Showing 30001 words to 33000 words out of 95753 words
Chapter 11 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
zauna a haka, kawai a aura mata Wanda zuciyarta take so
ta huta da wannan azabar da take sha."
Umma tace." Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Mimi bata da Miji sai Amjadu dole a bawa
zuciyarta hakuri abata abunda take so."
Ya Aminu ya kalleni ya kalli Umma zuciyarsa nayi masa wani irin ciwo yace." Umma don bani da
kudi bani da aikin yi bani da mota bani da babur bani da keken hawa kana bani da kudi a banki
kuke mun haka,? Meye laifi na meye? Aibuna anan Zan kula da Mimi zan tsare mutumcin ta
zan sanya ta farin ciki! Umma kar Ku kware min baya akan Mimi Ku duba halin da zan shiga a
kanta soyayyar ta tana iya kashe ni!!!!! Umma ni danki ne baza ki so wani bayan ni ba, Umma ki
dube ni da idanun rahama!! Ki tuna so da kaunar da kike min Umma ki bani Mimi domin itace
farin cikin rayuwata."!!!!!!!! Ya k'arashe maganar sa hawaye na zubowa daga idanunsa
Umma ta zube a gurin Tare da dafe k'irjinta tana salati aunt Hauwa da Ummansu Munnu suka
rike ta hawaye ne ya fara zirarawo daga idanunta muryarta na rawa tace"Ya Allah ka ije mun
wannan masifa da ta tun karo ni, Allah ka sanyaya min kasa kawo karshen wannan badak'ala!!
Sai hawaye sharrrrrrrr-sharrrrrrrr suka fara zuba a kuncinta. Duk taurin zuciya irin ta aunt Hauwa hawaye ta fara sharewa ganin Umma tana kuka abunda
zai sanya Umma kuka ba Karami bane hakuri kurum suke bata
Ni ko da sauri na bar gurin bayan na warce wayar Munnu dake tsaye, wani d'an korido na nufa
dake Cikin asibitin na fara Neman numbar sa, sai da tayi ringing sai uku ba a dauka ba,
Sai ana hudu ne ya dauka muryarsa da yanayin bacci yayi sallamsa da sauri nace." Kanwa ta
kar tsami! Kwarna fi ya kwanta. "!!!! Jin muryar yarinyar ya sashi mik'ewa zaune da sauri hade
da yaye blanket din jikinshi na ci gaba da cewa " Yanzu haka muna babban asibiti na zana Mimi
a kwance rai a hannun Allah bayan tafiyar ka, jini ya tsinke mata ta baki ta hanci!!!! Ta galabaita
mutuka duk ta dalilin ka!!! Ina kara fada maka duk abunda ya same ta Kaine sila Kaine!
Mujaza!! Mahaifiyar mu ta zubar da hawaye akan haka, mun zubar da hawaye a kan haka, duk
wani mai imani ya kalli Halin da Mimi ta shiga a yanzu sai ya tausaya mata, insha Allahu duk
wani sharrinka sai ya koma kanka ka cuce mu, ka yaudare mu, Ka azabatar da zuciyar Mimi
akan sonka kullum kana fada cewar zaka aure ta, alhalin karya kake!!! Wallahi mutukar ka bari
Mimi ta mutu baka yi Wani Abu akai ba nima sai na kashe ka."!!!!!!!!!!! Kamar wata mahaukaciya
haka na k'arashe maganar..... Wata irin zufa ce ta keto masa duk da cewar akwai AC a dakin
Muryarshi sanyi k'alau yace." Asma'u.!!! " saurin kashe wayar nayi na zube a gurin hade da
fashewa da kuka mai cin rai.
Mik'ewa yayi da sauri ya duro daga bed din toilet ya nufa ya dauro alwala ya futo yana kallon
agogo bango uku shaura na dare,
Jallabiya ce a jikinsa sai garan wando ya dauki wata rigar sanyi sa mai hula ya sanya kai a
gogonsa ya d'aura ya dauki key ya futa da sauri.
