Showing 48001 words to 51000 words out of 95753 words

Chapter 17 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

naji k'amshin ki,
humm! Ina fatan zan same ki, a yanda nake tsammani, sai kunzo."! Kashe wayar yayi ba tare
da ya bari tace komai ba, ya maida ita aljihunsa, ya cigaba da sabgar shi da jama'a.
Saroro nayi da waya a hannuna gwiwa tayi sanyi sai naji duk wani karsashi da kuzari na, yayi
kasa, tunanin guy nake, dama can yana son Mimi Ashe yake pretending ko kuma yanzu ya fara
sonta, ni dai tunda nake dashi ban tab'a jinshi da irin wannan muryar ba, gashi yana fad'a mata
kalamai na so, zuciyata ta shiga zullumi da wasi-wasi, gashi tayi min wani nauyi ina jin bakin
ciki a cikinta da kyar na dai-dai ta kaina na shiga cikin jama'a muka cigaba da hoto amma lokaci
lokaci sai inji fad'uwar gaba idan na tuno guy din.



Motoci uku ya turo masu zafi dama ba mu fi mu bakwai ba, muka shiga sai Jan bolo gurin
parking motocin suka k'arasa da mu sannan ko wacce ta futo, haske ko ina da ina kamar rana
ga wasu manya manyan motoci a fake a gurin, k'amshin turare kuwa na wannan yana wane
wancan, can hango shi ya tawo abokanshi biyu a bayan shi, gabana ya dinga bugawa tun kafin
su k'araso nake kokarin nemo jarumta ta tana guduwa yayi min masifar kyau! Farin mutum cikin
bak'aken kaya, sai ya zama kamar wani tauraro cikin abokan nasa abun mamaki tunda ga nesa
nake hango wani kwantaccan murmushi k'ayattace a fuskar sa, Suna karasowa gurin ya rike
hannun Mimi tuni abokan shi da masu d'aukar hoto suka fara aikin su, suka fara tafiya mukuma
muka rufa musu baya, na lura bani kadai ce na shiga halin d'imuwa ba har da k'awayemu suma
duk jikinsu yayi sanyi ganinshi narasa me yasa yake wa mutane kwarjini haka,mussaman mata.
Addu'ar Neman
nake cikin zuciyata, *"Wallahu galibun ala'amri."* wannan addu'ar nake yi cikin zuciyata domin
ina ganin zuciyata zata iya tona mun asiri, a gurin, shiyasa na dauki alk'awarin bazan k'ara
kallon inda yake ba, suna. Tafiya ana musu vedio da hotona har suka Isa gurin zaman su,
muma muka samu guri muka zauna, sannan guri yayi shiru mai gabatar wa ya tashi ya gabatar
da malamin da zai fad'a kar kam zaman aure da abunda auran ya kunsa
Wa'azi yayi kyau kuma ya fad'ar kar sosai bayan ya gama. Masu rabo suka shigo suka fara
raba wasu manya-manyan ledoji komai cikin nutsuwa akeyin shi, ko da wasa naki kallon inda
suke zaune, hira ma muke yi da Maryam tana k'ara fada min Yanda Mimi tayi dace da miji tana
fadin"Dole sai tayi da gaske domin akwai 'yan matan shi da suka d'aura arinyar akanta
mussaman Alina." Nace"Dole kuwa Alina kinga ko zuwa bata yi ba." Maryam tace"Yaushe zata
zo matar da tunda taji abun take tada Aljanu." Dariya nasa Ina rufe fuskata da hannuna kawai
sai naga hasken flash dago kaina nayi da sauri, naga d'aya daga cikin abokan shi Wanda suka
sanya kaya iri daya yana tsaye a kanmu nida Maryam sai daukarmu a hoto yake mussaman ni.
Bata fuska nayi ina kallon shi, murmushi ya sakar min, tare da kashe min ido daya. Dauke kaina

nayi ina Jan tsaki k'asa-k'asa. Gurin ya bari yana duba wayar shi, hotona yake dubawa

Duk abunda yake faruwa tsakanin Mujahid da Asma'u a kan idonshi, yasan halin Mujahid akwai
son matan tsiya gashi dai da auran shi, amma in yaga mata jikinsa har tsuma yake, yaji wani iri
a zuciyarsa amma kallon da yaga Asma'u na watsa ma Mujahid din ya ji dad'i a zuciyarsa yace."
Mata masu daraja kenan."

