doh kayi kamar
zaka bi takan 'yan iska da mota." Aikuwa Doh_ doh ya fafuri motar da guda! Lokaci guda suka
watse amma duk da haka wasu daga cikinsu sai da suka dinga d'aukar motar tashi hoto masu
vedio ma nayi kamar bala'i suka bi motar da gudu suna fadin"Yallab'ai me zaka ce a game da
jita-jitar da jama'ar gari suke a kanka wai zaka auri shegiya Mara Uba shin hakane ko karya ne,
Yallab'ai muna so mu ji ta bakin ka."

Ko kallonsu bai yi ballanta su saka ran zai amsa musu motar ta b'acewa ganinsu. Sai da sukayi
nisa sosai sannan yace." Doh ka kaini makarantar FCE Yanzu." Doh yace." OK Sir. motar na
shiga makarantar samari da 'yan mata suka yi mata Caa! Da ido kasamcewar duk inda motar
shi take an Santa saboda tambarin da yake bayanta. Doh.. Yayi parking inda aka tana da kana

ya futo da sauri ya bude masa kofar motar.


A hankali yace." Ka shiga ciki makarantar ka bunkita min ofis din Muktar Inuwa Gyaranya."
Shine ai nihin sunan Kawun Mimi wato Baban su Munnu kenan. Nan da nan doh-doh ya tafi
cika umarnin da aka bashi


*****

Muna cikin tsananin tashin hankali da rud'u tun lokacin da Umma taji labarin abunda jama'ar
gari suke fada a kan Mimi take kuka ta tana fadin"Yarinyar sinna ake shigantawa ni Mariya
Innalillahi kuka take sosai tun muna daurewa har muma muka fara taya ta, Ya Aminu ya shigo
gidan shima ranshi a bace domin yaga sai Wani irin kallo jama'ar gari suke masa sai kace
Wanda yayi sata ko maita Mimi ya kalle ranshi a mutukar bace yace." Kukan karya kike yi Mimi,
ko kin dauka auran Wanda ya shahara a duniya wasa ne? Kin dauka in kin auri Young
millionaire zaki samu irin kwanciyar hankalin da kike so, to bari kiji auran irin su Sai kayi ta
fuskantar kalubale kinga ishara yanzu da Uwar ki da ubanki jama'ar gari suna kiran ki da
shegiya, tom me zakice game da wannan zargin da suke miki, ku sani ga 'yan jarida can a waje
suna kokarin shigowa cikin gidan nan nine na hana su na rufe kofar gidan da sakata. "


Mimi kukan ta ya tsananta ta inda ta fara karkarwa tari ya sark'e ta har tana kokarin kifawa
k'irjinta ta rike tam da hannu biyu sai tari take ga hawaye na zuba daga idonta. Hankali a tashe
nayi kanta ina kuka wurjajan ina ji kamar in tashi in gaggaura Aminu mari, murya ta a sama
nace." Ya Aminu ka k'yaleta mana baka ga tari ya sark'e ta ba."!!!! Ko kallona baiyi ba ya futa
daga rumfar a fusace,!! Ni da Umma muka rike ta sosai muna dukan bayan ta duk mun gigice.!



Wata irin zufa ce take keto wa Baban su Munnu bayan ya gama sauran maganar da Amjadu
yaje masa da ita, to son ya San meye dalilin da yasa Uban Mimi ya gudu ya barta ko zancan da
jama'ar gari suke yi gaskiya ne.". Hankali a tashe Baban su Munnu ya fara magana kamar haka.
"Hak'ika Aishatu yar halak ce mahaifin ta Dan uwana ne cikin mu daya, mu 'yan kano ne gaba
da baya yan Asalin unguwar Gyaranya dake k'aramar hukumar Dala, tun bayan rasuwar Matar
shi wato Aisha mahaifiyar Mimi kenan ya ji zaman garin ya ishe shi bayan sadakar ar'abain ya
tafi Neman kudi a cewar sa, yau shekara goma sha shida kenan, ban sanya shi a idona ba sai
dai labarin sa yana zuwar mana sa'i da lokaci kuma kullum yar shi tana ranshi yana yi mata ake
akai akai, Mariya yar mahaifiyar ta Itace ta dauke ta shayar da ita nonota lokacin tana goyon
'yar ta Asma'u sai ta had'a ta shayar dasu tare babu abunda zamu ce da Mariya domin ta cika
jajurtacciyar macace. Wannan shine ainihin abunda yake faruwa." Kawu ya k'arashe maganar
sa yana goge zufa.!!

