Showing 60001 words to 63000 words out of 95753 words
Chapter 21 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
Hutu cikin ya danyi k'wari sannan.
Granny na zaune ita kadai a parlor tana kallo muna shigowa tace "Naji dadin dawowar Ku da
ina zaune ni kadai kamar wata mayya, Dariya nayi na zauna kusa da ita cikin gajiya tace." Ina
fatan dai komai lafiya nasan dai ciki ne da ita."
'Yar Dariya nayi nace"Eh ciki gareta Dr ya bata magungunan Karin jini kuma ta kula sosai da
jikinta."
Wani irin farin ciki naga granny tana yi sai washe baki take yi tana fadin"Allah na gode maka
'yar nan ubangji Allah ya sauke ki lafiya naji dadin wannan al'amari dole zama ya kama ni a
gidan."
Tausayi tsohuwar ta bani ganin yanda take murna da farin ciki. Na kalli Mimi wacce take ta
b'oye k'walla ko ta mecece oho mata.
Bayan sallah azhar nayi musu sallama babu yanda basu yi dani ba kan in zauna in ci abunci
naki zama.
Ko da na koma gida Umma har ta sauke nata,zama nayi rumfar ta ina ci muna hira nan nake
fada mata Mimi ciki gareta, itama murna take sosai har da 'yar kwallar ta.
Ni dai mamaki nake ko kwallar me suke yi oho.
**********
Kullum Mimi sai ta kirani a waya tana min magiya kan naje gidan ta wai na taya ta zama kafin
ya dawo wataran sai na zage ta sannan muke dai-dai tawa da ita. Wataran ma kin d'aukar
wayar nake yi.
*******
Yau watan Amjadu Uku a chana Wanda yayi dai-dai da watanin auran su da Mimi komai yayi
masa yanda yake so, don haka sai ya fara shirye-shiryen dawowa gida.
Lokacin kuma Mimi tana fama da Matsalar ciwon ciki matsananci Dr Mujahid shine tsaye a
kanta scanning anyi mata sau biyar kullum Abu guda yake nunawa Cikin Mimi na zaune a
bayan mahaifa Mujahid ya tsorata mutuka duk scanning din da zai sanya ayi mata zai nuna
masa twins amma ko gurin wanne kwanciyar daban, daya cikin mahaifa daya a waje Innalillahi
wa'innailahi raji'un.
Duk wannan fad'in tashin da muke yi Sam bai sani ba domin Mujahid yace kar Wanda ya fada
masa, Ni kad'ai ya fadawa abunda yake faruwa nima tare da gargadin kar in fadawa kowa
saboda kwanciyar hankalin su duk da haka granny tayi mugun tada hankalin ta, saboda ta Dora
wa cikin Mimi son duniya.
Tuni na tare a gidan Mimi kusan wata guda kenan muke cikin wannan tashin hankali Mimi ta
fige tayi wata shegiyar rama sai uban haske gashi bata cin abunci sai nayi da gaske sannan
take ciki ko kuma taga raina ya b'aci kullum da daddare ta dinga murkususu kenan Cikin ta,
kuka nake yi sosai ina mata addu'a.
Ganin halin da take ciki yana kara yin gaba, ya sanya Dr tununin Sanar wa da Amjadu dole
kome yake yi ya aje ya dawo gida domin duba halin da gidan yake ciki, Duk da cewa kullum
yana kiran waya safe da dare amma kira da ban zuwa daban, Dr yana ganin dole ayi mata aiki
shine za'a samu maslaha. To ko da ya kira Amjadu din a waya ya fad'a masa abunda yake
faruwa bai wani nuna damuwar sa ba yace." Insha Allah yana kan hanya.
Zaman mu guri guda da Mujahid ya sanya wata matsananciyar soyayya ta shiga tsakanin mu,
gani nake yanzu nake soyayya Mujahid ya cika mutum mai kyawun hali da tausayi tabbas duk
macan da ta aure shi tayi dace da miji na saki jikina sosai dashi, domin shine yake kaini
makaranta cikin motar shi kullum, siyayya kuwa babu irin wacce baya min, har yaron shi sai da
ya kawo min ya yini a gurini
Grnay tayi ta tsokanar sa, sai dai yayi dariya kawai.