Rbow suka ji ana kokarin tada mota hankali a tashe suka futo daga gurinsu, suna tambayar sa
yace." Su koma kawai shima yanzu zai dawo jikinsu duk babu k'wari suka tsaya a gurin har sai
da suka ga futar shi Daga gidan.
Kai tsaye......Asibitin Zana ya nufa zuciyarsa kwata-kwata babu dad'i abun yana mutukar bashi
mamaki shi dai yasan babu wata Kalmar so da ya tab'a fadawa Mimi wacce har suke zargin sa
da ya yaudara ta, maganar auran ta kuwa ya fada ne saboda son da take masa gami da ganin
yanda suka shak'u da Asma'u yana ganin ko ya aure su su biyu ba za a samu matsala ba,
yanayin dabi'un Mimi da nutsuwar ta gami da kunyar ta suna bashi sha'awa amma zallah so
gangariya babu Wanda yake wa sai Asma'u duk cikin 'yan matansa babu wacce ta samu
wannan matsayin kamar ta hak'ika Asma tana da babban matsayi a zuciyarsa.
Da wannan tunane-tunanen ya Isa asubitin, Madi suka bude masa kofar ya shigo cikin sauri
suka biyo motar da gudu yana parking suka bude masa kofa suna yi masa barka da zuwa.
Amsa musu yayi babu yabo babu fallasa, ya wuce ciki.
Suka tsaya suna binshi da kallo tare da tunani wane dalili ne ya kawo shi asibitin ? Suna zargin
yau ya zagayo su ne duba marasa lafiya da. da bada tallafi kamar yanda ya saba, murna suke
sosai yau zasu cika aljihunansu.
Wayarsa ya futo da ita yana laluben numbar da ta kira shi da ita yanzu....
*10/November/2019*
[11/11, 9:19 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*
*48*
Ringing d'in wayar ne ya dawo dani cikin hankalina wayar na duba sai naga numbar sa, da
kamar kar in dauka wata zuciyar tace"Dauki kiji me zai ce miki.
Jin alamun ta daga wayar ne yasa yace." Gani cikin hospital din ki futo kiyi min jagora har inda
kuke."
Bai saurari Abunda zata ce ba ya kashe wayar sa.
Futowa nayi daga gurin da nake.
Har yanzu suna tsaye kan Umma sun yi mata rumfa Aminu sai fiffita yake mata.
Aunt Hauwa ta kalle ni tare da fadin"Da ina kika shiga tun d'azu. "
Cikin wayan cewa nace"Futsari naje nayi."
Raba ido nake yi a gurin ko Allah zai sanya I n hango shi
Da yanayin tafiyar shi na gane shi.
Shiru nayi har ya k'araso gurin.
Cike da mamaki suke kallonsa.
Ya mik'awa Aminu Hannu su gaisa.
Da kyar ya mik'a masa nasa hannun kamar yanda yayi masa jiya.
Umma ya kalla yace." Umma Ashe bayan tafiya ta jiki ya rike CE."
Umma ta gyara zamanta hade da gyara mayafin ta tace"Wallahi kuwa aman jini take sosai."
Gaban shi ya fadin jin abunda Umma tace, Yace." Bari in ga dector babu matsala insha Allahu
komai zai zo da sauki."
Binsa mukayi da kallo har ya shige ciki abun mamaki babu Wanda ya hana shi shiga cikin
ma'aikatan sai ma da d'a gyara masa hanyar wuce da suka yi.
Kamar yanda dector ya yiwa Kawu Baya ni haka yayi Amjadu baya ni Wanda ya gamsar dashi
kuma shima ya gane kan ciwon Mimi kamar yanda Asma'u take fada cewar ciwon sonsa ne
yake damunta.
