Showing 54001 words to 57000 words out of 95753 words
Chapter 19 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
irin haushin sa da takaicin sa nake ji a lokacin sai na rasa me zance masa, kawai na buge
k'irjinsa da mugun k'arfi na futa daga tsaka insa tare da fad'in"Dan iska kawai."
Mamakin ta yake yi wai d'an iska take kiran shi a kan hakkin shi, ya gano kishi tsagwaron sa a
idanunta dama so yake ya tunzurata, babu wata damuwa a tare da shi yace." Ni kam babu
mahalukin mutumin da zai kirani da wannan Kalmar a kan HAKKINA, kawai Dan nayi marking
love da Matata sai a ce min d'an iska, kin ci albarka cin My Wife Mimi na da sai kin gane kuran
ki."
Yana gama maganar shi ya futa daga toilet din ba tare da ya saurari abunda zata ce ba.
Zamewa nayi na zauna dab'as! Kan tayal din dake kasan toilet din na hada kaina da gwiwa ta
wani irin kuka ya kufce min Wanda nayi ta kokarin danne shi, kuka nake sosai da sosai ina
addu'ar Neman samun sauki daga Allah, wani irin sabon sonshi da kaunar shi naji yana taso
min a zuciyata take jikina ya kama rawa duk narasa me zanyi inji dad'i a rayuwa ta. Motsin bude kofar naji na mike zumbur domin na dauka shine ya dawo sai naga Mimi ta shigo
tana bin bango, da sauri naje na kama ta, ita kuma ta dinga bin fuskata da kallo bakinta a bushe
tace"Habibty kukan kike yi ko." Babu karya domin ga hawaye ne nan tana gani a kwarmin idona
nace" Mimi kukan tausayin ki kawai kawai nake yi." Murmushi kawai tayi min tana fyada kanta,
ruwan ha hada mata cike wani baho na zuba detol kad'an a hankali na zaunar da ita ciki. Kara
ta k'walla ra tana rike hannuna nace" Mimi ki zauna ki Dade a ciki ZAKIJI dad'i jikin ki." Gyda
min kai tayi tana rintse idonta, futa nayi daga toilet din na barta.
Babu kowa a dakin, na hau cire bedshirt din shina duk ga d'igon jini nan, gashi duk ya
cukurkude raina babu dad'i ko na kwabo na cire shi hade da aje shi gefa guda, wani na ciro kai
kyau na shimfid'a kan bed din, na Ciro mata kaya masu kyau na aje gefan gado, zama nayi ina
jiran futowar ta,
Minti ashirin tayi ta futo yanzu tafiyar ta ta sauya ba kamar d'azu ba, na kalleta naga duk ta
rame lokaci guda.
Zama tayi kusa dani tana fadin,"Kinga yanzu naji dad'i wallahi."
Nace "Dole haka zaki dinga yi in anjima da yamma ma ki kara shiga ruwan zafin."
Tace"To."
Shiru mukayi tana kokarin sanya kayan ta, ina taya ta. Nace"Kin San me."? Girgiza min kai tayi.
Nace"Duk sanda ya kara zuwa yace zai yi sex dake Wallahi kar ki yadda har sai kin warke in ba
haka ba tafiya ma zata gagare ki, domin na lura ba imani ne dashi ba."
Karaf!! A kunansa lokacin za yake shigowa dakin yaji Hud'ubar da Asma'u take wa Mimi.
*18/11/2019*
[11/19, 10:01 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*
*56*
Cike da mamaki yake kallon Asma'u wacce tayi tsili-tsili da ita tasan tabbas yaji maganar da
take fadawa Mimi ga yanayin kallon da yake mata.
K'araso wa yayi dakin sosai hannun shi rike da wata Leda har ya zauna gefan Mimi idanunsa na
kàn Asma'u yana tuhumar ta da idonsa, sunkuyar da kaina nayi kamar wacce tayi wa sarki
k'arya.
Gyada kansa yayi hade da rungumo k'afafun Mimi yana kallona yace." Manene hujjar ki, na
bata wannan gurguwar shawarar.?
Kunya ta hanani in d'ago kaina na kalleshi.