Mik'ewa nayi daga gurin ina waige-waige Su Munnu na can baya an had'u da samari ana hira
da ciye-ciye ganin na mike yasa Maryam mik'ewa muka fara ratsa jama'a tafiya zamu yi tunda
dai an gama ango ya kawo amaryar sa gida domin na tsani kallon da maza suke min. Aikuwa
ido yayi caaaaa! A kanmu ni kaina a jikina nasan kallona ake yi, cikin sauri sauri nake tafiya
inda sassaan jikina yake motsawa, sai tsaki nake.

Amjadu kuwa tun lokacin da ta mike tsaye ya karewa jikinta kallo kuma yaga yanda shatin
jikinta ya futo ta cikin sharara din mayafin ta, sai yaji kamar ana soka masa kibiya a kahon
zuciyarsa, mussaman. Yanda yaga maza da dama sun raja'a a kanta, gumi ya tsinke masa, lips
d'insa ya tura a baki yana ji kamar ya hadiyi zuciyarsa ya huta da wannan bakin ci, Mimi ya
kalla a sace ya ga Sam ita babu wani abun assha da dinkin ya futo mata dashi, ya rasa wace iri
ce Asma'u me karuwan jiki, ko wane irin kaya tasa sai sun tona mata asirin jiki. Innalillahi
wa'inna'ilah raji'un. " shine abunda yake nanatawa cikin zuciyarsa ko ya samu sassauci.

Ganin duk sun mike ne suna kokarin futa daga gate sai hakan yayi masa dad'i mutuka wayar
sa ya dauka yana kiran Rambo yace." Maza'a maida su gida shi da kansa zai kawo Mimi gida
aikuwa haka aka yi, muna kokarin shiga mota ne sai ga Muhajid ya k'araso gurin, hade da kure
ni da ido yana sakin wani murmushi, yace." Asma'u." Nayi mamakin yanda ya San sunana
haka, babu yabo babu fallasa nace." Na'am ya kake."?
Murmushi yayi Wanda na lura hakan d'abiar shi yace." Lafiya amma ba Lou ba, tunda na ganki
na rikice na gigice na dimauce na rasa nutsuwa ta, Asma'u ina kaunar ki fisabillah." Ya k'arashe
maganar sa har da kwantar da kansa, Su Munnu kuwa dariya suke masa, yace." Ina da mata
da yara biyu ni ma'aikacin lafiya ne, ina aiki a nasarawa hospital ina fata zaki so ni kar kice na
miki tsufa." Yanayin barkwancin sa da yanda yake da sakin fuska da wasa da dariya yasa na
saki fuskata nace"Ashe dai ka sani ni kam kayi min tsufa bazan auri me mata ba." Marairaice
fuska yayi hade da fadin "Don Allah kinji. " sai na tsinci kaina da sakin dariya har fararen hak'ura
na suka bayyana Wanda yayi dai-dai da zuwan Amjadu gurin Hannunshi rike da na Mimi, ina
ganinshi na dauke kaina da sauri gaba na lugude, ko kallonmu bai yi ba nida Mujahid ya fara
magana dasu Rambo Wanda suke kokarin saka mutane a mota, Ina jin Mujahid nace "Aboki
nifa nayi mata a gurin nan gaskiya naji dadin wannan ranar wallahi na tsinci dami a kala."
Babu yabo babu fallasa ya kallemu dani dashi yayi wani killer smile As'usuel ya sosa kanshi
tare da fadin"Kayi dace Aboki amma bakayi gaggawa ba, kuwa." Mujahid yasa dariya tare da
fadin" Wane irin gaggawa kuma in tsaya kallon ruwa kwad'o yayi min k'afa."
Kamar babu abunda yaje damunsa ya sanya dariya tare da fad'in"OK ni babu ruwana wallahi
kai da Madam."! Mujahid din yace." Shareta ai ba da ita kadai zan zauna ba." Shiru yayi masa

ya cigaba da magana da Rambo, ko da wasa ban kalli shi ba sai ma sauri da nayi na bude
motar na shiga.

