Showing 81001 words to 84000 words out of 95753 words

Chapter 28 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

da ake ciki yanzu soyayyar ta ta cika min zuciyata duk da bata Raye, ta
inda nake yi wa mata kallon maza ciki kuwa har dake, saboda haka ki kiyaye fad'a min magana
ko wace iri ce,ni Amjadu AbulAbbas ma nasara na shafe ki a babin rayuwa ta."_

~AMJD ABUL ABBAS~


Wani irin gumi ne yake tsiyaya a jikina take wasu zafaffan hawaye suka kece min, Dana San
wad'annan mugayen maganganun guy nan zai fad'a mun da ban mishi magana ba, hannuna na
karkarwa nake bashi amsa..... Da sauri na tura masa, na kashe data hade da jefar da wayar
kan Katifa na rungume filo ina tik'ar kuka harda sharb'e majina,wato ni guy nan yake nunawa
iyaka ta kan abunda Mimi ta tafi ta bari gashi Ubangji ya zuba min kauna da son baby Aysha a
cikin raina, nafi awa guda ina kuka k'asa kasa don kar Umma taji fa kyar na rarrashi kaina tare
da alk'awarin cewar bazan kara shiga harkar shi ba har a bada..Data na k'ara kunnuwa ina
tunanin zanga sak'on shi domin nasan na fad'a masa bak'aken maganganu Wanda suka fi nashi
abun mamaki, ko da na duba sai naga yayi bloking d'ina, sak'on Dana tura masa Yanan yanda
yake, ajiye wayar nayi ina da na sanin bud'e whatsp din inda nasan wannan bakin cikin zan
riske, da kyar bacci ya dauke ni mai cike da mafarkin baby Aysha da Mahaifiyar ta.

Ko dana tashi da safe sukuku na tashi jikina duk babu kuzari har Umma ta fahimci wan Abu
amma bata ce min komai ba, saboda tana tunanin a jizanci ne irin na d'an Adam, sallama nayi
mata na tafi makaranta. To ko A skull din ma kasa b'oyewa Munnu nayi sai da na fad'a mata
komai kuma na nuna mata text din da ya turo min, Munnu ta dinga mamaki tsabar haushi da
takaici yasa ta dinga zaginsa hotonan baby take dubawa sosai tana fad'in"Wallahi karya yake in
Ku ya rabaku da ita mu bai isaba sai munje mu daukota Wallahi munganta ai wannan rashin
imani ne ace kamar jinin Mimi sai dai mu ganta a hoto gaskiya bai isa ba."!! Yanda Munnu take
masifa sai ya bani dariya nace"Munnu ni da zaki bi ta tawa da mun hak'ura wallahi duk son ki da
baby baki kaini ba, amma na hak'ura na bar masa kayan sa kamar yanda ya fad'a d'in, nasan
duk daran dadewa baby zata neme mu." Munnu tace"Ai sai munje har gidan mun ganta wallahi
hakkin mu, dole zan hurawa Babanmu waya muje tare." Shuru nayi mata ita kuma ta hau tura
hoton baby a wayar ta.