Ina dawo wa daga makaranta granny take fada min yau Mai gidan zai dawo domin yayi waya
bayan futa ta yace." Yana jirgi, shikkenan na nemi nutsuwata na rasa domin Sam bana kaunar
abunda zai sake hada ni dashi, tunanin hada kaya na nafara yi domun ina gudun cin mutumcin
da zai yi min a gidan shi....
*20/11/2019*
[11/21, 10:38 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*
*58*
Mimi na sanya tayi wanka ta gyara jikinta tsaf! Nima nayi wanka ban yi wata kwalliya ba, na
sanya atamfar mu ta anko Candy mu, ina kokarin zama kusa da ita tace." Asma'u ya kamata a
shirya masa abunci ko."? Kallonta nayi na minti biyu kana nace"Kina da tabbacin zai ci abincin
idan ka shirya masa nifa bana son wulakanci domin yanzu ma na had'a kayana tsaf! Zan tafi
inda nafi wayo."
Marairaice fuska tayi tace"Don Allah kar ki tafi yau kinji ki bari na warware tukkuna." Tsaki naja
tare da fad'in "Kinsan inuwarmu bata had'uwa guri guda dashi, bana son abun bata rai." Tace"
Ki rabu dashi don Allah duk abunda zai miki."
Shiru nayi kawai, Granny ta futo daga d'akinta da carbi a hannunta ta idar da sallahr la'asar, ta
kalli Mimi sai ta saki dariya tana zama kan kujera tace." Wato da kika ji Mijin ki na kan hanya
kinyi wanka tsaf har da kwalliyar fuska." Dariya nayi kadan nace"Dole tayi kar taje ki kwace
mata gakinan kin rambad'a kwalli har da sabuwar atamfa." Granny tace"Sai kiyi kuma komai
abunki bazan baki kwallina ba."
Dariya nayi nace"Ni ba kwalli nake so ba ki bani lallai me ja irin na k'afafunki."
Kallon k'afar tata tayi tace." Yana gidana nima Iyami ce ta kawo min daga garinsu, duk sanda
zata zo gidanan zan ce ta Zo miki dashi."
Nace"Yawwa granny ko yanzu ma a kira ta a waya ai tana da waya ko?"?
Granny tace"Tana da waya to wai ke meye kika damu da kunshi sai kace wata me miji, ki bari
mu masu miji muyi."
Dariya ta bani sosai nake yi nace"Ni ko nake da miji a hannu kin San shi don kullum yana zuwa
gaishe k.............Kafin in karasa ya shigo parlor tuni k'amshin turaran sa, ya mamaye parlor.
Yana sanya da Riga shart fara tas tana da gaje ran hannu, wando jikinsa jins ne blue ya sanya
fencing cap (hana sallah) idanunsa sake da bakin glass wuyan shi wata siririyar sark'e ce silver
sai shek'i take, hakama a gogon hannun Shi, shi kanshi blet din da yayi amfani dashi abun kallo
ne kafin kazo kan takalmin k'afar shi, booth mai igiyoyi blue colour in da kasan bature haka ya
koma.
Duk zancan da Asma'u suke da granny a kunne shi.
Fuskarsa murtuk! Ya tsaya bakin kofa, yana karb'ar wayoyin shi daga hannun Rambo
Granny ta washe baki tana fad'in"Oyoyo angon karni ya dawo sannu da zuwa angon Aishatu
sannu da zuwa."! Mik'ewa tayi karasa bakin kofar sai washe baki take, fuskarsa ya saki kad'an
ganin kakar tashi ya rungomta jikinsa hade da sumbatar goshin ta yana fadin"Granny na same
Ku lafiya."? A sake tace." Lafiya ba lafiya gaskiya amma shige ka huta tukkuna." Hannunta ya rik'o suka k'araso parlor, ina kallon Mimi ta yunk'ura ta mike tsaye ta nufi inda
suke, sakin Granny yayi ya kamo ta ya rungume ta hadda lumshe ido! Kauda kaina nayi da
sauri ina da na sanin zama na a gurin.