Ina kallonshi ya rungume kafad'un Mimi a jikinshi lokaci-lokaci yana sumbatar goshin ta, hade
da yi mata magana k'asa-k'asa, da sauri na kauda kaina dama tsautsayi ne yasa na kalleshi,
Yanzu kuwa Allah Allah nake motar ta tashi mubar gurin.








*16/November/2019*
[11/17, 1:56 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*


*MALLAKAR_ BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*




*54*




Sai ya tabbatar da motocin su sun tashi sannan yaja hannun Mimi suka bar gurin, cikin sauran
abokan sa ya koma masu hoto suka dinga d'aukar shi da Mimi sai sunkuyar da kanta take cike
da kunya shi kuwa rumgumeta yake jikinsa fuskar sa a sake, 'yan jaradi ma ba a bar su a baya
na sai da suka zo ganin k'waf tare da d'aukar amarya da ango hoto da vedio walima tayi kyau
sosai kuma ta k'ayatu, k'arfe 11:30 gurin yayi sauki jama'a duk sun a watse a gajiye yake sosai
amma babu yadda ya iya dole ya maida Mimi gida. Hannunsa rike da nata babu um bare umum
suka shiga mota tare Doh! Yazo da sauri, sai ya daga masa hannu alamun a'a baya ya matsa,

yana d'aga masa hannu yaja motar suka futa daga Estate din.. Sai da ya hau kan kwalta
sannan ya kalleta a fakaice yace." Momy kin gaji wannan idon naki akwai bacci a cikinsa."?
Mimi tayi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace." Wallahi na gaji sosai hankalina yayi
gida." Cike da tsokana yace." Da har ina cewa kinzo kenan baza ki koma gida ba." Kauda kanta
tayi cike da kunya, hira sama-sama suke yi da ita kamar wasu surukai har suka Isa badawa
yayi parking a inda ya saba, kallonta yayi da lumsassun idonsa saurin dauke kanta tayi, ya saki
murmushi tare da fadin "Kije ki huta kinji ko gobe ina jiran ki, kiyi min tanadi me kyau." Kofar
motar ya bude mata hade da sumbatar hannunta guda, Mimi ta futa a hankali tana d'aga masa
hannu, motar yaja ya bar gurin, dake da wutar NEPA a unguwar yasa matasa basu watse ba.
Mimi ta tsallaka ta shiga lokonsu cikin sauri

Hira muke da su Munnu amma hankalina da tunani na nakan Mimi gamin har k'arfe goma sha
biyu saura bata shigo gidan nan ba, Umma ma ta leko dakin kusan sau uku tana tambayar ta
shigo, aunt Hauwa ce ta kwantar da hankalin ta, tunda dai tana gurin mijinta,Ni da Munnu hirar
muke Mimi ta shigo da sallama, duk muka bita da kallo, 'yar dariya tayi tare da fadin'Meye daga
shigowa ta zaku zuba min ido."? Tsaki naja ina d'an hararata nace." Mimi dubi lokaci fa ke ko
tsoro bakya ji, bakya ce masa dare yayi." Maryam dake danne-danne a waya tace "Wane irin
tsoro tana tare da mijinta." Munnu tace "Nima dai abunda na gani kenan." Tab'e bakina nayi
kawai ina kallonta ta tsallako har inda nake zaune k'amshin turaran sa ya buge ni, domin duk
jikin Mimi k'amshin masifaffan turaran sa take, d'an rungume ta da yayi, sai naji zuciya babu
dad'i wani irin kallo nake mata cike da zargi ina tunanin ko wani Abu ya shiga tsakanin ta dashi,
tunda nasan halinsa ba hakuri ne dashi ba, mik'ewa nayi na futa daga dakin domin ji nayi wani
irin fleelings na taso min jin k'amshin turaran sa sai na dunga tuno da salon soyayyar shi, Uwar
dakin Umma na shifa duk mutane kwance a rumfa na tsallake su, kwanciya nayi kan gadon ta,
gefan aunt Hauwa wacce take bacci sosai nasan gajiya ce." Lumshe idona nayi ina addu'ar kar
Allah ya dora min tashin sha'awa ta a wannan daran nasan zan shiga mugun hali ga jama'a a
gidan.


