Showing 33001 words to 36000 words out of 95753 words

Chapter 12 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

tana fadin"Mimi ke ce kika dawo haka lokaci
guda." Ganin Umma na zubar da hawaye Mimi ma ta fashe da kuka kamar zararriya ta hau
dukan k'irjinta tana fadin"Umma k'irjina ciwo da nauyi na rasa wace irin masifa ce wannan?
Umma na rasa me yake damuna gwara in mutu in hutaa!!!!! Aunt Hauwa ta buga mata tsawa
Cikin jin haushin ta tace"Don Allah ki daina wannan kukan da kike yi kiyi tawakkali mana ita
rayuwar ai duk hakuri ake yi, kina kuka kina bugun k'irji dole hankali Umma ya tashi, ko me kike
ji a zuciyar ki sai ki dinga fadin "Innalillahi Allah zai miki magani."



Leb'anta na rawa tace"Aunt Hauwa baza ki gane ba ne, bana fata Allah ya dora wa wani
masoyina abunda nake ji a zuciya ta, gwara in mutu da wannan rayuwar."



Hankalina ya kai k'oluluwar tashi jin abunda Mimi take fad'a ban tsaya naji Abunda Ummansu
Munnu take cewa ba na futa daga d'akin. ba tare da sun ganni ba.


Diri-diri nake harabar a sibitin kamar wata sabuwar mahaukaciya nayi waje da sauri na, bakin
titi na tsya na tari a dai-dai ta sahu, na fad'a mishi idan zai kaini. Har kofar gidan Kawu Yunusa
ya aje ni, nace"Bari in shiga ciki in karb'o maka kudinka." Kallo kawai d'an a dai-dai ta ya bita
dashi.

Ina shiga soron gidan naci karo da Musa zai futa yaci kwalliya cikin shaddar sa, gaishe shi
nayi ya amsa yana was he min baki, tare da fadin "Husna kece a gidan nan da Safiya." ?
Nace"E h Musa ga mai s dai-dai ta can bashi kudinsa don Allah." Da sauri ya futa ni kuma na
shige gidan.



Muka gaisa da Baba Mariya a muntunce sai tsokana ta take da amarya amarya ni dai nayi
mata shiru, tace"Na ganki duk a furgice ." nace"Kawu yanan ko."? D'aga kanta tayi tare da fadin
yana sama tare da d'aya Kawun naki Idiris nasan maganar auran ki suke yi." Mik'ewa nayi ina
fadin"Yawwa dama gurinsu Nazo." Babu yabo babu fallasa nayi sallama dakin Kawun namu Wanda ya zame mana waliyi, daga ciki
naji muryar shi yana fad'in "Shigo ko waye." Na shiga cikin mamaki suka Bini da kallo shi da
Kawu Idiris na zauna muna gaisawa . Kawu Idiris yace." Daga ina kike da sassafe nan." ?
Nace"Daga asibiti. " Kawu Yunusa yace."Waye babu lafiya."? Kuka na fashe musu dashi
nace"Mimi ce ." Kawu Idiris yace."Mai ya same ta kiyi shiru kiyi mana bayani yanda zamu
gamsu."




Cikin kuka nace"Aman jini take sosai da kyar likitoci suka shawo kan Matsalar kuma sun ce
lallai a bata abunda take so idan ba haka ba zuciyar ta zata buga da ko wane lokaci."


Kawu Yunusa yace." To mu wannan ai bs hurumin mu bane zaki zo ki tayar mana da hankali
da sanyi safiyar nan." Kawu Yunusa yace." Nima abunda na gani kenan kije ki Sanar da kanin
mahaifin ta shine magana."



Kallonsu nake cike da mamaki dama halinsu ne rashin zumunci da rashin taimako Sam 'yan
uwan Babanmu basu da kara basu da kawaici kowa kansa ya sani da iyalinsa, mun sha wahala
sosai bayan mutuwar mahaifinmu shiyasa nake jinjinawa aunt Hauwa ta ko wane fanni domin ta
taka muhimmiyar rawa a gare mu, kafin Umma ta tsaya da k'afafunta.


