Showing 78001 words to 81000 words out of 95753 words
Chapter 27 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
ta raine ta kamar yanda ta raini Mimi, Umma tace wannan kuma nice zanyi hidima
tunda nice mamanta a yanzu, nan na dauki a niyar fad'awa Mujahid kudirina kan Baby Aisha,
yarinyar da ta zama cikkakiyar mutum domin yanzu tayi k'wari sosai ta cika wataninta na
haihuwa, Jahid yace." Zai fad'awa mahaifin ta ko zai amunce, dama ya karb'i babyn sa, yau
kwana uku kenan, jin abunda Jahid din yace sai ya d'aga min hankali Ashe har sun bashi baby
babu labari mu gamu a zaune kullum muna kwadayin ganinta, to yanzu da ya karb'a wa ya
kaiwa? Ni kadai nake tambayar kaina, ina dawowa daga makaranta na fad'awa Umma halin da
ake ciki, tace "Aikuwa bai kyauta mana ba, muma ai muna da hakki a kanta, gashi kwana biyu
ya daina kiran Aminu a waya balle kusan halin da ake ciki." Nace"Umma to yanzu wa zai kaiwa
babyn ma." Umma tace "Kakarshi mana." Shiru na minti biyu nace "Umma kakarshi bata da
k'wari don Allah ki amunce a dauko ta." Umma tace"Ai dama bani naki amincewa mutukar zai
bamu muna so hakkin sa ne." Nace "Nayiwa Jahid magana zai nemi alfarma a gurin shi." """"
Rayuwa kenan duniya babu tabbas yau kwanan Mimi Hamsin da bakwai a karkashin kasa
komai yayi farko yana da k'arshe Amjad ya sake ya barwa Allah komai ya tabbatar dukanin
Abunda ya same shi daga Allah ne.
A halin yanzu ya maida hankalin sa ne gurin k'ara bunk'asa harkokinsa na waje, a cewar sa
mu'amula da turawa yanzu ya fara saboda wasun su sun fi muslumin mu amana da tausayi,
tunda gashi da Dan uwanshi musulmi aka hada baki dashi gurin cutar shi da izgilanci ga Allah
ga manzon sa, yana nan ya sanya matakan tsaro ko ta ina yayi lamfu bunkice yake sosai aka
mutanan da suka kulla masa sharri, maganar company kuma tunda sun rusa shi babu wasu
kudinsa da zai futo dasu ya saka tada wani, suje kawai Wanda bai ji bari ba zai ji hoho.. Loptop
ce a kan cinyar shi yana duba sakkonin da Anthony ya turo mishi tsawon lokuta dama wasu ya
bashi amsa wasu bai bashi ba, ya bari ne in yaje can sai suyi maganar. Granny CE ta futo daga
dakin ta ta zauna kusa dashi.. Hankalinsa na kan Loptop din bai dago ba yace." Ina Sweetheart
yau banji motsin ta ba." Granny tace"Tana gurun Iyami tun safe da tayi mata wanka take bacci."
Dariya yayi yace." Wannan Aishar ai rigamammiya ce tafi uwarta fitina." Granny tace"Mai suna
Aisha kuka ne da ita ai." Yace." Granny ina tunanin cikin satin nan Zan tafi Chana kuma zan kai
wata uku a can insha Allah, amma ina tunanin tafiya in barku fa."
Granny tace"Allah ya taimaka ni kam babu wata chana da zan biki to kaji."!! Dariya yayi yace."
Shikkenan zamu je da sweetheart d'ina OK." Hararshi tayi tace"Kaje ka bawa wa ita wannan
garin ai ku da ku ga zaku iya zuwa." Murmushi yayi kawai ya cigaba da duba lptop d'insa.