****
Shima bashi bangaran damuwa da tsanani gajiya su suka dame shi, don haka yana shiga part
dinshi yayi wanka ya futo parlor ya kwanta kan doguwar kujera lokaci guda bacci ya dauke shi,
mai cike da mafarkai bar katai.


****
Washe gari da kuncin zuciya na tashi har 'yan buki suka so su gane ganin naki walwala kamar
jiya yasa suka dame ni da tambaya dole na sake na cigaba da wurda da mutane kamar yanda
na saba.


K'arfe bakwai dai-dai motoci sun fi ashirin kofar gidanmu da bakin layinmu duk na d'aukar
amarya ne da 'yan uwanta kowa sai da ya samu guri wasu ma basuyi niyyar zuwa ba,

mussaman makotanmu amma saboda su kashe kwarkwatar idonsu yasa suka dinga futowa
daga gidan jansu su da gayyar 'yayansu suna fadin"Hali Yayi yau Dole suje suga gidan *Young
millionaire* Estate din sai da ya kusa cika da mutane sai hauka suke da ihu hade da k'auyanci
aikuwa karnuka na rufe a gurinsu suka dinga haushi sosai, saboda ganin sabon Abu.


Kowa fadin albarka cin bakinsa yake game da kyau da tsaruwar gidansa ni da Munnu da ita
kanta Mimi gidan ba bakonmu bane, saboda haka bamu damu ba, amma dai naga sauye-sauye
a parlor ba kamar zuwana na baya ba.

Mimi kuka take sosai da sosai ta rirrike Aunt Hauwa wacce take kuka a fakaice,ji nayi idanuna
na kokarin kawo ruwa da sauri na fuce daga dakin, Umma kuwa dama kin zuwa tayi domin ba
k'aramin artabu aka sha da ita da Mimi ba, tana kuka Mimi na kuka aka futo da ita.

Da kyar mutane suka futa daga gidan ko wacce tana jin ina ma itace a cikin gidan Mimi
mussaman 'yan matan gurin. Munnu da Mimi kuka suke sosai, naja tsaki tare da fadin"Dallah
Munnu ki tashi mu tafi ki rabu da ita." Mimi ta dago kanta tana kallona cikin hawaye take fadin
"Haka zaka ce, ko ? Shine kika munafurce ni wato kin San bada ke aka d'aura auranan ba,
kukayi min shiru ni yanzu yaya za'ayi na iya rayuwa ba tare dake ba." Kuka take sosai,
nace"Haka Allah ya nufa kiyi hakuri mu zamu tafi." Tashi Tayi da gudu taje ta kulle kofar hade da
tsayawa jikin kofar tana kuka, ni da Munnu muka bita da kallon mamaki! Nace" zaki bata
kwalliyar taki tun kafin angon yazo." Cikin kuka tace"Asma'u baki yi min adalci ba, yanzu ke idan
aka ce ki tafi ki barni a gidan nan sai ki tafi ki barni." Dariya ta bani sosai nace"Mimi mata nawa
akai wa aure suka zauna su kadai kema kiyu hakuri dama mace 'yar haka CE." Tace"Ni dai na
fada miki babu inda zaku je Wallahi."

Tun muna d'aukar abun da wasa har mu ka dawo rarrashin Mimi amma kememe ta ki bude
mana kofa, agogon dake manne a dakin na kalla k'arfe goma da kwata nace" Mimi dubi lokaci
don girman Allah ki bude Mana kofa." Ki tayi, Munnu ta kwanta kan gado tare da fadin""Ki
k'yaleta dole idan angon yazo komai abunta mu tafi, gwara mu d'ana gadon amarya." Bude
bakina nayi zanyi magana naji muryar shi k'asa kasa yana kiran Mimi da "Momyna" yana
kokarin bude kofar. Da sauri na janye ta daga jikin kofar na zaunar da ita kan bed din hade da
rufe mata jikinta.