Yace." Doctor yanzu kun gama komai ko."? Gyada kai Dr yayi tare da fadin"Mun gama komai
dasu domin har sunje sun karb'o magani a pharmacy kuma yanzu na sanya nurse ta bata
maganin babu matsala insha Allahu mutukar an bi doka."
"Yanzu sauransu biyan kudi domin yanzu nake cewa Narse ta zo mik'a musu rasit." Yace."
Kar ka damu insha Allah ka bani numbar accont din Ku na hospital din sai a turo maku hakkin
Ku.
Da sauri Dr ya dauki 'yar k'aramar ta karfa da biro ya rubuta masa hade da mik'a masa, ya
San ba iya kacin kud'in su zai tura musu ba Dole sai yayi musu kari, tunda dama ya saba kawo
musu ziyara a sibitin.
Har ya mike zai futa sai kuma ya tsaya tare da fadin"Yanzu babu halin a ga yarinyar. " ? Dr
ya mike da sauri yana fad'in"A'a Yallab'ai kai zaka iya shiga ka ganta."
Tare suka shiga room d'in da Mimi take kwance bacci take sosai sai dai har yanzu nuffashin
ta bai gama dawo wa normal ba. Dr ya futa hade da jawo masa kofar , ido ya tsura mata sosai
yake kallonta mace har mace tana Neman ta jefa rayuwar ta a wahala.
Domin shi a ganinshi wahala ce,kaso Wanda bai San kana yi ba, bai tab'a tunanin son da
Mimi take masa ya kai haka a zuciyar ta, sai yaji zuciyar sa tana ce masa da ma wannan
Soyayyar daga gurin Asma'u ka same ta daka ji dad'i. Amjad mutum ne mai mutukar son a
dunga tattashin sa da rarrashin sa kulawa da soyayya, shiyasa yake addu'ar Allah ya bashi
mace wacce take da wannan azanci domin matan ma suna suka tara.
Yafi minti goma a tsaye a kanta yana kallonta, kokari yake yaji wani abu wanda ya shafi so
ya darsu a zuciyarsa a game da ita, bai ji komai ba sai dai tausayin da taye mata da kuma
kaunar da yake mata saboda sunan Maman shi, Wanda ba ita kadai yake wa wannan kulawar
ba, mutukar A kace kina da suna Aisha to zaki samu kulawa sosai a gurin shi.
A gogon dake daure a hannunsa ya kalla hud'u shaura na Asubah. Gyad'a kansa yayi ya
bude kofar dakin a hankali ya futa, har yanzu suna zaune a inda suke sai dai sun matso cikin
wata rumfar kwano dake gurin saboda sanyin asubah. Sosai suka bashi tausayi mussaman
Asma'u da ya ganta tayi wujuga-wujuga da ita ga idanunta sun kode. daga nesa ya tsaya tare
da fadin "Umma ni zan wuce Allah ya bata lafiya."
Umma tace"Ameeen suma ameen mun Gode k'warai da kulawa." Kallona naga yayi a fakaice
sai kuma ya kalli Aminu dake dauke dauken kai ya mik'a masa hannu domin suyi sallama.
Da kyar Aminu ya bashi hannunsa, Amjadu ya wuce yana mamakin abunda Aminu yake yi
sai kace jahili in banda dalili ya kai dalili Aminu ya Isa yaga inuwar shi ma ballanta ya hada
hannu dashi, duk sanadin Asma'u ne.
Sai da ya shiga motar sannan ya kira ta a waya, ina jin wayar na ringing naki dauka Munnu ta
karba daga hannuna tana dubawa. Mik'a min tayi tare da fadin"Shine." Aunt Hauwa tace" Sai ki
tashi kije mybe akwai abunda zai ce miki."
Kallon da Umma tayi min ne yasa na mike da sauri na bi hanyar da naga ya bi.Na gane
motar shi tunda duk inda suke basa b'uya bayan haka kuma gurin da haske.