Fuskar ta ya d'ago da hannunshi yace." Momyna haka kika koma."!? Mimi ta fara k'walla, saurin
rungume ta yayi yana Dan dukan bayan ta kad'an cikin sigar rarrashi yace." Sorry baby na ya
taso ki a gaba kiyi hakuri insa Allahu zaki warware."
Kungunta ya riko har suka k'araso tsakiyar parlor.
Ya kalleni a d'age. Nima na kalle shi babu yabo babu fallasa.
Wuce wa yake kokarin yi, granny tace "Zaka wuce baku gaisa da Asma'u ba, yarinya hazika
kuma jajurtacciya ta tsaya kan matarka sosai, gaskiya samun me zumuncin ta sai an tona."
Babu yabo babu fallasa tace." Granny na ganta ai ni da ita waye zai fara gaida wani ko banza
na girme ta nesa ba kusa ba, bayan haka kuma a gidana take dole ta girmama ni."
Tsaki granny Taja tana fadin"kai dad'i na da kai kenan,son girma kowa ai da irin tashi fahimtar
ko kaga ka wuce bata gaishe ka ba."
Fuskata na saki don kar in kunya ta granny nace"Sannu da zuwa ka dawo Lafiya. "? A fakaice
ya kalle ta, yayi saurin dauke kansa, jin muryar ta ya tayar masa da abubuwa da dama, yana
tafiya yace." Lafiya k'alau na dawo."
Bedroom d'insa ya shige da Mimi rungume a jikin sa.
Wanka ya shiga ya futo Mimi na kwance kan bed ya kalleta cike da tausayi ya dawo da
matsananciyar sha'awa babu hali domin akwai rashin imani ya kusanci Mimi duba da halin da
take ciki.
Sabbin kaya ya sanya ya shirya tsaf dashi kana ya zauna kusa da ita.
Mik'ewa tayi zaune cikin kasala, shi kuma ya tsira mata idonsa.
A hankali yace." Momy kin rame sosai laulayi ya sanya ki a gaba ko." ? Mimi tace." In laulayi ne
kadai da sauk'i kullum da daddare fa bana iya bacci ciwon ciki, Dr Mujahid ne a tsaye a kaina
sai Asma'u, domun ta dalilinsa take zaune a gidanan tunda shi ya tursasa ta, yana da kirki
wallahi, kusan kullum sai ya shigo ya duba ni."
Fuskarsa ya kirne! Kamar bai tab'a Dariya ba yace." Kina so kice min kun karya mun doka ke da
Asma'u, bana nan kuna shigo mun da k'ato cikin gida. "!?
Mimi ta tsorata ganin yanda yake zare mata idonsa.
Tsawa ya buga mata tare da fadin" Kinyi shuru ki bani amsa ta."
Gyada kanta tayi tace." Tun ranar ya ganmu zamu hospital shine ya dauke mu a mota can
asibitin su ya akaimu shine ya sanya akai min duk wasu gwaje-gwaje."
Mik'ewa yayi tsaye da sauri ya nuna ta da hannu Cikin daga murya yace." Da kika kirani a waya
me na fada miki."?
Mimi tayi shiru gabanta sai fad'uwa yake yi.
Ni da granny duk muna jiyo hayaniyar shi, yace." Ko ba cewa nayi dake kar Ki sake ki bi ra'ayin
wancan yarinyar ba, wato ni ban Isa dake ba kenan , in banda lalacewa da kudina da komai Ku
shigo mun da wani banza cikin gidana bayan bananan, me hakan yake nufi."!!? Mimi har ta fara
kuka tana bashi hakuri Cikin banbami masifa ya cigaba da cewa" Nace dake akwai kudi a dakina ku yi amfani da ko
nawa ne, shine zaku zumar mun da mutumci, ni d'an maula ne."!? Ya fada da wata irin tsawa.!