Nace." Kawu Wallahi nayi rantsuwa da Allah mutukar baku sanya Ya Aminu ya janye
maganar auransa da Mimi ba to nima dole Ku warware nawa Ku mai da wa da Amjadu kudinsa,

na aure da kuka karb'a, Mimi ba son Aminu Amjadu take so saboda haka yace. Zai auremu ni
da ita Ya Aminu dole ya hak'ura tunda shi namiji ne idan yak'i hak'ura kuma to nima bazan aure
shi ba."





Jikinsu ne yayi sanyi jin abunda yarinyar take cewa, Suna murna arziki ya shigo musu gida ai
ba za su Bari wannan dama ta kubce musu ba shiyasa suka yi ruwa suka yi tsaki kan al'amari
idan banda rashin hankalin Asmau da kanta ta zo nema wa kanta kishiya. Babu ruwan su su dai
burinsu suga tabbatuwar auran ta da Amjadu ko banza zai kira su Waliyyanta Kuma zai dunga
tunawa dasu, duk abunda zai biyo baya babu ruwan su."




Kawu Yunusa yace." Wannan ce matsalar taki."? Gyada kaina nayi ina share hawaye na,
Yace." Kar ki damu zan samu Aminu in rarrashi shi tunda kinji kin gani shikkenan Allah ya sanya
alkairi." Ameen nace na mike hade da yi musu sallama.




Tana futa suka cigaba da maganar cike da mamaki sukan ba damuwar su bace hakan
burinsu tabbatuwar auran kawai.



Ko da na koma asubitin tashin hankali na tarar domin Ya Aminu ya dawo ya tadda Surutun
da Mimi take yi tamkar me motsuwar kwakwalwa take sambatu tare da fad'in sunan Amjadu ,
fad'uwa yayi a gurin hankalinsa a tashe, yana dafe k'irjinsa haki! Yake sosai, likitoci suka shigo
dakin suka dinga fada sosai suka yi kora waje, nan suka dauki Aminu da bai San a wace
duniyar yake ba, cikin tashin hankali suka yi wani daki dashi ganin yanda yake jawo numfahi da
kyar oxygen suka sanya masa.



Mimi jikin ya kara rike wa likitan ta kamar ya mammari su Umma haka yake ji ya dinga fada
sosai da sosai itama Oxygen din aka sanya mata Dr din yana addu'ar Allah yasa kar jinin ya
dawo mutukar jinin ya dawo da zubah to babu shakka sakamakon su ya nuna masa cewar
zuciyarta zata iya daina aiki.

*11/November/2019*
[11/12, 11:13 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*





*Mallakar_BINTA UMAR*





*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA*




*49*




Hankalin Umma ya kai k'oluluwar tashi inda ta dinga wata irin zufa!! Gabanta yana wata irin
fad'uwa su biyu kawai iyayen su suka Haifa ita da k'anwar ta, Aisha maihaifyar Mimi kenan
tabbas idan ta rasa Mimi bata da wani Abu da ya dangaci k'anwar ta, Mimi take kallo a matsayin
Aisha k'anwar ta, Aminu danta ne dole zata iya sarrafa shi ya hak'ura da Mimi a bata zabin
ranta, ko da kuwa Shi Aminu zai rasa tasa rayuwar wannan hukuncin ta yanke, ba tare da bata
lokaci ba ta sanya aunt Hauwa ta kira mata Kawu a waya yace gasu nan zuwa asibitin.

Sunzo sun tadda badakalar da take faruwa Umma tace Ita ta Riga ta gama yanke hukunci
Aminu ya janye auran sa a kan Mimi dole a aura mata Wanda take so.