A hankali tace"Ni ko nace dama akwai wata magana da na yanke a kanka." Gyada kansa yayi
tare da fadin"Ina sauraren ki." Tace"Mai zai hana ka nemi auran Hafsatu. Da zan ce ko yarinyar
nan Asma'u to amma naga wannan yaron Dan albarka Mujahid yana nemanta ana barin halas
Dan kunya ko ba haka ba ne."? Bata fuska yayi had'e da ya mutse ta yace."granny ki k'yaleni in
huta tukkuna ni kam yanzu babu maganar aure a gurina sai an kwana biyu sannan. "
Tace"Aikuwa dole kayi aure domin shine cikar mutum ka kai munzali kace baza kayi aure ba,
baka Isa ba."
'Yar dariya yayi yace." Granny nayi aure har na samu riba mutuwa ta rabani da mata ta, ki k'yale
ni na huta tukkuna zanyi amma ba yanzu ba." Tace." Ni kam bazan ta kallon ka a haka ba dole
ni nayi maka aure. " dariya yake yana mamakin rigimar ta, yace." Ok kiyi min aure sai in barki
da matar wallahi inyi tafiya ta tunda bani na saki ba." Granny ta hau zuba masa masifa, dafe
kansa yayi yace." Ina aiki kin hani oh my god."!!! Iyami ce ta shigo da Baby Aisha a goye a
bayanta tana motsi, alamun ta tashi. Granny tace" Ta tashi ne."? Iyami tace"Gashinan fa da
alama Dadynta take so." Rufe loptp din yayi yana kokarin karb'a baby daga hannun granny sai
murmushi yake, yarinya tayi mulmul da ita tayi wata irin kib'a hasken fatarta ya kara futowa
Iyami ta iya raino gaskiya sai wani kamshi take yi, tana cikin kayansu na jira jira abun gwanin
sha'awa, leb'anshi ya manna a kumcinta yana sakin ajiyar zuciya yace." Momyna 'yar rigima
hummmm! Yau ba kuka kenan. "? Kamar yana da magana da babban mutum haka yake yin
magana da baby Aisha.
Granny tace"Aiki ya same ka kana magana kamar kana magana da babban mutum." Dariya
yayi hade da kamo bakin baby yana Dan tsotsa yarinyar ta fara mamular leb'an shi da sauri.
'Yar dariya yayi ya cire bakinsa ya kalli Iyami dake zaune kusa da granny yace." Allah Iyami
zanci tarar ki sweet heart dina yunwa take ji ga alamu nan na gani." Iyami tace"Afuwa Uban
gida dama yanzu nake so in dama mata madarar ta, kaga ai bacci take kuma sweeh Hart din
naka ci ne da ita Wallahi ." Dariya ya kyalkyale dashi jin yanda Iyami take fadi wai sweeh hart.
Yace." Ungo ta ki bata bana so tayi kuka yanzu dai kin San halinta." Iyami ta karb'e ta da sauri
ta futa...... Wayar shi tayi k'ara yana dubawa yaga Jahid ne, murmushi yayi hade da daga wayar
sallama yayi Jahid yace." Kana gida ne." ?
"Eh ina Gida yanzu amma k'arfe biyar dai-dai zanje government house." Jahid yace." OK
ganinan zuwa nima ina Gida kasan yau Sunday muna Hutu. " Amjad yace." OK sai ka shigo
din." Kashe wayar yayi ya cigaba da abunda yake yi.
Minti goma tsakani sai ga Jahid ya shigo parlor yana zama yace." Ina baby Aysha take." Amjad
ya rufe loptop tare da fad'in"Tana gurin me raino yanzu kuwa ta dauke ta suka bar gurinan
granny ma yanzu ta tashi." Jahid yayi Dariya tare da fadin "Babu wasa cikin al'amarin muna so
ka bamu baby Aysha fa."" ! Amjad yace." Ai gatanan ga kanan Aboki baby Aysha taku ce kai da
Madam." Jahid yace." Thank you my friend, wallahi Asma'u ce tun jiya ta dame ni lallai a basu
ita shine nace zanyi maka magana nasan dai baza ka hana ba." Tunda ya ambaci sunan
Asma'u ranshi ya b'aci don har sai da fuskarsa ta nuna ya kalli Jahid din babu alamun wasa a
tare dashi yace." Babu wannan maganar my friend babu Wanda zan iya bawa sweet heart
gaskiyar magana." Jahid yace." Kuma yanzu kace ka bani ita."
