Showing 15001 words to 18000 words out of 95753 words

Chapter 6 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

aure ku
dake da 'yar uwarki Asma'u."
Gyada kanta tayi tace"Ya fada ma Umma."
"Masha Allah." Ya fada da murmushi a fuskar sa, shiru na minti biyu sannan yayi gyaran murya
tare da fadin" Shikkenan kije gida sai munyi waya, sai ki kira min *Asma'u* itama muyi zance
kamar yanda mukayi dake."
Jiki babu k'wari Mimi ta bude mota ta futa, ya bita da kallo had'e da fadin "Kar ki manta fa ki
kashe wayar ki, kafin in kwanta ina son jin muryar ki." Mimi taji wani sanyi ya tsirga mata a
zuciyarta murmushi ta saki tare da fadin"Insha Allah."
Hannu ya d'aga mata ta tsallaka titi kana ta shiga layin su.
Umma na zaune a inda take tace"Har ya tafi."? Mimi tace"A'a Asma'u yace." A kira masa."
Umma tayi shiru cike da mamaki tace." Asma'u Kuma. " daga Kai Mimi tayi.
Ina kwance a dakin ina jinsu sama-sama, domin bacci ya soma hawa kaina.
Ina jin sanda Umma take fadin "Sai kije ki kira ta tana daki."
Mimi ta shigo dakin hade da tsayawa a kaina tana kiran sunana.
Banza nayi mata.
Tace" nasan dai kina ji don yanzu ba lokacin baccin ki bane, kije Amjadu yana kiran ki."
Mik'ewa zaune nayi nace"Uwar me zanyi masa."
Tace"Idan kinje sai kiji."
Yanda ta fad'i maganar na gane taji zafin zagin da nayi.
Tsaki nayi na koma na kwanta.
Tace.don Allah ki tashi kije babu kyau wulakanci."
Ina daga kwance nace"Kin San Allah Mimi babu inda zanje domin ban ga tsiyar da zan masa
ba.
Futa tayi daga dakin.
Can naji Umma na kwala min kira.
Mik'ewa nayi da sauri na futo tsakar gidan INA amsawa
Fuskarta a hade tace "kije kiran da ake miki ko ranki ya b'aci."
Shiru nayi raina a bace
Cikin tsawa tace." Ko bakya ji ne."
Nace" Tom Umma" dakin mu na koma na zurmo hijabina na sallah na futo silafas na zura a
kafata na futa.
Tsayuwa nayi a waje ina tunanin ko in lab'e a wani gurin ne. ?
Wata zuciyar tace" kije ki kare masa rashin mutumci tunda yazo unguwar Ku.
Aikuwa tafiya nayi inda nasan zan ganshi
Can na hango motar shi kasancewar ya kunna futular motar.
Ina zuwa gurin na buga motar da k'arfi. Budewa yayi hade da haske fuskata da hasken wayar

shi, kalon-kalon muka fara ni dashi. Gani nayi ya kauda kansa yana dariya
Haushi da takaici suka kama ni, sai kace mahaukaciya ya tasa ni a gaba yana dariya. Cike da
takaici naja tsaki hade da juyawa da niyyar tafiya, ji nayi an fuzgo min hijabi da k'arfi na fada
cikin motar.
Jikinshi ya kwanto kaina ya rufe motar hade da sanya mata security, kallonshi nake a tsorace!
Naga fuskarsa a mutukar murtuke Yayi bala'in shan kunu irin Wanda bai tab'a yin irinsa ba,
Ya hasko fuskata sosai da wayar shi, Yana kallona tare da ya mutse fuskar sa.
Kauda kaina nake ganin yadda ya dallare min ido.
Hannunsa guda ya sanya ya shak'o wuyana dake cikin hijabi, Murya k'asa-k'asa yace." Maimata
irin zagin da kikayi min a waya jiya." Kifkifta idona kawai nake, ya k'ara shak'e min wuyana hade
da d'aga kaina sama sosai, yace"Ko bakya ji ne."?
Da kyar na samu na kakaro magana nace"Sakar mun wuya kar ka kashe ni."
Kin saki yayi sai ma kara damk'e wuyan yayi, hannuna guda na sa ina kokarin b'anb'are
hannunsa daga jikin wuyana, ko motsi ya kiyi, wuyana yayi bala'in sagewa, nace"Ka Sakar min
wuyan....... Ka tsani Yayi ta hanyar fad'in" Ki maimata irin zagin da kikayi min jiya Zan sake ki."
Babu wasa a cikin maganar sa.
Hawaye na ziraro min nace"Wane irin zagi nayi maka, duk abunda na fada maka gaskiya na
fada ciki babu sharri ko kashe ni zakayi sai dai ka kashe ni."