Kallonta yake yana daga cikin motar har ta k'araso. Ajiyar zuciya ya sauke babu wasa a
tartare dashi ya bude motar tare da fadin"Shigo muyi magana dake ta fahimta."
K'in shiga nayi na tsaya ina kallonshi. Shima ya kalle ni babu fara'a yace." Time d'in sallah ya
kusa ki shigo muyi abunda zamuyi in tafi gida Ok."
A hankali na shiga motar na zauna ina kauda fuskata. Ya kalle ni na minti uku, kana yace."
Wannan kukan da kike yi Sam! Ba zai miki maganin komai ba sai dai ma ya kara sanya miki
damuwa da ciwon kai, Yanzu shawara zamu yanke dake idan kin amince ni mai sauki ne."
Kallonshi nayi ina d'an ya mutsa fuskata nace"Ina jinka." Shiru na minti biyu bai ce komai ba
yana kallona, na dago kaina hade da watsa masa harara nace"Kace lokacin sallah ya kusa
amma kuma ka sanya ni a gaba kana kallo kamar tv."
Ajiyar zuciya ya sauke hade da lumshe idonsa, k'asa-k'asa naji yace." Asma'u Allah ne kadai
yasan ita a dadin kaunar da nake miki a cikin wannan zuciyar tawa, tun da nake a rayuwata ban
tab'a furta wa mace WANNAN Kalmar ba sai ke, duk da cewar nayi rayuwa da 'yan mata iri-iri
masu kyau da kudi Asali nasaba da wayewa amma babu wacce ta samu wannan Kalmar sai
ke."
Shiru nayi sauraron shi. Ya cigaba da cewa "Ina da kudi sosai Wanda ban San iya a dadin su
ba kuma kullum karuwa suke yi ina zakka da duk wani Abu da Allah yace kayi da dukiyar da ya
baka amana, Abu guda ya rage min mata, kuma na samu insha Allah." Shuru Yayi na minti biyu
ya cigaba da cewa "Mimi ta bani tausayi mutuka nasan illar so, tabbas tana so na, Wanda naji a
zuciyata dama kece kike min irin son da take min da babu namijin da ya kaini dacewa a duniyar
nan."
Kallonshi nayi jin abunda yake fada.
Dauke kaina nayi hade da d'an ya mutse fuskata nace"Me yasa ka yaudari Mimi kasan baka
son ta."
Shiru yayi yana nazarin magana ta can naji yace." Da farko da wasa nake yi, amma daga baya
na d'aura niyyar auranku tare domin in cuzguna miki dalilin yin haka kuwa shine Rashin
mutumcin da kika je kikayi gurin pary Ku ya bani haushi shiyasa na yanke wannan shawarar."
Murmushi nayi me ciwo nace"Idan domin ka bani haushi kace zaka auri Mimi a lokacin
wallahi da baka wahalar da kanka,saboda kasan shi so sai ana kishin mutum ake yin sa, Mimi
tana sonka tana kishin wani ya rab'e ka ciki kuwa har da ni, Mimi ita yafi da cewa ka aura bani
ba."
Fuskarsa ya Dan hade yana kallona tare da k'ankantar da idanunsa yace." Gashi ni kuma
ba Mimi nake so ba ke nake so, sai dai idan kin yarda in hada ku, Ku biyu in aura amma duk
abunda ya biyo baya kar kiyi kuka dani."
Ba tare da tunanin komai ba nace"Ni dama akan wannan k'adami nake, Ya Aminu dole ya
janye maganar auran Mimi idan yak'i janjewa nima nace bazan aure ka ba, sai dai duk mu
hak'ura dama ni ban damu ba, itace abar damuwa."