"Yes Ni nace na baka ita saboda nasan muna tare da Kai har abada, naji ka sanyo min zancan
wata Asma'u ne, am sorry my friend Asma'u bata da haleyan K'warai Wanda zata iya tarbiyan
tar da d'an wani. Bana jin Zan iya bari baby Aysha ta yini a gidansu ma balle har ta kaita ga
kwana gudun ta d'auko d'abiun yarinyar." Jahid ya sha kunnu mutuka yace." Kayi dai-dai
Asma'u kake ciwa fuska a gabana ko."? Dariya Amjadu ya sanya tare da fad'in"Sorry halin ta ne
fa, amma da baka yimin wannan maganar ba ni babu ruwana." Jahid ya bude hannunsa dake
kan kafad'un sa yace." Wato kana nufin matar da zan aura bata da tarbiya ko me."? Hannu
Amjad ya d'aga cikin sigar bada hakuri fuskarsa da murmushi yace." Ban fad'i haka ba my
friend.........................
*26/11/2019*
[11/26, 9:01 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*
*64*
Sosai Jahid yaji babu dad'i saboda yana k'aunar Asma'u tsakani da Allah kuma sam baya
kaunar yaji wani ya fad'i mummunar magana a kanta, kokarin mik'ewa yake Amjad din ya mai
dashi ya zaunar, gyara fuskar shi yayi babu alamun wasa yace." Karfa kayi magana ta wata
fahimta ta daban, ba wai na fad'i wannan maganar bane domin ranka ya b'aci ko kuma kaji wani
fargaba a game da k'udirin ka kan yarinyar kace zaka janye auran ta. No kawai na fad'i iya abun
da nasa ni a kanta, kuma kasan ko wane mutum Tara yake bai cika goma ba, amma hak'ika ka
cancanci yabo da godiya a gare ni abokina babu abunda zaka nema a gurina na kasa yi maka
shi, misali kace min in baka Baby Aysha zaka had'a ta da Salim ka rike min, wallahi babu
abunda zai hanani in baka saboda nasan Maman Salim macace da take da nutsuwa gami da
tarbiyya sai ince maka ma kusan halayen su d'aya da Mimi Allah ya jikanta, amma maganar In
bawa Asma'u baby ka aje ta gefe guda a halin yanzu babu ita." Jahid ya Dan ji sanyi a ransa,
amma duk da haka bai hak'ura ba saboda kwata kwata baya son b'acin ran Asma'u yace."
Yanzu idan Allah ya kaddara auramu da Asma'u zaka bamu ita ko ? Tunda kana ganinta a kusa
dakai sai kayi mata tarbiyar da kake so." Amjad yayi Dari hade da Sosa kansa yace." Mai zai
hana kuwa zan baku wannan nasan muna kusa kuma kai ma zaka samin ido sosai." Jahid yaja
tsaki tare da mik'ewa tsaye yace." Baza ka fasa ba kenan ? Ni kaga tafiya ta." Amjad ya mike
tsaye shima yana dariya ya rufa masa baya. To kafin suyi sallama ma sai da suka d'an jima a
tsaye sannan suka rabu, dama kuma tun Asali cikin makotan sa, sunfi shiri da Mujahid din
saboda saukin kansa.
****
K'arfe takwas dai-dai Mujahid ya kirani a waya cewar gashinan a waje yana jirana, a shirye
nake saboda nasan da zuwan sa, cikin motarsa na same shi, Duk sanda zai zo gurina da
sabbin kaya a zuciya nace Jahid ba dai gayu ba, budewa nayi na zauna sosai ya sakar min
murmushi tare da fad'in "Yau kin futo da Wuri." 'Yar dariya nayi nace"A shirye nake dama ya maganar mu da kai." Fad'uwar gaba yaji amma
dake namiji ne sai ya dake yace." Kya bari mu gaisa ko."?