"Very good."!! Ya fad'a yana k'ara bank'are min wuyana sama, cike da mugunta, yace." Na lura
da abunda kike so in yi miki ni kuma bazan yi ba, na daina hora ki da abun domin na lura yana
miki dad'i shiyasa kike bukatar haduwar mu, Yanzu zanyi miki horo ne irin na gidan prison. "
Kasa magana nayi saboda yadda naji mak'o gwarona ya bushe, Hannu ya sanya ya cire hijab din jikina, na rintse idona saboda nasan babu rigar arziki a jikina
wata vest ce mai kama jiki sosai kuma iya kacin ta cibiya ta, domin nayi shirin bacci Mimi ta
tashe ni shine kawai na zura hijab din a kai.

Miskilin murmushi ya saki tare da cije lips d'insa yace" Surprise!" Wato dama kin tawo da shirin
ki kenan ko."? Shiru nayi masa wasu zafafan hawaye na zubo min a Kumatuna.
Murmushi yayi had'e da shafa sajan shi yace."Wannan karon baza ki samu abunda kike so ba,
domin na fara nisanta kaina dake, sai kije gurin wannan saurayin naki mai kama da alade,sai
Yayi miki wasa dasu."

Shashshekar kukana ce ta fara futowa fili ina mugun Jin ciwon rashin mutumcin da yake min.

Muryarsa a kaurare! Yace." Wancan karon kin min lafi nace ki bani hakuri kink'i OK wannan
karon ki bani hakuri ko kuma in dauki mata ki nag gaba a kanki."

Cikin shashashekar kuka nace"Babu hakurin da zan baka tunda banga laifin da nayi maka, ba,
kuma bak'i mai kama da alade da kake magana a kansa gwara min shi sau dubu a kanka, Allah
ne ya hallice shi a haka. "
Gyada kansa yayi tare da fad'in"Wannan ke yake damu, kiyi abunda na umarce ki kafin in Riga
goma." Cikin daga murya ya fad'i maganar.

Jin nayi shiru ne yasa ya damk'i gashin kaina hade da ja da mugun k'arfi !! Ihu! Na kurma ina
fad'in"Zan y......Fuzgar gashin Yayi da k'arfi yace." Oya! Ce ne *Amjadu* kayi hakuri sau goma
sha biyu nake so ki fada."
Rintse idona nayi ina cije bakina na fara fad'ar *Amjadu kayi hakuri bazan k'ara ba.!"* sai fa na
fad'i haka sau goma sha biyu kamar yanda ya umarce ni.

Babu sauk'i a muryarsa yace." Duk naga shirme da kika rafka naga irin rashin mutumcin da kika
tsula a gurin party ku , to ki sani ma Sam! Bakiyi wani kyau ba, kullum kina kiran kanki da Me aji
mace mai daraja to duk baki amsa wannan sunan ba, *Momyna* ita za'a kira da wannan
sunan." Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Momyna ita yafi dacewar na aura a tsakanin Ku, to
kuma sai d'azu wanki Aminu yake rokona kan in hada in aure Ku gaba d'aya, cewar kin tayar da
hankalin ki, ke ni kadai kike so, hake ko ba haka bane."? Kallonsa nayi cike da mamaki anya Ya
Aminu zai fada masa haka.? Wata zuciyar tace" Tsaf Ya Aminu zai iya fada masa haka saboda
daman ba shiri kuke dashi ba."

A d'age na kalleshi ina ya mutse fuskata nace"Sai dai Mimi don da ita kuka fi dacewa amma ni
ko maza sun k'are bana jin zan aure ka gwara in k'are rayuwata a haka."