Kawu Yunusa yace." Muma maganar da take tafe damu kenan domin Asma'u taje har gida ta
Sanar mana saboda haka tunda taga zata iya shikkenan dama kuma shi yaron Neman auran
mutum biyu yazo ita da Mimi saboda haka kan Aminu baza mu bari a rusa wannan auran ba
domin mu abun alfarin mu ne, hada jini da Amjadu saboda haka zamu tattashi Aminu."

Wannan shawarar ita ce matsaya Babansu Munnu na tsaye bai ce komai ba sai da suka gama
magana yace."Idan babu damuwa Aminu yazo ga Munnubiya na bashi sai a d'aura auran rana
daya.



Kawu Idiris yace." Mungode da wannan karamci zamu jira ya dawo hayyacinsa muji ta
bakinsa.



4:35 Aminu ya farka masha Allah nuffashin sa ya dawo dai-dai budar bakinsa "Ina Mimi take
kar kice min ta mutu Innalillahi wa'ina ilahi raji'un."
Ya fada yana yunk'urin tashi zaune


Dr Yayi saurin mai dashi ya kwantar yana rarrashin sa fafur Aminu yak'i zama dole sai an
kaishi gurin Mimi, Dr da kansa ya Dora shi keke saboda jikinsa babu k'wari kai tsaye dakin da
Mimi take ya nufa da shi.



Mimi na kwance sambal hancin ta sakale da oxygen idanunta a rufe Aminu ya tsura mata ido
zuciyarsa nayi masa zafi wai yanzu shi Mimi take gudu tafi son bare dashi, hak'ika Allah ya
jarrabe shi da kaunar ta tun tana 'yar jaririyar ta, Ashe zan Ga wannan ranar ta bakin ciki, wasu
zafafan hawaye ya share cikin zuciyar sa yace ."Ya zama Dole in hak'ura dake Mimi domin ko
ns aure ki zuciyar ki na can gurin wani bazan samu kulawar da nake so ba."


Wasa-wasa har k'arfe goma na dare Mimi bata farfado ba, likita ya duba ta sosai ya tabbatar
tana Raye kawai tayi dogon suma ne, nan ya rarrashin Aminu da ya tada hankalinsa a kan
hakan.

Da kyar Aminu ya futo daga d'akin sai yaji duk ya samu sauki ma domin halin da yaga Mimi a
ciki ya tsora tashi babu shakka zai iya SADAUKAR da soyayyarsa a kanta domin ta rayu.
Wannan shine sahihin so.da wannan tunanin ya futo.


Ya Tarar da tashin hankali a waje Inda Umma ta kasa nutsuwa ta tare wata narse tana share
hawaye tana rokonta wai ta fada mata idan Mimi ta mutu shikkenan sai su hak'ura saboda d'azu
da Dr ya futo Lokacin su Kawu Yunusa nan yake tambayar sa,lafiyar Aminu yace masa ya dawo
dai-dai Ita Mimin ce bata dawo normal ba shine hankalin ta ya tashi .


Aminu yazo ya rike ta zuciyarsa nayi masa rad'ad'i da zugi ga wani irin jiri yana d'ibar
muryarsa a shake yace." Kiyi hakuri Mimi lafiyar lau bata mutu ba, yanzu daga gurin ta nake."
Umma ta rike hannunsa tana kallonsa cike da tausayi ta bude baki zata yi magana ya katse ta
ta hanyar fadin "Umma na hak'ura da Mimi idan shine samun kwanciyar hankalinta na hak'ura
ta auri Wanda take so. Umma ta rungume shi tana share hawayen ta tace." Aminu Allah yayi
maka albarka Ubangiji Allah ya zab'a maka mafi alkairi a rayuwar ka, nagode da wannan
karmanci da kayi min yarona ka fidda ni daga zargin mutane."