Jan kofar yake yana kiran sunanta a hankali na gyara fuskata sosai naje na bude hade da
juyawa. Idonshi yayi masa tozali da bayan Asma'u tana tafiya, take yaji yana nema ya fadin
saboda abunda ya tsone masa ido, saurin kauda kansa yayi ya shiga dakin sosai hade da rufe
kofar, babu yabo babu fallasa ya kalleni tare da fadin"Me ya hana Ku tafiya."? Idona tsaye
kanshi yana sanye da jallabiya me ruwan tuka, fuskar shi fayau da ita, nace"Mimi ce ta hana mu
tafiya amma tunda kazo zamu tafi yanzu.." Na fada ina kokarin futa, Munnu ta mike ta itama
tana YAFE mayafin ta

Da wani mugun gudu Mimi tayo kaina hade da rungume ni muka kusa fad'uwa ni da ita kuka
take sosai tana fadin"Wallahi babu inda zaki je."

Cike da mamaki nake kallonta kuka take haik'an sai naji tausayin ta ya kama ni da gaske murya
ta ta karye tana rawa nace"Wai meye haka Mimi wannan abunda kike ba dai-dai bane gaskiya
ni sake ni don Allah."! Kin sakina tayi ta cukyukuye min mayafi har d'ankwalin kaina na cire wa
yalwatacciyar suman kaina ta bayyana, banyi ki tso ba, tunda aka wanke min kai sai na
tattarashi guri guda na Daure da k'aton ribbom. Takaicin ta ya kamani, kokarin nake in janyo
mayafina in rufe kaina dashi ganin yanda Yayi tsaye a kanmu hade da kura mana ido, kafin in
Ankara mayafin ya fad'i kasa saboda yanda take rikeni rai a bace nace ja Tsaki tare da fadin"Ki
sake dallah."!!! Ki Tayi har ilahi yau tana kuka.

A hankali ya karasa kusa dasu, ya sanya hannunsa yana kokarin janye Mimi tana kara rungume
ni kamar cingum, nima nawa b'angaran kokari nake in kwace kaina mussaman yanda nake jin
hucin nuffashin sa kusa dani hade da k'amshin sa, yayi yayi ya janye Mimi taki Munnu dai na
tsaye tana kallon ikon Allah. Da ya kasa janye Mimi sai ya dawo kaina babu kunya ya rike kafad'una wai zai janye ni.
Hannunsa na tankwabe da sauri ina watsa masa mugun kallo
Ya kalleni na kalleshi, bai ce uffan ba, ya kara kai hannu a karo na biyu na goce da sauri,
gabana na fad'uwa.
Da sauri ya fuzgo ni daga jikin Mimi nayi taga-taga zan fad'i can na tsaya daga k'afafuna ina
haki! Mimi ya rungume a jikinsa yana Dan dukan bayan ta alamun rarrashi. Da sauri na tsuguna
kasan k'afafun su na dauki dankwalina da mayafina na mike INA d'aura d'ankwalin ina kokarin
bude kofa bana kallon gabana sosai gabana yake fad'uwa. Munnu ta biyo bayana da sauri muka futa.


Mimi kuwa tun lokacin da ya rungume ta ta nemi nutsuwar ta tarasa a hankali ya zaunar da ita
kan bed ya futa daga dakin tare da kulle kofar da key don kar ta futo.
Lokacin har mun futa harabar gidan Tsit!! Sai hasken fitilo ko ina INA, kai tsaye muka fara tafiya
a k'afa. Can naji hon din mota Munnu tace."Asma'u tsaya ina jin za'a kaimu gida ne ga motanan
za tawo. Bana cikin nutsuwa ta shiyasa banji abunda take cewa ba, sai gani nayi motar taja
burki a gabana, da sauri na tsaya, a gurin, ya bude motar tare da fadin "Shigo i n kai Ku gida
dare yayi Yanzu." Bani da zab'i dole sai hakan Munnu tayi saurin shiga na shiga na zauna kusa
da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login