Miskilin murmushi yayi bai ce komai ba ya sake ni, hijabina na dauka ina kokarin sanyawa naga
ya tada motar nace"Ina zaka kaini."? Ko kallo ban ishe shi ba, ya figi motar da gudu.!

Da sauri na sanya hannu guda na rike sitiyarin motar murya ta na rawa nace"Ka mayar dani
gida don girman Allah." Ko kallona bai yi ba, ya cigaba da fafura gudu, kuka sosai na sanya
tsoro ya shige ni ganin fuskarsa murtuk!! Nace"Wai me nayi maka ne kake kokarin wulakantani
? Ita Mimi meya sa baka yi mata abunda kake min. " Shiru babu Amsa, yanzu tsoron gida nake
da tsoron dukan da Yaya Aminu zai yi min.

Hannunsa na rike tamau! Ina rokanshi motar ta fara gargada! A fusace! Ya fuzge hannuna had'e
da yarfa min mari." Cike da mamaki na dafe kuncina ina kallonsa... Da Jan ido ya kalle ni tare
da fad'in"Ki shiga hankalin ki."
Shiru nayi tsoro yana shigata.
Gudu yake sosai kan kwalta, naga mun wuce Jambulo wajan gidan shi ya mik'e titin BUK
bakina na rawa nace"Kayi hakuri." Hankalinsa na kan driving ki kallona bai yi ba.

Rimin Gata muka shiga sosai, yayi parking dai-dai wani k'aton gidan mai
Haske ko ina jama'a na ta shiga da motocin su Suna shan mai.

Da sauri naga wani mai aikacin ya nufo mu jikinsa sanye da Uniporm orange da tambarin
sunan mai gidan mai yana k'araso wa na ga jikinsa rigarsa an sanya *A&A Amjadu Mai nasara
feturolium* nace Ashe har gidan mai ne dashi, cikin turanci naji suna maganar Sam ban
fuskanci komai ba na dai ga mutumin ya juya ya tafi da sauri!

Minti biyar sai ga mutumin shida wani, sai da suka k'araso sannan naso na gane wanene. Gaba
na ne ya fad'i ganin Abokin Shamsu wato Abba gana, yayi tsuru-tsuru,
Bude kofar motar Yayi hade da umar tarsa ya shiga
Abba gana ya shiga motar ba tare da gaddama ba. Shi kuma ma'aikacin ya koma gurin akinshi

Juyo wa yayi yana kallonsa, muryarsa babu wasa yace." Malam meye sunan ka? Kuma meye
ya kawo ka wannan jahar."?

Abba yace." Sunana Abba Gana ni mutumin mai duguri ne, yau sati na biyu a jahar kano, Nazo
Neman kudi."

Gyada kansa yayi murya a cunkushe yace." Kasan wannan yarinyar."?
Naji gabana ya buga damm!!!
Shiru Abbah yayi, tsawa ya buga masa tare da fadin" Answer me." Baki na rawa Abba yace."
Banga fuskarta ba Yallab'ai."
Cikin wata irin kyara da hantara yace." Ki juya masa fuskar ki ya kalle ki."!!!!
Da sauri na juya muka hada ido da Abbah Wanda tun ranar party mu bamu sake had'uwa dashi
ba.
Da sauri Abba yace." Na Santa sosai Yallab'ai. "
"Good."!
Yafad'a yana jin jina kansa. Bakina na rawa nace" A ina ka sanni da har kake cewa kayi min
farin San.....ban k'arasa ba, ya gwab'e min bakina da gwiwar hannusa. Dafe bakina nayi ina
kallonsa hawaye na zubo min.
Kallona yake shima fuskar sa babu sauk'i.
Minfi minti biyu a haka sannan ya juya da kaurarriyar murya yace." Abba kana son ta ko."?
Abba yace." K'warai kuwa Yallab'ai. "
Gyada kansa yayi yace."Zaka aure ta ni zan tsaya maka a kan komai zan baka gida akin yi da
duk abun bukata."
Abba ya dinga godiya tsakanin sa da Allah, yace." Kana iya tafiya"Abba ya fara kokarin bude
motar sai kuma ya daka ta tare da juyo wa Cikin sauri yace." Yallab'ai nagode k'warai da
wannan karamcin naka, hak'ika idan ana samun mutane irin Ku to da talakwa sunji dadin su,
amma ka yafe min hak'ika yanzu na kara tabbatar da cewar Asma'u matar manya CE, nagode
da karamcin ka, Asma'u da kai ta dace Yallab'ai. "
Wani kallo Amjadu ya watsa masa yace." Bayan kun gama wasan soyayyar da ita zaka ce dani
ta dace. Tab'e bakinsa yayi yana girgiza kansa yace." Ni nafi k'arfin socond hand, kawai idan
baka so in bawa wani."
Abbah yayi shiru yana tunani daga bisani yace." To Yallab'ai duk yanda kayi dai-dai ne."
'Yar dariya yayi yace." Yanzu kayi magana guy kaje kawai ka fara shiri."
Simi-simi Abbah ya bar gurin yana mamakin meye manufar sa kan haka, yarinyar da yayi-yayi
ta bashi numbar waya tak'i yau ita za a bashi, shi ba Yaro bane yana kallon tsantsar so hade da
kishi a idon sa, addu'a yake Allah yasa kar ya auna shi garinsu dama jarabar fad'an da ake ne
yasa ya biyo Shamsu tunda dukanin su iyayen su sun mutu. Kunna motar yayi muka fara tafiya. Da gefan ido ya kalleni tare da fad'in"Ko kiyi min shiru ko