******
Amjadu kuwa ranar da yaje amsa kiran da me girma governor yayi masa basu kwashe da dad'i
ba, domin wasu zantukan banza yake masa wai yaga jama'ar gari suna zargin sa kan harda sa
hannunsa kan afkuwar abunda ya faru, ya kama rantse-rantse yana fad'in kwata-kwata bai San
zancan ba, don haka yayi hakuri kar ya kulle CE shi kuma a matsayin sa na shugaba insha
Allah zai sanya a tsaurara bunkice domin gano wadanda suka aikata haka." Kallon shashasha
Amjad din yake masa domin ya ma kasa cewa dashi komai kawai ya mike zai bar gurin,
governor yadawo dashi, cikin sigar rarrashi yace." Sai magana ta biyu cewar nayi maka
alk'awari insha Allah wannan kujerar tawa Kaine zaka maye gurbin ta, tunda na lura jama'ar gari
na sonka zamu had'a baki dakai muyi murdiya ga Wanda yaji zab'e zaka tsaya takara a jam'iyya
ta, sai milki ya dawo hannuna." Amjad yaji kamar ta kwakwkwad'a masa Mari lallai
shaye-shayen da yake yi ya soma tab'a masa kwakwalwa da har yake tunanin dashi zaiyi
wannan aiki.
Kallon banza Amjad yayi masa yace." Idan ina sha'awar mulki kai! Baka isa ka sanya ni nayi ba,
lokacin da zaka ji ni a duk jam'iyyar da nake so zakayi mamaki so wannan Ba damuwar ka bace
tawa ce, maganar zaka tsaurara binkice kan mutanan da suka shirya wannan sharri gami da yin
izgili ga Allah da manzon sa, wannan bai dame ni ba, saboda ni nasan ko su waye kar ka bawa
kanka wahala kuma zan dauki mataki a Kansu."!! Tebur din gaban shi ya buga da k'arfi! Ya mike
tsaye hade da fad'in"Na barka lafiya." Futa yayi cikin yanayin tafiyar shi, ta gwarazan maza.
Governor ya bishi da kallon mamaki! Wato duk inda yake tsammanin yaron ya wuce nan, lallai
su Alhaji Hashimu mai citta sun shirya masa sakiyar da babu ruwa ya tabbata da babu wannan
maganar a kasa, zai iya Jan ra'ayin yaron ya karb'i takarar governor kano a jam'iyyar su, domin
ya tabbatar Da babu abunda zai hanashi ya lashe zab'e saboda kaunar da jama'ar gari suke
masa, shi kuma tanan sai yayi amfani da damar shi, shiru yayi yana tunanin mutukar ya sauka
daga kan mulki kashin sa ya bushe zai tabbata bashi da tsunsu bashi da tarko.

****
Tsaf ya fito cikin shiri, granny da Iyami na zaune a parlor suna hira, ya k'araso tsakiyar parlorn
hannu ya mik'a ya dauki baby dake jikin granny a kwance sai wuntsin-wuntsil take, sama ya
d'aga ta kamar yanda ya saba yi mata yana kyalkyala dariya itama na b'angale baki, yafi minti
goma yana wasa da yarinyar sannan ya zauna da ita a jikinsa yana fad'in"Baby zanyi missing
dinki fa....Granny don Allah Ku shirya mu tafi tare kinji. " cikin shagwaba yayi maganar, granny
tace"Kasan Allah babu inda zamu bika kai dai kaje kurrum Allah ya bada sa'a idan ka dawo ma
ina so muje muga 'yan uwa Chadi. " yace." Sai dai idan kin yarda mu tafi tare bayan nagama
Abunda ya kaini sai mu wuce Chadi din ko ya kika ce." Girgiza Kai tayi tana fad'in"Oh-oh!! Kaje
dai ka dawo idan kuma kak'i kaini ai da k'afafuna sai in tafi ka dawo ka tadda bama nan." Yace."
Ki Bari zamu je granny nasan halin don girman Allah kar ki d'aukar min Baby kuje wani guri."
Tsakaninsa da Allah yake maganar. Granny tace"Ikon Allah!! Yanzu ni kakewa gargad'i kan 'yar
ka K'ato! Lallai baka da ta ido!! Dariya yayi ya mike yana fad'in"Granny soyayyar sweetheart
dina ta cika min zuciya ta shiyasa idona yake rufewa. " romot din dake kusa da ita ta dauka ta
jefe shi dashi, tace"Marakunya kawai, ni kam bana maka fatan samun matsala da duk matar da
zaka aura nasan kam Aysha zaka iya sakin ta." Babu wasa a fuskar shi yace." Granny duk

wacce zata zauna min da sweet heart lafiya ina maraba da ita, zaman lafiyar mu da ita ta so
baby Aysha." Granny da Iyami suka girgiza kai cikin mamaki

Iyami ya mik'awa baby din ya kalli agogon dake daure a hannunsa, Cikin nutsuwa yace." Ni zan
tafi sai munyi waya ko
"? Granny tace" Allah ya kiyaye hanya muna maka fatan alkairi,Iyami ma fatan alkairi take masa
ya fuce daga parlor da sauri,baby ta bishi da kallo tana d'aga hannunwan ta, yarinyar sun saba
sosai da baban ta.
Yana futa su Rambo suka rufa masa baya, kai tsaye airport suka kaishi sai da suka ga tashin
jirgin su sannan suka bar gurin. Hade da yi masa fatan dawo wa lafiya.