Dariya naji yanayi kasa kasa yace." Saboda mugunta kike zugata ta bujere min a shimfid'a kina
mata bakin ciki tafi ki ta ko wane fanni, ga lada ga dad'i zata kwanta a kirjin mijinta shi kike wa
bakin ciki ai na gane yanzu."
Kaina na dago in kallonsa yanda ya wani matse Mimi a jikinsa yayi mugun bani haushi a zuciya
ta nace "Wannan guy wai wane irin tantiri ne?
Ba tare da nace komai ba na mike tsaye hade da gyara hijab dina INA kallon Mimi dake lumshe
ido a ka fad'ar sa, nace" Ni Zan tafi idan kin dauki shawara ta kan ki kika yiwa Allah ya bamu
alkairi."
Kofa na nufa da sauri.!
Mimi ta yunk'ura da sauri ta mike ta biyo bayana cikin dingisa k'afafu shima bayan ta ya biyo
lokacin har na Isa parlor Tarar gabana tayi hade da marairaice fuska tace "Don girman Allah kar
ki tafi yanzu ki bari sai gobe."
Kallon baki da hankali nayi mata wai in Bari sai gobe lallai Mimi, ni idan nabar gidanan nayi
rantsuwar babu Wanda zai sanya ni na kara dawowa cikin shi, kokarin bude kofa nake in futa
yazo ya bake kofar Yana min wani kallo kasa-kasa yace." Malama Madam tace ki bari sai
anjima kya tafi kin ji, yanzu ki shiga kicin kiyi mana girki ni da ita." Hararsa nayi a lokacin sai ya bani dariya saboda nasan duk abunda yake yi domin ya bani
haushi pretending yake ina kallon wani Abu boyayye a k'wayar idonsa.
Nace"Wallahi da Kai da Mimi babu Wanda zan yiwa girki Kaji na fada maka ma."
Babu yabo babu fallasa yace." Wato kinanan da Wannan gantsarar taki ko? Na hanani sanya
Wannan bakin hijab din kinki ji ke gaki da baki kamar shuni."!!
Naji haushin ba'ar da yayi min sosai na kalleshi fuskata a daure nace",Bani hanya na wuce." Ki
yayi ya tsira min ido, Mimi ta k'araso gurin jikinta a sanyaye tace."My heart ka k'yaleta ta tafi
tunda baza ta zauna ba."
Kallonta yayi yace." Ok tunda kince a k'yaleta ta tafi kar ki k'ara kiramin sunan ta, idan anjima,
dama don kin damu a dauko ta ne."
Hannunsa ta rike tana murmushi,
Matsawa yayi daga jikin kofar na bude na futa ko kallonsu ban yi ba.
Harabar gidan na tsaya INA waige-waige karaf ! Muka hada ido da Mujahid ya futo daga part
din shi, jikinshi sanye da kayan kwallo shi da wani boy da bool a hannunsa suna bugawa a filin
gurin.
Saurin dauke kaina nayi na fara tafiya
Da sauri Mujahid ya mik'ewa yaron shi, boll din ya Isa gurin ta fuskar sa dauke da kayattacan
murmushi.
"Asma'u" sanyayyar murya shi naji yana ambatar sunana, tsayuwa nayi hade da sakin fuskata
nace"Na'am kana lafiya."? Ya saki murmushi tare da fad'in"Lafiya Lou nake sai dai tunanin ki ya
hanani Sakat! Jiya da kyar nayi bacci wallahi." Dariya na danyi nace"Ka fiye ban dariya har da
rantsuwar ka." "Am serious wallahi babu karya a magana ta jiya da kyar nayi bacci Allah ya Dora min so da
kaunar ki kamar raina." Shiru nayi ina kallonshi fuskata a sake, yace." Kin lek'a amare har zaki
tafi." Nace" Wallahi kuwa." Agogon hannunsa ya kalla tare da fadin"Gaskiya ana rana bari in
futo da mota in kai har gida." Nace"Aikuwa da ka kyauta." Juya wa yayi da sauri ya nufi part dinshi, kallo na bishi dashi ina
murmushi guy yana da kyau da sanyin hali ga nutsuwa.