Shima Nashi b'angaran wani irin faragaba da fad'uwar gaba ne ya riske shi lokacin da ya gama
jin abunda Babansu munnu yake fada, hannunshi na rawa ya Ciro hankici daga aljuhunsa ya
fara tsane gumin dake saman goshinsa, minti goma babu Wanda yayi magana a cikinsu, da
kyar ya bude baki yace." Kana so ka fada mun cewar *Asma'u da Mimi* sun sha nono d'aya
kenan."? Kawun su Munnu ya gyada kansa tare da fadin"k'warai kuwa."
Amjad ya sauke gwaron numffashi yace." Aurena da Mimi ya haramta idan Asma'u zan aura
idan kuma Mimi zan aura aurena da Asma'u ya haramta.!!!!!!! Babansu Munnu ya tsinci kansa
da shiga rud'u da fargaba Sam!! Ya manta da wannan k'aulin *Innalillahi wa innailahi raji'un*




*K'ak'a k'ara k'ak'a tsara*







*13/November/2019*
[11/14, 7:52 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*




*51*



Cikin yanayin damuwa Babansu Munnu yace." Wannan abu akwai rikita-rikita a cikinsa akwai

daure kai, tunda ake wannan sabgar ban tab'a tunanin wannan alak'ar ba, Babbar magana ce
wannan, tsarin na addini islama babu aure a tsakanin mutum biyu sai dai ka dauki daya ka bar
d'aya, sun Riga sun tsotsi nono d'aya mutukar ba d'aya ce ta mutu a cikinsu ba, to baka da
damar auran 'yar uwarta har abada, amma kasan ko wane ijma'in malamai da nasu k'aulin,
Allah ne dai masani."
Babansu Munnu ya kare maganar sa cike da tararrabi yanzu idan Amjadu ya zab'i Asma'u ya
bar Mimi wand irin hali zata shiga? Watak'ila ma karshen rayuwar ta yazo."

Amjadu jikinsa yayi wani irin sanyi tunda yake bai tab'a shiga rud'u da fargaba ba irin na yau, ko
mutuwar iyayen sa bai shiga wannan halin ba duk da cewar mutuwar ta girgiza shi sosai
wannan yasan dole ce ko wa sai ya d'and'ane ta.



Kusan mintuna goma babu Wanda yayi magana a tsakaninsu dukaninsu suna tunanin ya za'ayi
su warware Matsalar, Mik'ewa yayi hade da mik'awa Baban su Munnu hannu sukayi sallama,
ba tare da yace masa komai ba ya futa daga ofis din.


Yana shiga mota ya fara kiran wayar Kawu Yunusa buga daya ya dauka hade da yin sallama
kamar zai masa sujjada, saboda kwantar da murya. Yace."Aure tsakanina da Mimi ya haramta
saboda sun sha nono d'aya da Asma'u tun farko Asma'u ce zab'i na saboda haka na janye
Neman auran Mimi ina rokon Allah ya fe min kuskurana, ita kuma Allah ya bata miji nagari."