****
Gurin Jahid naji cewar yayi tafiya sai ban nuna komai ba, ko da wasa ban fada masa abunda ya
faru tsakanina dashi ba, haka muke tafiya dashi cike da kauna da kulawa kullum kuwa idan ya
shiga gaida granny sai ya dauko min picture din baby ya turo min, mu yini muna kallonta ni da
Umma. Allah mai iko tsakanin Ya Aminu da Munnu soyayya ce mai k'arfi ta kullu shiyasa ma Munnu ta
rage zuwa gidanmu a cewar ta wai kunyar Umma take ji,magar auran su ta kankama inda
Baban su Munnu da Kawu Yunusa suka tsaida magana insha Allah wata uku za'a d'aura
auransu tunda Ya Aminu ya yarda ta cigaba da makaranta a gidan shi, Kawu Yunusa da kansa
yazo gidanmu ya karewa Umma zagi har dani sai da ya had'a ya dinga zaginmu da cin mutumci
iri-iri wai tunda na ki auran Amjadu to in fito da miji a hada da Aminu ya fuskanci wannan yaron
da yake Neman aurena Mujahid yaudara ta zaiyi tunda gashinan kullum sai yace zai turo
magabatan sa a tsaida magana sai yak'i saboda haka inyi maza in futo da miji ko kuma Wallahi
ya d'aura min aure da Musa tunda dama tuntuni shine ya fara cewa yana sona." Ranar kuka ns
yini ina yi ina samun chaji a waya ta ns kira Jahid din tare da fashe masa da kuka duk na
kwashe Abunda yake faruwa na fada masa. Shima babu shiri ya je ya Sanar da mahaifin sa
halin da ake ciki. Take Alhaji Auwalu yace." Zai tura akai kud'in aure da sadaki. To ko da Jahid
ya samu mahaifiyar sa da maganar tsalle tayi ta dire tace wallahi Sam! Bata yadda yaje ya auro
'yar talakawa ba, domin baza ta tab'a had'a jinita da talakawa masu dattin hula ba, tsaf! Ta
sanya akaje akayi mata bunkican su waye su Asma'u kai har gidan su sai Da tasa aka binkito
mata. Aikuwa ita da Aminiyar ta suka shirya cikin shiga ta alfarma suka tafi gidan, Baban
abunda ya tayar mata da hankali yanda taga wani k'aramin gida kamar akurki wai nan gidan
Mujahid dinta zaije ya nemi aure salon ya zubar mata da mutumci da kima a fusace! Suka shiga
gidan Momy Mujahid din ns karkada key dinta motar ta cikin izgili
Ina sunkuye bakin rijiya ina dauraye hijabai na, Umma kuma na cikin rumfa tana d'aurin sukari
hira baby Aysha muke yi da ita kawai naji wani mugun kamshi ya bak'unci hancina sawun tafiya
naji na kalli kofar shigowa da sauri, wasu hamshakan mata ne suka shigo cikin ya tsine fuska
sukayi sallama, na d'ago Cikin nutsuwa nake amsa musu, Hajiya Fatima ta kalleni ya a mutse
tace"Da'alama kece "Asma'u ko."? Babu walwala a tare dani nace" Nice." Kallon banza tayi min
ta wani ya mutse fuskar ta had'e da tofar da miyau! "She is ugly girl!!." Ta fad'a tana kallon
Momyn Jahid dake bin tsakar Gidanmu da kallo kamar Wanda take Neman wani Abu.... Wani