kuma in sauke ki anan."
Cikin kuka nace"Allah kad'ai na mik'a masa kuka na akan ka, ka zame min bala'i ka shiga
rayuwa ta, me na tsare maka a duniyar nan, da kake kokarin tozar ta ni." Cikin zafin zuciya
yace." Kika tozarta kanki dai! Ni gata nake so nayi miki saboda na lura da yanda bagalar ki take,
kar ki dauko abun kunya domin baki da juriya, nace zan rufa miki asiri in aure ki kin ce bakya
so, tom naje gurin sauranyin naki da Kuka gama rungume-rumgume dashi zan taimake Ku,
shine kike min kuka harda hada ni da Allah, me kike so ayi miki."?
Murya ta a shak'e nace"Idan na dauko abun kunya meye damuwar ka? Na farko dai dani da kai
bamu had'a dangartakar komai ba, babu wata alak'a a tsakanimu,saboda haka baka da
damuwa da wannan....ka tse ni yayi ta hanyar fadin"Sai kace ba musulumi ba, wato kina so
Allah ya kama ni kenan ? Idan kika je kika dauko zunubi dole ya shafe ni tunda Allah ya nuna
min ko wacece ke, kuma kina maganar dan gantaka a tsakanimu idan yanzu babu ita tom nan
da kwanaki kad'an zata samu, bana so duniya ta dinga kallon ki a matsayin k'anwar matata
wacce ta dauko abun kunya......Ihu!!!! Na kurma da k'arfin gaske ina zuciya ta kamar zata tsage,
dukan shi na kama yi kamar wata sabuwar mahaukaciya ina Kuka ina fadin "Allah ya Isa na."!!!!
Motar ya tsayar da sauri ganin tana kokarin sauka daga kan titi.
Bakina ya matse da k'arfi!!! Muka fara kallon kallo dashi, babu alamun sassauci a fuskarsa
yace." Duk abunda na fada gaskiya ne, ga zahiri ne nan na gani, saboda na saba tab'a jikin ki in
muka had'u shine kika sanyo k'aramar riga don in gani inyi sha'awa, tab'e bakinsa yayi ya
cigaba da cewa"Ko tsirara zakiyi a yanzu bazan sha'awar komai naki ba, saboda kin gama
rabawa gayu a titi yanzu sunan ki sorry."!! Ya k'arashe maganar sa hade da Sakar min bakina
da ya matse yana shegen murmushin sa da ya saba.

Fad'ar tsananin b'acin ran da nake ciki a lokacin b'ata wa ne,raina yayi min bak'ik'ikirin ta inda
naji duk a fadin duniyar nan bani da babban makiyi sama da guy nan, tunda nake a rayuta ba a
tab'ai min tozarcin irin na yau ba, lallai na yarda ko wane namiji akwai sharrin shi don shi
wannan guy ma na rasa a ina zan aje shi, duk inda kake zaton sa ya wuce nan........