Mintuna uku naga motar shi na futowa daga nashi gurin, saurin dauke kaina nayi ganin shine
yake driving din.
Kusa dani ya tsaya yana yi min Hon!
Banza nayi dashi ina kallon part din Mujahid aikuwa sai gashi ya futo cikin motar shi, ya k'araso
gurimu tare da futowa.
Fuskar sa a sake ya mik'awa Amjadu Hannu tare da fad'in "Ango! Ango."!! Dariya suka yi a tare
Amjadu ya Sosa kanshi As'usuel yace." Wato dama wayo kuka yi min Ashe haka ake Jin dad'i
shine kuka b'oye min."
Mujahid ya bashi hannu suka tafa, tare suna kyalkyala dariyar shakiyan ci, Mujahid yace."Baka
da wasa fa wato har an wuce gurin kenan. "
Amjadu yace." Tuntuni Alhaji yanzo sai jiran sakamako."
Dariya suka kece da ita a karo na uku suna tafawa.
Ji nayi tsayuwar gurin ta ishe ni, domin gani nake yi duk abunda yake yi kamar da hujja yake yi,
motar Mujahid na fufa jikina duk babu k'wari ,wai ni guy nan yakewa wannan tozarci, wallahi
babu abunda zai kara kawo ni gidansa
Bude motar nayi na shiga na zauna abuna.
Amjadu yana kallonta a take ya gimtse fuskar sa daga dariyar da yake yi, kafin ya Ankara
Mujahid ya saki hannunsa tare da fadin"Bari i n kai wife dina gida insha Allah."
Fuska ya had'e sosai yana kallon bayan Mujahid da yayi gaba, har ya bude motar sa ya shiga
idonsa na kansa yana mamaki yaushe suka shaku shi da Asme yasan halin yarinyar da girman
kan tsiya.
Duk yanayin da ya shiga ina kallon shi, tunda motar Mujahid tana gefan tashi, naji dadin ganin
yanda ya shiga halin damuwa
Kawai sai na shiga dariya babu gaira babu dalili, shima Muhajid din dariya yake yana kallona
cike da so ya kunna motar shi muka wuce motar Amjad din da sauri.
Gumi ne yake tsiyaya a jikinshi wato wulakanci. Da yarinyar nan zata yi mishi kenan, da kanshi
ya futo domin ya kaita gida, Dalili ya aiki su Rambo shine zatayi masa wannan cin mutumcin ya
lura fa Mujahid da gaske yake ganin yanda yake zak'ewa akan yarinyar bude motar yayi a
fusace! Ya nufi part dinshi yana wani taka k'asa da k'arfi sai huci yake yana jin wani irin kishin ta
a zuciyar sa.
*****
Hira sosai muke da Mujahid sai yanzu na kare mishi kallo kyakyawa ne sosai yana da d'an kiba
amma ba sosai ba fari ne amma ba kai Amjadu ba, fuskar sa kullum a sake, take naji ya kwanta
min domin duk cikin samari na babu Wanda na tab'a sakarwa fuska kamar shi, a yanda yake
fada min shi da gaske yake aurena zai yi kuma, baya so aja wani dogon lokaci, to nima gaskiya
ya kwanta min a rai naji zuciya ta ya kwanta min shiyasa na bashi numbar wayata da zamu
rabu, tare da yi min alk'awarin zai kirani da daddare mu sha shira nace masa ina sauraren sa.
Ko da na koma gida a lokacin aunt Hauwa ta tafi gidan sai Umma kadai tana gyare-gyaren
abunda ba'a rasa ba, tana kallona cike da mamaki take fadin ",Har kin dawo kenan."? Nace" Eh
Umma zaman me zanyi"
"Lafiya dai ko."? Umma ta fada tana kokarin futa daga dakin, ta San dai ta tsuniyar gizo bata
wuce ta koki.
Shiru nayi mata domin ina jin nauyin fada mata dalilin kiran Mimi di.