irin tsinkewar zuciya naji lokacin da tafad'i min wannan Kalmar kallo nake binsu dashi cikin
mamaki!! Momy Jahid ta kalleni a wulakance tace"Ke! Ina uwarki kwad'ayyaya gurun ta nazo
ni." Umms ta futo tana fad'in "Asma'u ke da waye ne."? Cikin takaici da jin haushi nace "Umma
wad'annan sakarkarun matan ne suka shigo mana gida babu sallama ko wacce tana fama ra
karnin bleecing sune har suke kiran wani da mummuna."! Momy Jahid ta kawo min wani
bahagon mari tare da fadin" Ke don ubanki kin San kuwa ni wacece a gari nan. "? Kaucewa
nayi da sauri ina fadin " Sanin ko ke wacece bai dame ni ba nasan dai ke macace mara tarbiyya
mace mai izgil...... Kafin in karasa Umma ta gwab'e min bakina tare da fad'in"Asma'u baki da
hankali ko."? Nace. " Umma kin..... Tsawa tw buga min tare da fadin",wallahi in bakiyi shiru ba
ranki zai b'aci a gurina."!!Momy Mujahid tace "Ki k'yaleta ta zageni da kyau! Nagode Allah da ya
nuna min halin ki tun kafin Dana ya aure ki dama jama'ar gari na fadin haka a kanki,to bari kuji
gargadi na daku da babban murya tun wuri Ku janye jikin Ku domin har indai nice mahaifiyar
Mujahid wallahi bazai aure ki ba bazan hada jini da talakawa fakirai irin Ku ba, mutsiyata kawai."

Mamaki ne ya lullub'e ni jin Ashe da da mahaifiyar Jahid nake magana naji tsoro da kunya
sosai amma lokaci guda naji wata irin muguwar tsanar matar domin a rayuwata na tsani masu
kudi marasa kaunar talaka ya rab'e su. Cikin daki na shige cike da takaici a fili nace "Wallahi
kinci darajar Mujahid ne kawai." Ashe taji duk da k'asa kasa nayi maganar aikuwa naji tana
fad'in"Da kin sani kin dake ni kamar yanda kikayi NIYYA marakunyar yarinya kawai. " Umma
kuwa hakuri kawai take basu Hajiya Fatima ta daka mata wata irin tsawa "Dallah rufe mana
baki."? Umma ta rike hab'a cike da mamaki! Hajiya Fatima ta cigaba Da cewa" DUk laifin naki
ne ai hausawa suka ce ido na mudu ba yasan k'ima, in banda abunki ina mu INA Ku kwadayi ne
ya rud'e ku kuma kinyi a banza domin dai d'anmu bazai auri yarinyar Ku ba." Umma taji zafin
maganar da Hajiya Fatima ta fad'a to dake kowa na da nashi hankalin, sai ta share kawai tace
"Shi aure nufi ne daga Allah idan Mujahid shine mijin Asma'u babu mahalukin da ya isa ya
hana, idan kuma bashi bane Allah ne masa ni don haka Ku kwantar da hankalin Ku."

Momy Jahid ta Ciro d'aurarrun kudi cikin jakar ta dauri uku ta watsa ma Umma a jiki cikin izgili
tace"Ki tofar da bakin miyau na bakin ki domun kinyi sab'o Wallahi Mujahid bazai auri yarki ba
mutukar ina Raye. "!!! A fusace taja hannun Hjy Fatima suka futa daga gidan.
Umma ta shigo inda nake tana fad'in" Ikon Allah Ashe haka wasu masu kud'in suke? Ashe
mahaifiyar Mujahid bata da kirki shikam yaron kirki dashi lallai albasa bata tayi halin ruwa ba."
Nace Umma ki k'yaleta badai Jahid ne bata so na aura tom ni. Kuma sai na aure shi sai inga ya
zata yi."!
Umma tac"A'a ni bana yi miki sha'awar auran shi tunda uwarsa bata so ko anyi anyi auran ma
to ba dad'i zakiji ba, kowa ya shaida cewar matar shi mutuniyar kirki ce kingani ke babu
Matsalar kishiya tunda ta amunce ko ka bata amunce mijinta ya aure ki ba tom Allah da manzon
sa, sun hallasta amma gaskiya matar nan ta bani tsoro." Nace"Umma ki kwantar da hankalin ki,
kamar yanda kika fad'a cewa aure nufi ne na ubangiji to ni ina nan kan bakana Wallahi babu
gudu babu ja da baya sai dai in Jahid din ne yace ya janye maganar aure na tom sai in hak'ura.
" Umma tace "To Allah ya zab'a abunda yafi alkairi dai." Amin nace zuciyata duk babu dad'i.