Mamaki ya kamani jin wata irin magana tana futowa daga bakinsa, dama alkairi yana koma wa
sharri ? Me ya kawo maula cikin taimako na tabbata Mujahid bada wata NIYYA ya taimake Mimi
ba sai dai hakkin makota ka.
Shashshekar kukan Mimi muka ji nida granny sai hakuri take bashi shi kuma yana kara fusata
sai hayaniya yake mata cike da rashin tausayi.
Cike da b'acin rai granny ta mike tana fadin"Wannan rashin hakuri dame yayi kama? Daga
zuwan ka, ka fara fad'a ki tausayi babu, wato kai duk irin abun da akai maka na taimako baka
gani."
Dakin ta bude ta shiga tana cigaba da fad'an ta.
Mimi tace"Don Allah kayi hakuri wallahi ba laifi na bane."
Da sauri yace." Dama nasan ba laifin ki bane nasan me zuga ki, duk abunda kike yi tunda da
kunne na naji."
Granny tace"Kai ko daga dawo wa zaka soma tashin hankali ka duba halin da take ci ki mana,
kila da bama gidan dukan ta zaka yi ko."? Ranshi a bace Yace. " granny a gaban ki ake shigo
min da namiji gida bananan,duk da cewa makoci na ne, amma shigowar shi cikin gidana bashi
da wani amfani mutukar bani na kawo shi ba, kuma nasan dalilin da yake kawo shi gidana,kune
kuke ganin taimako ne yake kawo shi ni za'a rainawa hankali."!
Ya k'arashe maganar sa cikin hayaniya.
Duk ina jinsa, a zuciya ta nace"Ikon Allah daga taimako ya koma tashin hankali, mik'ewa nayi
da sauri na nufi bedroom din Mimi domin in fara had'a kayana zama bai ganni ba.
Granny rarrashin Mimi take sosai ganin yanda take wani irin haki! Ya tsorata sosai, ta zauna
kusa da ita tana fadin "Kiyi hakuri ki daina kuka shi namiji ba'ayi masa haka, kinga yanzu kin
nuna masa langon ki." Ita dai Mimi hawaye kawai take sharewa tana mamakin jarabar mijin nata
.
Shi kam Amjad tuni ya bar dakin. Ko da ya futo yaso ya samu Asma'u a zaune ya wanke ta tas
sai yaga bata gurin, k'wafa yayi a fili yace."Zamu hadu dake kema."
Parlor ya zauna hade da Dora kafa daya kan daya ya k'urawa TV ido sai faman huci yake.
Futowa nayi daga bedroom din bayan na gama hada kayana,kawai na ganshi zaune da har zan
koma ciki kawai na dake sosai Nazo na gifta shi zan nufi kicin, k'afar shi ya sanya ya tad'o tata
cike da mugunta
Taga-taga nayi zan fad'i da sauri na rike hannun kujera, sai ya sanya hannunsa guda da k'arfi
ya buge min hannuna na fad'a jikinsa kaina ya daki k'irjinsa.
Kafin inyi wani yunkuri ya ture ni daga jikinsa hade da Jan tsaki, yana min wani irin kallo.
Kamar zan fashe da kuka na mike tsaye hade da d'aukar dankwalina da ya cire na d'aura.
Murya na rawa nace"Allah ya Isa wallahi."
Zuba min ido yayi yana kallona.
K'irjina nayi saurin kalla ganin shi yake kallo, saman breast dina duk sun futo dama kaida ne
hakan.
Tsaki naja nace"Iskanci a cikin gidan aure Allah ya raba mu da irin auran wannan mazan." Kicin
din na wuce da sauri ina hard'ewa nasan kallona yake yi.
Dauke kansa yayi bayan shigowar ta har yanzu ya rasa wane irin hukunci zai yi ma yarinyar .
Tsayuwa nayi tsakiyar kicin din ina tunanin abunda ya kawo ni, minti biyu na tuna Mimi nake so
inyi wa miyar ogon da hanta, kullum nake mata taci da bread ko gurasa domin su kadai take iya
ci,sai wainar fulawa, gurara sa, Mujahid ne yake jigilar kawo mata, in bashi ba, Umma ta aiko
mata.