*6/November/2019*
[11/7, 11:04 AM] BintuUmarAbbale: [11/6, 10:37 PM] .: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*



*43*





Wani irin gudu yake da motar kan kwalta, tsoro duk ya kama ni burina kawai in ganni a gida, tun
lokacin da yace nayi shiru na rufe bakina domin ina jin tsoron kar ya tsoro da wata futunar.
Dai-dai tal'udu yayi parking din motar hade da futa kallonsa nayi ina cikin motar naga ya dauko
glass cikin aljihunsa ya sanya a fuskar sa, tsallaka titi yayi ya nufi had'addan gurin abincin nan
wato *Mai takobi* ina nan zaune mintuna goma na hango shi,
Saurin kauda kaina nayi cikin zuciya nake fadin"Mutum har mutum amma babu kyawun hali
Hannunsa rike da ledoji ya shigo motar kujerar baya ya aje ya kunna motar muka tafi
Bacci ne ya fara daukata kamar daga sama naji muryar shi yana fadin
"Kar ki sake kiyi min bacci a mota"
Zumbur na bude idona
Da suka fara yin ja.Kauda kansa yayi yana ya mutse fuska.
Nima ban sake kallonshi ba,
Har yanzu fuskata a hade take tamau! Nayi alk'awarin har in sauka daga motar bazan kara kula
shi ba duk abunda yayi min na barshi da Allah.
Wayar shi ce tayi kara a lamun ana kira, a hankali ya sanya hannunsa ya dauki wayar da take
kusa dani.
Ji nayi tsigar jikina ta mike jin hannunshi na tab'a gefan cinya ta.
Addu'a ns fara yi a zuciyata ta neman rinjaye.
Cikin wani irin voice naji yana fadin"Hibbah!! Wai sau nawa zan fad'a miki ki rabu dani ."! Ban ji
abunda tace ba, sai naji ya ja tsaki yana fad'in"Ki jik'a ki sha kayan ki, kwanan nan zanyi aure
in huta da bala'in Ku, ko wace 'yar iska ita dai a cita."
Kallonsa nayi a fakaice ina mamakinsa cikin zuciyata nace"Zaka aikata abunda yafi haka.
Ina jin budurwar tashi tana kaskantar da kanta hade da yi masa magiya, takaici ya she ni, cikin
zuciyata nake fadin"Mata yanzu sun koma bin maza har da magiya akan ya so ta wallahi
abunda bazan taba iya wa ba kenan.
Tsaki ya ja ya kashe mata waya
Draving dinshi ya cigaba da hannu daya daya hannun kuma da wayar a hannunsa yana
dubawa.
K'arfe goma shaura na dare,

Aje wayar yayi gefe na, saurin matsawa nayi jin hannunshi ya tab'a ni
Haka muka isa unguwar mu, masu sana'oin dake kan layinmu duk sun fara tashi unguwar tsitt!!
Gashi duhu dumd'um muna Matsalar wutar NEPA.
Parking yayi hade da juyo wa yana kallona.
Dauke kaina nayi da sauri!
Yace."Kina iya tafiya." Hannu nasa ina kokarin bude kofar
Taki bud'ewa, hannunshi ya d'ora kan nawa cikin wani irin salo ya shafa sannan ya bude min
kofar
Jikina a sanyaye na futa daga motar ina wurga ido domin akwai ni da bala'in tsoro ga unguwar
mu da karnukan tsiya gari yayi tsitt ga duhu. Leda guda ya mik'o min cikin ledojin nan
yace."_Karb'i ki kaiwa my Wifi bayan haka kice ta kunna wayar ta ina son muyi hira."
Share shi nayi ina kokarin tsallaka titi.
Sunana naji ya ambata *Asma'u* kin ji yuwa nayi na wuce da sauri!
Wani kare ne yayo kaina da gudu, yana haushi.
Ihu!! Na sanya na dawo da baya ina haki!
Dariya yayi ya bude motar ya futo
Karan ya kara haushi da k'arfi!
A hankali yace." Wannan bakin hijab din na jikin ki shiyasa yake miki haushi.
Cikin tsoro na kalle shi, nasan bala'in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login