Rife fuska ta nayi da tafin hannuna ina dariya, shima dariyar yake yace." Ke kinfi baby Aysha
rigima ma." Bude idona nayi har yanzu da murmushi a fuskata nace"Wallahi na damu na ga
babyn ne." Yace." Kina da gaskiya amma kin san me."? Girgiza kaina nayi, yace." Babanta ya
hana wallahi yace ki Bari tukkuna muyi aure zai bamu ita." Raina a bace nake kallon Jahid din
nace"Ban gane ya hana ba."? A hankali yace."Shima baya so tayi nisa dashi a yanda na
fahimta yana kallonta baby ne yaji sanyi a ransa duk lokacin da ya tuna matarsa.
Nace." Jahid abun da bangane ba shine, shi kad'ai ne yake da hakki da yarinyar? Mu da muke
a matsayin iyayen ta bamu da amfani kenan Jahid gani ba ci ba, dama baby 'yar shi waye yace
ba tashi ba."! A zafafe na k'arashe maganar.
Jahid ya gyad'a kansa ya San zai fuskanci haka daga gurin ta, yace." Matsala ta dake saurin
d'aukar zafi kiyi wa magana ta kyakyawar fahimta mana." Cikin takaici da jin haushin sa
nace"Na lura kamar bakin Ku d'aya Jahid baka San yanda nake ji ba Wallahi tallahi tunda naji
kuna fadin baby suna kama da Mimi naji ina mugun kaunar ta." Cikin rawar murya ta karasa
maganar, cike da tausayin ta yace." Kiyi hakuri dai yanzu dai kar kiyi min kuka Jahid UA fad'a
cikin rarrashi. Nace"Wallahi na saki jiki zangan ka da tare da ita." Cikin shagwaba take
maganar,Jahid yaji kamar zai suma a gurin hannunsa na rawa yace." Bari kiga hotonta hankalin
ki ya kwanta, nima dai kin kusa bani nawa babyn ko."?
Murmushi kawai nayi masa ina Allah-Allah ya mik'o min wayar in gani.. Da sauri na karb'a ina
dubawa sosai baby Aysha take kama da Mimi sai da tafi ta haske kamar yanda naji suna fad'a
ta murmure sosai da gani ma hoton tana jikin babanta aka dauka don ga jikin shi nan ya futo da
hannunshi guda da ya rike ta, Dole in gane saboda manya manyan azurfan dake bisa yatsun
sa.
Wayar na rungume a k'irjina ina sakin ajiyar zuciya nace"Jahid baby Aysha na kama da Mimi
wallahi ka bani wayar nan yau ta kwana a hannuna in kwana ina kallonta kaji. " dariya yayi
yace." Kece kin ki ki bude whatsp da sai na turo miki hoton." Da sauri na mik'a mishi wayar
nace "Bari in dauko wayar tawa ka tura min wsp din don Baby Aysha amma da na daina yi."
Dariya yake min har na futa daga motar. A tsakaice dai sai da Jahid ya bude min wsp dina da
na rufe tun bayan rasuwar Mimi ya tura min dukanin. Hotonan baby Aysha, yace" kullum zai
dinga d'aukar ta sabbin pictures Yana turo min sosai naji dadin haka na saki jikina sosai muka yi
shirarmu nan yace insha Allahu a karshen wata yake so ya turo magabatan sa gurin Kawu
Yunusa nace"Allah yasa nan mukayi sallama dashi ya tafi.