Cikin sauri na fara had'a abun bukata, Allah-Allah nake in gama in bar gidan.
Ina tsaka da Yanka hanta ya fad'o kicin din.
Saboda tsoro saura kadan in yanke hannuna. Jarumta na aro na daure fuska ta tamau.!
Cikin yanayin tafiyar shi ya k'araso inda nake tsaye. Ya kalleni shekeke tare da fad'in "Mara
kunya Nazo ki maimata min zagin da kika yi min."
Cike da mamaki nake kallon shi, zallahr fitina na hango a kwayar idon shi, shiru nayi masa na
cigaba da abunda nake yi.
Fuzgo ni yayi da sauri bisa tsautsayi knife din hannuna ta yanke ni, a Dan ya tsaya. Da sauri na
aje ta ina yarfar da hannun Cikin azabar zafi, sai cije bakina nake.
Gurin yarfar da hannun nawa duk na bata mishi kayan jikinsa.
Ko a jikinsa, zare min ido yayi yace." Wane d'an iskan ne, yace ki shigo min da saurayin ki
gidana."
K'walla ce take kokarin zubo min, ga zafin da nake ciki ga jarabar sa.
Shiru nayi ina kallonsa, yace." Zaki daina kallona ko sai na tsone miki ido! Nace"Wane shegen
ne yasa ki shigo min da wancan banzan gida, ko an fada miki kowa ma irin ki ne."!
Murya ta na rawa nace"Kullum baka da zance sai gida-gida dai gida-gida wai meye a cikin
gidan ne? Da har kake ihu! Ina ce duk gida sunan shi gida mutukar za'a shiga a kwanta a
cikinsa, sannan za'ayi kashi da futsari a cikinsa, ko da ko gidan bunu ne Wanda aka yi da
karare sunan shi, gida kuma bashi da maraba da Wannan da kake magana a kan sa."!
Mari! Ya kai mata a fusace! Yace." Ni kike kokarin fad'awa magana Cikin gidana, na fad'a
gidana idan kinyi zuciya kar ki kara zuwa balantana kiyi min shirme dama rashin zuciya ne,
tuntuni na fad'a miki bana son ganin k'afar ki a gidana ko. Ba haka ba."!? Ya fada cikin sigar
rashin mutumci.
Cikin mugun takaicin sa nace"Tabbas gida gidan ka ne, kuma dole inzo gidan nan,tunda 'yar
uwata na cikin sa, da bata cikin gidan kai kanka kasan babu abunda zai had'a ni da kai."
Tsaki yaja ya nuna ni da Dan ya tsaya "Wallahi wannan ne na farko da k'arshe a gurin ki ko da
wasa kar ki kara shigo min da wani banza cikin gidana."
Cikin sigar kuntatawa nace"Mutum da kake magana akan shi ni yafi min daraja a kan ka, so ina
mutukar jin ciwo idan ka zage shi."
A kufule yace." Owk don Allah kiyi gangancin sake shigo min dashi gida, Wallahi ke dashi sai na
daure Ku! Duk iskancin da zakiyi kije kiyi shi a waje ya fi miki sauk'i ba sai kin kawo min gardi
gida ba."!! Wani irin kallo nayi masa sai naga duk ya wani burkuce sai hura hanci yake!
Nasan na kular dashi
Nace"Allah sarki My Jahid hummm yanda ka dauke shi shi ba haka yake ba, a tunani na kai
zaka yi shaidar shi, tunda ka rigani sanin sa, wallahi tunda nake dashi ko gyalena bai tab'a
rikewa ba, balle har ta ja shi ga tab'a jikina."!
A hasale! Yace." Me kike nufi."?
Shiru nayi mishi ina kokarin barin gurin.
Jawo ni yayi da sauri ya matse jikin bango, muka fara kallon juna ni dashi. Murya ta na rawa
nace"Kasan da wannan abun da kake aikata wa haramun ne ko? Idan da Kayi