Kuka sosai Momyn tasa take da kyar ya shawo kanta tayi shiru yace." Ki fada min ko menene
Mommy" Tace"Wai ni yau ka kajawo wa zagi a gurin wadanda basu isa ba, Mujahid yau matar
da kake Neman auranta ta zage ni ta kirani karuwa wai mai bleecing sai ta kara fashewa da
kuka sosai har da dafe kanta." Jahid ya sunkuyar da kansa cike da mamaki anya kuwa Asma'u
zata iya zagin Momyn sa kamar yanda ta fad'a to wai ma shin a ina suka had'u da juna ne.?








*27/11/2019*
[11/28, 7:55 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*




*66*



Mujahid ya cigaba da rarrashin Momyn sa har sai da tayi shiru tukkuna ya kalleta a nutsu
yace."Momy wai ina kika ga Asma'u da har tayi miki rashin kunya nifa abun nan ya bani
mamaki."! Cikin fusata Momy tace"Naga kamar kana shakka ne Jahid har kana titsiyeni ka
tambaye ni, to gidansu nasa aka kaini domin in gargade ta ta fita harkar ka domin naga mayu
ne kana zaune da matar ka ta kirki ka je ka kwasowa kanka kaska shine fa ta yi mana wankin
babban bargo nida Hajiya Fatima." Mujahid yayi kasa da dansa cikin mamaki jin wai momy
gidansu Asma'u taje to in hakane Ashe itace ta jawowa kanta raina yasan halin Momyn sa da
zubda girma mybe taje tayi wulakancin da ta saba ne. Tace "Saboda haka in dai nice mahaifiyar

ka ban yarda k auri yarinyar ba, shida shiru yayi mata har sanda ta kare fad'an ta yayi mata
sallama ya tafi gida. To ko da yaje gida ma matarshi kasa gane kansa tayi dama 'yan kwanakin
nan haka yake mata duk ya sauya kwayenta nace mata dama idan namiji zai kara aure canza
hali yake, ita dai tunda ta hada masa abunci sai ta shige d'akinta domin ta lura kamar zamanta
a kusa dashu baya so. Jahid kuwa ba wani ci abunci da yawa ba, ta kwanta duguwar kujera
yana tunanin ala'amri lokacin yi wayar su nayi ya kirata. Lokacin ina zaune ina yin game a
wayata naga kiransa dama na tsammaci haka, Muka gaisa kamar yanda muka saba kana ya
d'ora da maganar shi kamar haka" Asma'u wai da gaske Momyna tazo gidanmu."? Nace"Babu
wai Mujahid Momynka tazo gidanmu. " shiru yayi na minti biyu yace."Ki fada mun gaskiyar
Abunda ya faru." Nace"Jahid Momyn ka tazo tayi mana cin mutumci sosai takai har sai da na
mayar mata da martani a rashin sani sai daga baya da ta fad'i cewar itace Momynka sannan
naji kunya don Allah kayi hakuri nasan duk zata fada maka abunda ya faru tsakaminmu amma
ni abunda nayi mata a rashin sanine." Jahid yaji ya kara kaunar Asma'u yana ganin ba zai iya
janye kudirinsa akanta ba zai lallaba Momysa ta hak'ura ta barshi ya aure ta A halin yanzu ita
kurrum yake gani yaji sanyi Asma'u tw zame masa wani b'angare na jikinshi, take ya manta da
b'acin ran Momyna suka cigaba da hira shi da Asma'u Cikin shaukin so Sam! Ya manta ma
cewar a cikin gidan shi yake kuma a patlor Maman Salim zata iya jinshi, Aikuwa tana daki tana
tik'ar kukan takaici a zuciyarta tana ji ta tsani Asma'u tunda ta shiga tsakanin ta da mijinta da
suka Gina rayuwar su cikin aminci da yardar juna.

****
Mujahid ya nunawa Momynsa kamar ya janye maganar auran sa da Asma'u a b'oye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login