Kawu Yunusa ya share gumin fuskarsa shima sai yanzu ya tuna da wannan alak'ar mamaki
yake sosai me ya hana su tuno da haka sai da magana tayi nisa, idan hakane Ashe Aminu duk
abunda yake akan yarinyr babu aure a tsakanin su."
"Kawu Yunusa yayi gyaran murya tare da fad'in "Idan ban da ka tsaurara bunkice a kan
al'amarin da sai dai muyi ta tafiya a haka domun idanun mu sun rufe akan al'amarin ta inda
muka mance da wannan alak'ar saboda haka yanzu zab'i na gare ka, Kaine zaka zab'awa kan
ka matar aure cikin su biyun."
Ranshi babu dad'i yace." Matar aure tuntuni na zab'e ta Kawu Asma'u ita na zab'a Insha
Allahu ina fatan ta zama Uwar 'yayana." Kamar yanda Kawu yayi tsammanin haka daga gareshi
hakane ya tabbata hamdala yayi a fili yace." Insha Allahu baza kayi nadamar auran d'iyar mu ba
Allah ya sanya alkairi.." Ameen suma ameen Yanzu dole kaje ka Sanar da Umma halin da ake
ciki na janye auran Mimi tunda bai hallasta ba." Kawu yace." Yanzu kuwa zan bar kasuwa inje in
Sanar da ita, kuma maganar d'aurin aure tanan jibi insha Allahu." Sallama suka yi da juna,
Amjad ya kashe wayar zuciyar sa na sak'a masa abubuwa da dama jikinshi na bashi kamar
akwai wani Gagarimin al'amari da zai faru nan gaba.

Kai tsaye gidan Granny ya wuce domin ko ya koma gida yanzu yasan mutane baza su bar shi
ya huta ba, to zancan kenan itama Granny fad'a tayi ta yi tana fadin dama Ashe basu da Asali
yaran haka kawai zai jawo wa kansa zuvewar mutum ci to itama ba ta yadda da wannan auran
ba, yana kwance cikin kujera yana jinta bai ce mata komai ba, duk abun duniya ya dame shi,
daga zarar ya tuni Asma'u sai yaji faduwar gaba, abunda bai ta faruwa dashi ba.


******
*Innalilhi wa inna ilahi raji'un* shine abunda Umma take nanatawa lokacin da ta gama sauraron
maganar da Kawu Yunusa yake tafe da ita, tashin hankalin ta sai ya ninka na da tana fargar bar
Mimi taji wannan mummunan labari tsakanin ta da Amjadu babu aure tunda dai ya zab'i Asma'u
a cikin su, ga jikinta ya rikice tun d'azu take kuka an kasa shawo kanta. Cikin yanayin damuwa
da tashin hankali Tace." Kawu wannan k'addara Allah ya ije mana ita naso yaron nan ya zab'i
Mimi domin ceto ranta, rai shine abun dubawa Mimi marainiya ce kuma tana dauke da ciwo mai
mutukar hadari kuma kaga ta dalilin sa ta Sam......... Bata k'arasa ba Kawu Yunusa yayo kanta
da bala'i yace." Baki Isa ba Mariya wallahi tallahi baki Isa ba!!! Arziki yana neman mu kina
korarsa awwo!! Bakin ciki kike mana? Ko kuma bakin halin ki zaki nuna mana wanda kika saba,
'yarinya dai 'yarmu ce muna da ikon mu aura mata duk Wanda muke so ke!! Baki Isa ki hana
mu ba 'yar bakin ciki kawai." Tsakanin Kawu da Umma dama ba a shiri tun Asali, basa jituwa a
cewar sa itace take zuga Babanmu lokacin in ya dauki albashi baya taimaka wa mahaifiyar su
lokacin tana Raye.Umma ta fusata! Ranta ya b'aci sosai wato har Yunusa yana da bakin
magana akan 'yayan ta, mutanan da suka wofin tar da ita bayan mutuwar mijinta suka watsar
da zuri'ar shi, wahalar duniya babu wacce bata sha ba, akan 'yayan ta, sai yanzu da suka ga
sun zama mutane shine zasu yi wata magana har da gadara cewar 'yayan su saboda kwadayin
abun duniya to har indai itace ta haifi Asma'u zata nuna masa iko a kanta. Ranta a mutukar
bace tace." Yunusa ni kake d'agawa murya har kana kokarin kai min duka akan 'yaya na, Yanzu
kai kana da bakin magana akan Asma'u wacce baka San cin ta ba baka San shan ta ba,
sutturarta karatun ta duk baka San wannan ba, sai yanzu daka ga ta zama mutum sannan zaka
yi wata magana akanta."? Ta k'arashe maganar cike da mamaki, Kawu Yunusa ya mike tsaye a
fusace! Yana a matsayin wan mijinta take kiran sunan sa kai tsaye, ransa ya b'aci sosai yace."
An fad'a miki nace na fad'a miki magana Mariya kiyi abunda zakiyi dama ai baki da kunya nasan
halin ki d'an uwana yayi hakuri zama dake, kina maganar suttura da sauran su, ki fad'i kud'in
wahalar da kikayi sai a biya ki, wacce bata gaji arziki ba, mu bama haihuwar 'yayan banza d'an
uwana ya iya haihuwa koma komai abunki sai anyi wannan auran."!!!