Gabanshi ya fad'i jin abunda take cewa, tana nufin idan Aminu bai janye maganar auran
Mimi ba itama baza ta aure shi ba? Lallai a kwai badakala anan gaba, idan Aminu yak'i janje
maganar shima ya kusa fadawa chakwakiya kenan, yanzu zai canza salo domin ya risinar da
zuciyarta iya zaman shi da ita ya fahimci yarinya ce me mugun taurin kai da kafiya.Dole ya
nema wa kansa mafuta domin bai San abunda zai je ya dawo ba nan gaba.
Shiru motar tayi bayan na gama magana ta. Yace." An sanya wata uku na auranmu ina ganin
za'a kara sauko da lokacin k'asa saboda gudun wata masifar, ki San yanda zakiyi a gida ki ga
Aminu ya janye kudirin sa daga kan Mimi ni kuma zan aure Ku ga ba d'aya."
Motar nake kokarin bud'ewa ina fadin"Kai kake damun kanka da lallai sai ka aure ni, nifa idan
Ka aure duk d'aya idan baka aure ni ba ma duk d'aya ne, mutukar ka aure Mimi da ka sanya ta
fad'a komar ka shikkenan bukata ta tabiya domin likita yace zuciyarta daf take da ta buga."
Ina gama magana ta na bude motar hade da fucewa a fusace.!! Kallo ya bita dashi cike da
mamakin gaud'ancin ta yarinya mai baud'andan ra'ayi shi a yanzu ma ya rasa in da ta dosa.
Jikinsa babu kuzari yaja motar ya tafi zuciyarsa na masa wani irin ciwo idan ya tuno kalaman ta
wai bata son sa, wannan kalma ta nayi masa mugun ciwo ya za'ayi ya auri macan da zata dinga
gasa masa magana ko wace iri CE, da Alama Asma'u baza ta kula dashi. Mimi ita ke son sa
sosai da sauran 'yan matansa tabbas a gurin su zai samu irin kulawar da yake buk'ata.
Bayan munyi sallah gari yayi haske sai ga Babansu Munnu ya shigo a sibitin cikin motar sa,
dama jiya gida ya koma saboda b'acin ran Aminu.
Da sauri muka mike ni da Munnu muka karasa gurin da yayi parking din ya futo muka gaishe shi
hade da karb'ar kayan dake hannunshi, k'aton Fula's din tea ne sai wata Leda babba cike da
bread da kayan shayi dangin su madara da Milo gaba yayi muka bishi a baya.
Cikin mutum ci suka gaisa da Umma aunt Hauwa ta gaida shi Aminu baya nan domin ana
idar da sallahr ya tafi gida, kai tsaye..... Ciki ya shiga gurin dector
Ni da Munnu ne muka had'a wa kowa tae d'in shi ga manya manyan bread nan kowa ya
dauki Wanda yake so, Ni kam tea din kawai nake kurb'a bakina babu dad'i fargabar rashin
lafiyar Mimi da tunanin maganganun Amjadu na d'azu, nayi mamakin yanda yake k'aryar min da
kai da sanyayyar murya yake fadin Yana sona, mutum me kudi kyau mukami izza da ginshera
duk ya na dasu, amma d'azu duk ya aje su gefe, gaskiya na gazgata maganar shi, tab'e bakina
nayi kawai na cigaba da kurbar tae din amma lokaci zuwa lokaci sai in ji gabana ya fad'i tsigar
jikina ta mike idan na tuna shi.
K'arfe Takwas dai-dai wata nursa ta futo tace"An futa da Mara lafiyar yanzu zaku iya shiga Ku
ganta duk da cewar ma yanzu za'a baku sallama." Da sauri muka mike dukaninmu muka fara
turereniyar shiga duba Mimi.
Tana zaune kan gado tayi wani firgai-firgai da ita fuskarta ta kode ta kara wani ufan haske
Mimi da ma ba jikin arziki ba tayi wata irin rama lokaci guda. Umma na ganin ta sai hawayen ta
ya dawo ta zauna kusa da ita hade da iri hannunta