*****
Rayuwa kenan yau kwanan Mimi biyar a dakin mijinta, inda Umma kullum ya zauna zancan
Mimi take yi, duk da cewar kullum sai sunyi waya da ita, wani lokacin ta bani wayar mu gaisa ta
k'araci korafin ta ta gama , sai dai in ce mata kawai tayi hakuri zan zo. Wani lokacin kuma idan
ta kira wayar kin karba nake yi ko in tashi in bar gurin.
Ya Aminu da Babban su Munnu sune suke mana cukucukun makaranta nan FCE Babban su
Munnu yake sha'awar muyi mu samu ko Diploma ne tsakanin Munnu da Ya Aminu soyayya
tayi k'arfi domin Babansu ya kori Shamsu tunda yayi da shi ya turo manya a yi magana
shikkenan ya gudu daga ranar be kara zuwa ba.
Gaskiya naji dadin koma wa makarantar da zamu yi ina mutukar son in ga nayi karatu me zurfi
a rayuwata.
Ni da Munnu sai shirye-shirye muke yi wacce tayi tayi dani muje gidan Mimi naki zuwa, ita kuma
tace baza taje ita kadai ba.
********
Rayuwa suke da Mimi babu yabo babu fallasa Shine me Dan shige mata jiki ita kuwa kullum
kamar suruka take a gurin shi, idan yana guri ta dinga b'oye-boye kenan shi dai sai dai yayi
dariya kawai yana mamakin me zata b'oye masa Wanda be gani ba.
Tun ranar da ya kwanta da ita kwamciyar aure bai kara takar ta ba, sai dai duk daran duniya
yana ragewa kansa zafi da ita, amma bai kara gangancin yin sex da ita saboda baiji da dad'i ba
a farko.
Misalin k'arfe goma sha biyu da rabi na ranar Asabar Wanda yayi dai-dai da satin Mimi biyu
gidan Amjadu, tana zaune a parlor ita kadai lokacin ya futa zuwa company sa kuma dai
shirye-shiryen tafiya Chana yake yi shiyasa kwana biyu baya zama sosai.
Kallo take yi ita daya kamar tsuntsuwa, sai ta soma jin takun takalmi za'a shigo parlor da sauri
ta kallo kofar shigowa, suka Had'a Ido da Alina ta shigo cikin wasu 'yan iskan kaya fuskar ta
tasha make up sai taunar cingum take, hannunta rike key din motar ta tana kar kad'a shi, tazo ta
tsaya kan Mimi tana girgiza jikinta, cikin shigar raini. Mimi tace" Alina babu sallama kika fado min gida."
Wata irin mahaukaciyar dariya Alina ta kwashe da ita tare da fadin"Su Mimi masu gida!!!!
Hahahahaha.'' Mimi ta bita da kallo cike da mamaki.
Wani irin tauna tayi wa cingum din bakinta tayi kwai dashi ta kalli Mimi a d'age tace."Ina sugar
Boy yake yi."?
Alina ce kawai take kiran shi da wannan sunan."
Mimi tasha kunu tare da fadin "Ban sani ba ni Zak........ Kafin ta karasa Maganar tata Alina ta
wanke ta da mari tare da fadin" Kinyi ganganci Wallahi!! Kinyi gangamcin shiga gona ta, shigiya
'yar mutsiya ta, kar ki ce bam san abunda yake faruwa tun daga farkon auran Ku har karshen
sa, duk nasan komai, Wallahi i n da nasan haka zakuyi min da ban gayyace Ku brhday na ba,
Maciya amana kawai."
Mimi ta mike tsaye da sauri tare da buge hannun Alina dake kokarin kai mata wani sabon marin,
tace"Ba Isa kizo har cikin gidana kiyi min iskanci ba, wallahi yanzu zan sanya ayi miki fata-fata a
gidan nan."!! Dariya Alina ta kwashe dashi ta daki! Kirjin Mimi tana watsa mata kallon raini
tace"Nasan fa komai banza kawai kema da kike rawar Kai kin aure Sugar Boy a banza domin
bake ya ke so. Ba ya fi son wancan mutsiya ciyar yarinyar mummuna Asma'u, to Wallahi duk sai
nayi maganin maciya amana kawai."