Umma ta fashe da kuka Wanda yasa na futo wuf!! Daga cikin dakinmu Allah yasa na samu
Mimi tayi bacci duk irin tujarar da Kawu yake wa Umma a kunne na kuma duk naji zancen da
suke yi, rai na a b'ace na futo INA kallon Kawu dake tsaye kan Umma yana ta surfa mata
masifa! "Ita yarinyar da kike so ya aura yace. Ba yaso saboda rashin galihu ya fi son 'yar Asali
me cikkakiyar nasaba, bayan wannan kuma sun sha nono d'aya babu yadda za'ayi ya aure su
duk su biyun, in banda kidahumanci irin naki Mariya 'yar ki zata auri mai kudi Wanda duniya ta

San dashi ke kanki kin bar kangin talauci ki nuna ba kya so Allah yayi wadaran ki Mariya."! Ya
k'arashe maganar sa a harzuke.



Kuka na fashe dashi jin irin cin mutumcin da Kawu yake wa Umma tana kuka ko tausayin ta
baya ji, idanuna sun rufe ta inda nake ganin girman shi ya zube a gurina, tunda nasan da me
yake wannan tashin hankali, duk dan kudi da soye-soyen rayuwa yau da talaka ne Amjad Kawu
bazai tako cikin gidan mun ba ko dan kar ace yayi kayan daki, amma yanzu dubi yadda yake
tada hak'arkari da jijiyar wuya.



Ina kuka nace." Kawu wannan ba dai-dai bane kar ka manta da cewar har gidan ka naje
munyi magana dakai cewar mutukar Amjadu bai auri Mimi ba nima bazan aure shi, to yanzu
duk naji abunda kuke magana akai ni da Mimi mun sha nono d'aya, Amjadu ya zab'e ni a
matsayin matar auran sa ya bar Mimi, Kawu kayi hakuri da hukuncin da na yankewa rayuwa ta,
idan shine ya aiko ka ka koma ka fada masa cewa ni Asma'u d'iyar Sulaimanu mai madara,
bazan aure shi ba, idan son gaskiya yake min ya karb'i Mimi 'yar uwata a matsayin matarsa ta
sinna domin mu ceto rayuwar ta, daga halaka."
[11/14, 6:35 PM] .: Cikin tashin hankali da damuwa Kawu yake kallon Asma'u, yace." Asma'u
kina da hankali kuwa kike fad'ar wannan maganar cewar ke baza ki aure shi ba kin barwa
wata."! Gyada kaina nayi rai na a dagule nace"K'warai kuwa Kawu na rantse bazan aure shi
ba, sai da ya hak'ura tunda babu halin ya hada mu mu biyu idan kuma da gaske kaunata yake
tsakani da Allah to sai yazo yayi abunda nace." Kawu yace." Baki Isa ba wato Bakin Ku d'aya
da Uwar ki ko."? Da sauri! Nace"Ko daya Kawu wannan ra'ayi na ne, kuma don Allah ina
Neman alfarmar ka daina zagin Umma haka, kayi hakuri kar kace nayi maka rashin kunya, a
matsayin ka na babba bai dace ba da abunda ka keyi ka daina don Allah."


Kawu yayi mamakin abunda yarinyar tace wato suna so suyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login