Rungume ta yayi tare da tausar zuciyar ta, Ni da aunt Hauwa muka kama ta muka zaunar da
ita jikinta sai bari yake. A hankali Ya Aminu yace." Ni zan je gida in kwanta in huta jiri nake ji."
Aunt Hauwa tace." Idan kana ganin babu matsala shikkenan. " gyada kansa yayi kawai ya bar
gurin yanda yake tafiya zaka San ba shi da cikkakiyar Lafiya.

Tun lokacin da Ya Aminu ya fad'i cewar ya janye maganar auran sa da Mimi naji wani irin
sanyi a zuciyata tayi wasai duk wani bacin rai da fargabar da nake ciki naji babu shi. Umma ma
na lura ta sauya ta saki jikinta


Munanan zaune har sha biyu babu Wanda yake kokarin kwanciya ko gyangyadi muna
sauraren futaw Dr wata narse ce ta futo daga d'akin da Mimi take Fuskata babu yabo babu
fallasa tace." Wacece "Asma'u a cikin Ku."? Da sauri nace" Nice." Tace." Kizo maralafiyar nan
da kuka kawo na Neman ki. Hamdala Umma tayi tare da fadin"Ta farfado kenan." ? Narse tace
"Eh kusan awa biyu da farfadowar ta shine Yanzu tace." Wai a kira mata Asma'u." Umma tace."
Maza jeki kiji kome ye ko kara kwantar mata da hankali." Da sauri na bi bayan nurse din.

Mimi na zaune ta jingina da jikin gado kanta a kasa tana wasa da hannunta kamar wata
sokuwa ko kuma sabon shigar hauka duk ta sauya, cike da tausayin ta na zauna kusa da ita
tare da fadin"Mimi gani menene."?
D'ago kanta tayi hawaye na bin kuncin ta, ta rike hannunwa tamau!! Bakinta na rawa tace."
Habbity ya zanyi da rayuwa ta ne."!!!!? Ba kasaifai take kira na da wannan sunan ba, sai muna
cikin damuwa da ni da ita.



Hannunta na rike sosai nace." Mimi ba dai *Amjadu* ba."? Shiru tayi min hawaye na zuba a
idonta. Murmushi nayi me ciwo nace." Kamar kin aure shi kin gama an gama komai manya ma
sun shiga maganar Ya Aminu kuma ya janye maganar auran ki, Yace ki auri Wanda kike so." Na
k'arashe maganar fuskata dauke da murmushi na karfin hali.


Hannuna dake damk'e da nata ta matsaye sosai tana gyda kanta,bata CE min komai ba, minti
biyu tsakani nace." Kuma d'azu yazo duba ki lokacin kina bacci ya dad'e ma tare da dr duk
wasu hidima shine yayi, nima na amunce ya aure mu tare ki kwantar da hankalin ki."



Cikin nauyin baki tace"Nagode Habibty 'yar uwata ta kaina hak'ika kin cika 'yar halak Nagode
Asma'u na rasa wata irin zuciya ce dani narasa wace iri ce ni, ki yafe min zuciya ta tafi karfina
bazan iya sarrafa ta ba."



Murmushi nayi hade da rike hannunta nace "Ba laifin ki bane Mimi sharrin so ne kawai kowa
ma haka tana iya faruwa dashi, kuma kinsan kowa da irin zuciyarsa wani yana da dauriya wani
kuma bashi da ita, hakanan wani yana iya sarrafa zuciyar sa, wani kuma zuciyarsa tafi k'arfi sa,
kamar ke kenan, hummm!! Yanzu dai magana ta wuce insha Allahu baki da miji sai Amjadu
zakiyi rayuwa inuwa guda dashi."




Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tare da sakin wani irin murmushi Wanda dashi gwara kuka
tace." Asma'u na Dade da sanin cewar *Jad* baya sona nice nake haukana a kanshi, ke yake
so inda ke kuma baya gaban ki!! Ki bani shawarar Ya za'ayi na jawo hankalin sa kaina. "

Murmushi nayi ina mamakin Mimi da so ya rufewa ido ashe har suna ta sanya masa wai *Jad*
humm!! Sunan kuwa yayi min dad'i. Domin in kara kwantar mata da hankali nace" Mimi ke kike
abunki kar ki damu ni nasan da an d'aura aure zai so ki kamar ya mutu zai so ki fiye da yanda
Ya Aminu yake son ki, Mimi kina da kyau kina da kira mai d'aukar hankali gaki fara alkyabar
mata, babu namjin da zai kauda kansa daga kanki ki kwantar da hankalin ke dai."



Murmushi tayi hade da sunkuyar da kanta har yanzu hannuna guda na rike da nata.nace
"Kinga wayar ki ma a hannuna Bari in kira miki shi Ku gaisa ko."?

Bata ce min komai ba, na fara kiran numbar shi, bugu daya ya dauka muryar shi da alamun
bacci yace."
*HUSNAH."!* Sai da naji wani irin yarrrr! A jikina jin yanda ya ambaci sunana da ba kowa ne
yake kira na dashi ba, ga muryar tayi low sosai kamar me mura. Ajiyar zuciya na sauke babu
yabo babu fallasa nace"Ga Mimi za kuyi magana. "


Shiru naji yayi nace ."Hello." Gyaran muryar shi na ji yace." Owk bata wayar." Mimi na
mik'awa wayar da murmushi a fuskata, hannunta na rawa ta karb'i wayar tayi sallama da
dusashashiyar muryar ta.


Ina jinsa yana amsa mata a sake, yace." Ya jikin naki Momyna."? Tace." Jiki da sauki."
Yace." Alhmdullahi ki kwantar da hankalin ki kinji ko duk abunda kike tunanin bazai yi wu ba to
zai yi yuwu da izinin Allah idan Allah ya kaddara ke din matata ce Sai ki ga munyi aure, ki daina
tashin hankalin ki, Tare da yardar 'yar Uwar ki ni na amunce zan aure Ku a tare ina fatan alkairi
a kan haka, daga k'arshe nake ce wa dake ki godewa 'yar Uwar ki, domin tabbas ta sadaukar
da nata farin cikin a kanki da samun fi gaban ki hade da lafiyar ki. Momyna hak'ika kin sa'ar 'yar
uwa me kyawun zuciya."
Ya karasa maganar tasa cikin nutsuwa.



Ba Mimi ba ni kaina kalaman sa sun yi min dadi kuma naji dadin yabon da yayi min abunda
bai tab'a faruwa ba ni dashi, bai tab'a fad'ar alkairina ba sai yau.


Murmushi naga tana yi kunne na kasa sosai ko zan ji abunda yake fada mata Wanda yake
sata sakin wannan kayataccan murmushi, babu abunda nake ji daga b'angaran sa saboda ya
k'ara yin kasa da muryar sa sosai, ita kanta Mimi sai ta kasa kunne sosai sannan zata ji abunda
yake fad'a.

Ji nayi zuciyata nayi min wani irin zafi nayi saurin kauda kaina tare da ambatar innalillahi
cikin zuciyata domin ji nayi take wani kunci ya ziyarce ta, zuciyar tawa sai take raya min kamar
da akwai wani munafurci a ciki don me yasa zai dinga magana a waya kamar munafuki wannan
bayi bane ni a ganina. Maganar da Mimi tayi ce ta dawo dani hayyacina , wayar take mik'o min
tare da fadin"Yace." A baki wayar ku yi sallama."



D'aga murya nayi domin yaji nace"Mimi kashe wayar nan don Allah bacci nake ji, tunda dai
kun gaisa dashi shikkenan dama haka nake so in sanya zuciyar ki farin ciki, kashe wayar mu
kwanta Wallahi nayi bala'in gajiya."



Ga mamaki na sai naga Mimi ta kashe wayar kamar yanda na umarce ta ta aje wayar gefan
kamar ba ita ta saki fuska sosai tana yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login