Ko da Umma taga hoton baby Aysha tayi ta mamaki sosai sai taji sha'awar ganin yarinyar a
zahiri tace." To tunda ya hamu ita ni zanje da kaina in duba ta ai hakan ba laifi bane." Umma da
kin kyaleshi dai komai abunda baby Dole ta nemi dangin uwarta wallahi." Umma tace"Ai
baza'ayi haka ba, domin bamu San munufar sa tayin haka ba, to koma dai menene abar shi da
d'iyar shi yayi yanda yake so da ita." Shiru nayi ina raya wani Abu a raina
Abunci naci nayi wa Umma sallama, kai tsaye dakinmu na nufa, na tube kayan jikina wata
duguwar Riga na sanya a jikina mai uban kyau da tsada duk cikin kayan Mimi suke, hula na
sanya a kaina na kwanta kan katifa, hade da rufe k'afafuna hotan baby na tsurawa ido ina
murmushi nima wallahi na damu inga yarinyar a zuciya ta.
Wsp na shiga na d'ora pic dinta kan df na, wsp din dake amfani a waya ta mai Gb ne ya nuna
min Amjad na online wata zuciyar tace kiyi masa magana kawai tunda gashi a onile da sauri na
shiga gurin shi naga ya sauka akai. Yanzu Df shi na kamo da sauri ina dubawa, pic dinshi ne da
baby Aysha ya d'aga ta sama yana dariya hat tada dimple dinshi sai da ya futo saboda dariya
itama babyn dariya take naji sun bani sha'awa, zuciya ta tace min "Shi yana Cikin jin dad'i har
da dariya gashi ga 'yar shi hummm! Ai in da mutumci Amjad bamu cancanci haka daga gurin shi
ba, message na tura masa kamar haka
_" Duk d'an halak baya bance alkairi kuma tilas! Ace da mijin iya baba, duk talaucin mu, baby
na tabbata sai ta neme mu, domin mune dai dangin uwarta."_
Tura masa nayi na kashe data ta, tsawon mintuna ashirin, na k'ara bud'e datar, ina dubawa
naga har ya gani, sai naji wata fad'uwar gaba, messenges na cigaba da dubawa ina sauraron
amsar sa, shiru kusan minti talatin kuma duk dubawar da zanyi sai inga yana online, bakin ciki
da takaici suka ishe ni, abunda na tsana a rayuwa ta shariya guy nan yaga sakona zai
wulakanta ni, lallai ya sanja sabbin halaye, ji nayi wasu zafafan hawaye na nema su kufce min.
Kira ne ya shigo wayar tawa ina dubawa naga shine.....
*26/11/2019*
[11/27, 4:45 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*
*65*
Cikin fad'uwar gaba na mik'e zaune sosai ina k'ara duba wayar tabbas shine ya kira ni. Cikin
zuciyata nace to me zai ce min lallai ma, kin d'agawa nayi har ra katse wani kiran ya k'ara
shigowa ina kallon wayar nan ma ta katse band'aga ba, sai da ya kira sau uku nak'i dagawa
sannan ya hak'ura, kwanciya nayi ina sak'e-sak'e a zuciya ta, data ta kara kunnawa aikuwa
sak'on shi na farko hannuna na rawa na shiga ina dubawa. Ga Abunda yace.
_"Maganar ki gaskiya ne 'yan mata, Sweetheart bata da wani dangi sai ku domin kune iyayen
ta, Abunda na kasa fahimta a maganar da kika ce duk D'an halal ba ya mance alkairi, shin wane
alkairi kuka yi min da har na manta? Bayan nan kuma ina so in k'ara jaddada miki cewar Aysha
d'iya tace domin nine k'ashin bayan Samar da ita, dukanin Ku baku da iko akanta, ni nake da
iko akan kaya ta, so bana son damuwa don Allah daga yau sai yau karki kara yi min magana
makamamciyar wannan, ina fatan kin fahimta? Kin turo min Jahid kan bukatar ki, to baki isa ba
indai nine uban Aysha bazan tab'a Bari ki raine ta ba ballanta ki koya mata munanan d'abi'un ki,
tabbas yanzu na tabbatar da cewa a baya nayi wauta da nake kokarin rabuwa da mace tagari a
kanki , na tabbata Mimi alkairi ce a rayuwa ta, kuma duk macan da zan aura sai dai tabi
bayanta wallahi,a halin