Mimi ta fusata ta d'aga hannunta zata kai mata duka Alina ta goce da sauri ta sanya gwiwar
hannunta cike da mugunta ta mangare Mimi ta fad'i kan kujera, takalman ta masu tsini ta cire ta
fara dukan Mimi dasu abun. Mamaki, Mimi ta fara kokarin k'watar kanta tana kare fuskar ta,
inda Alina ta sanya tsinin takalmin ta ta buga mata a goshi da mugun k'arfi sai jini ya soma
zuba, da sauri ta futa daga parlor.Mimi ihu kawai take hade da dafa goshin ta dake zubar da jini
duk ya b'ata mata fuska.
Alina kuwa a fusace ta figi motar ta ta fuce daga gidan.
Da kyar ta dauki wayar ya ta fara Neman numbar sa, kira kusan biyar bai dauka ba, gashi dai
tana ringing aje wayar tayi tana kuka ta nufi firji k'ankara ta dauko ta Dora a goshinta inda yake
zubar da jini gurin har ya kumbura yayi tsini
Alina kuwa tana tafiya cikin motar ta tana tunanin sharrin da zata kulawa Mimi gurin Amjadu.
Wayar ta dauka ta fara kiran shi, sai da tayi ringing sau uku ba 'a dauka ba. Ana hudu ne ya
d'auka,
Murya sa s tsaye yayi sallama domin ya gane numbar Alina ce.
Wani irin mahaukacin kuka ta fashe dashi, tana fadin "Na shiga uku na lalace!! Hubby naje
gidanka sun taru sunyi min duka."
Kasa gane inda maganar ta ta dosa yayi yace." Ke wai meye ne, ina da uziri yanzu."
Alina tana gursken kuka tace." Asma'u da matarka Mimi ne sukayi min dukan mutuwa Yanzu na
ina kan hanyar zuwa hospital."
Cike da mamaki yace." Me kika yi musu? Kuma me ya kaiki gidana." Cikin kuka kamar gaske
tace"Kasan munyi skull tare dasu sai ince maka gurin zaman mu d'aya dasu, dake ban samu
damar zuwa bukin ba, sun gayyace ni, shine naje nayi musu Allah ya sanya alkairi Asma'u tazo
gidan ,shine suka taru suka dinga dukana."
Kashe wayar yayi saboda tsabar takaici, Alina ta fashe da dariya tana draving tace"Shegu 'yan
iska ai tunda bani na aure shi ba, sai na hada muku sharri a gurin sa, wayar sa ta kara kira yana
kallon kiran yak'i dauka.
Tunani yake wato bayan futowar shi daga gida Asma'u taje gidan shi, yasan duk abunda Alina
ta fad'a Asma'u zata aikata sun mayar masa da gida sansanin yak'i baya ganin laifin kowa sai
na Mimi gani yake Asma'u ce take murza akalar ta, sai abunda tace da ita sannan take yi,
Wayarsa ya dauka ranshi a b'ace! Sai yaga kiran Mimi kusan sau shida, lallai zancan kenan,
bugu daya wayar tayi Mimi ta d'auka tana shashshekar kuka.
Wata irin tsawa ya buga mata tare Da fadin"Babu babban mai laifi sai ke Momy menene zaku
Tara mata a gidana kuna fadace-fadace sai kace wasu yara, na lura sai abunda Asma'u tace
kiyi kike yi ko."!!
Mimi ta tsananta kukan ta tana so ta fahimtar dashi amma Sam yak'i sauraranta masifa yake
mata.
Daga k'arshe yace." Kafin in dawo ki sallami Asma'u domin baza ta zo gidana tana tada min da
fitina ba."
Kashe wayar yayi bai bari tace Komai ba.
Mimi rasa abunda yake mata dad'i tayi goshinta ya suntume yayi tsini ga zugi yana yi mata, ta
lailaiya shi, duk da haka babu sauki, kwamciya tayi kar kujera tana kuka tare da tunanin
maganganun Amjadu da inda suka dosa, wanene Ya sako Asma'u cikin case din gidan sa, da
zai kama fad'ar bakaken maganganu Sam