Showing 93001 words to 95753 words out of 95753 words
Chapter 32 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
shi, kana ganinsa kasan yana
Cikin farin ciki, Liman yayi addu'a kamar yanda addini ya tanada Alhaji Isa mahifin Jahid ya
mik'a sadaki Asma'u dubu Dari cif kana Liman ya fatiha tare da shafawa duk Wanda ke kusa da
Liman a lokacin ya shaida Amjad da Asma'u Aka d'aura aure ba da Mujahid ba kamar yanda
suka gani a rubuce a invitation, tofa wani maroki sake kusa da Liman ya kururuce! Fad'i yake."
Allah ya tabbatar da Alkairi yau an d'aura Auran Amjad da Asma'u kan sadaki dubu Dari cif
ladan ba ajalan ba, tabbas wani kaya sai amale muna rik'on Allah ya sanya alkairi badi iwar
haka mu dawo suna." Take guri ya rikice jama'a da dama da su kasan Amjadu din suka rufu a
kansa suna yi masa Allah ya sanya alkairi duk ya rikice a lokacin domin al'amarin ya gigita shi
kuma yazo masa bazata! Wato abunda Jahid zai masa kenan, yawan jama'ar dake kansa yasa
ya nemi su Mujahid din ya rasa, haka dai ya dinga gaisawa da jama'a babu yabo babu fallasa a
tare dashi, shi tunani. Yake meye munufar Jahid din akan haka. Kafin kace kwabo 'yan jarida
sun rufu a kanshi kowa naso yaji ta bakinsa da kyar ta sub'uce dafa hannunsu ba tare da tace
musu komai ba...............
Kawai Yunsu da saurn yayyan babanmu suka shigo gidanmu lokacin INA gidan aunt Hauwa
mai kunshi nayi mana Dana tunda na tashi nake jin fad'uwar gaba, Kuma ina kallon wani irin
kallo da aunt Hauwa take min sai ta gyad'a kanta, Mamakin ko kallon me take min oho, ita aunt
hauwa tasan da faruwar abun domin Ya Aminu ya sani shima Kawu Yunusa ne ya fada masa
yace masa kuma yayi shiru da bakinsa shine shi kuma ya Sanar da aunt Hauwa din, to
dukaninsu sunyi murna da farin ciki sun San Baby Aysha baza tayi maraicin uwa ba. UMMA ta
shimfid'a musu ta barma suka zazzauna bayan gaishe-gaishe Kawu Yace." Ga sadakin 'yar
kinan Asma'u an d'aura aure." Umma tace"Alhamdullahi Allah ne abun godiya ina yi mata fatan
alkairi da samun zaman Lafiya gidan minjinta." Kawu Yunusa yw zakud'a tare da bata fuska
yace." Ba da Wanda kike tunani aka d'aura mata aure ba, yarinyar mu Mun d'aura mata aure ne
da yaro Dan kirki Wato Amjadu bisa fa yardar shi wancan yaron wato Mujahid mun b'oye muku
faruwar al'amarin ne saboda kar Ku kawo mana nakasu a kai saboda haka shi Mujahid din yaga
cancantar ya barwa Amjad din Asma'u saboda wasu dalili NASA,saura Wannan karon ma ki
zugata ra bujirewa Umarnin mu."!! Yana gama maganar sa ya Mike yana wani baza babbar
Riga, take sauran ma suka mike suka futa daga gidan. Suka bar Umma da kudi a hannu tana
mamakin Wannan al'amari.
*31/11/2019*
*BABBAN YARO*
*MALLAKAR BINTA UMAR
*70*
Wannan al'amari ya d'agawa Umma hankali sosai ta inda ta fara tunani. Artabun da zata sha da
Asma'u saboda tasan halin taurin kanta da kafiyar ta, Amma itama taji dadin wannan Abu ko
babu komai baby Aysha ta samu uwa baza tayi maraici ba. Tanan zaune har jama'a suka fara
cika gidan sai ta saki fuskarta ta dinga karb'ar baki. Har lokacin da 'yan d'aurin aure suka shigo
Aminu ya shigo gidan da gayyar abokan shi sai fama vedio da hutana suke yi. Dole Umma ts
fito aka yi hoton da ita saboda tarihi.Aminu sai washe Baki yake yana gaisawa da jama'a, can
ya kalli Umma tare da fad'in"Ina Asma'u ne? Umma tace"Tana gidan auntku ita da kawayen ta."
Ya Aminu yace." Ya kamata tazo muyi hoton tarihi."Umma tace"Kai ta hoto kake Aminu shin wai
kasan abunda ke faruwa ma kuwa. "? Aminu yace." Na San komai Umma Asma'u dai ta auri
Amjad hakuri ne ya kamace ta domin anyi mata laifi dole a rarrashe ta."Umma tace"Ina gudun
abunda zai je ya dawo n........ Kafin ta rufe bakinta suka shigo gidan, hankali jama'a yayi caaaa!
Kan Asma'u kowa na fadin albarka cin bakinsa akan ta, murmushi kwai tayi hade da rufe fuska
su Maryam suka rufa mata baya, Munnu kuwa dama tun ana gobe d'aurin aure ta koma gida.
Maryam ce tace"Wallahi kinyi kyawun da baki tab'a yin irinsa ba a duniya Asma'u wai dama
haka kike da kyau!.
Hafsa da bata San abunda yake faruwa ba, tunda tun ana saura kwana biyu tazo gudansu
Asma'u suka had'u da sauran kwayen su irinsu Alina ake gudanar da shagalin buki tare
tace"Wallahi nima haka nifa k'amshin da take yi ne nake bala'in so gaskiya dole idan na tashi
aure aunty Hauwa tayi min irin wannan gyaran domin in burge autan maza." Shewa! Suka sa,
Alina ta tab'e baki tare da fadin"Yo ke dama Hafsi wannan jikin naki ai dole sai da mugayen
turarrika masu karfin gaske. " b'ata fuska tayi tace"Alina bana son iskanci aikin banza kawai."
Cikin danne damuwar da nake ciki gami da fuduwar
Gaban dake damuna tunda na tashi nace" Alina ki saurara don Allah bana son tashin hankali a
bukina." Dariya suka kwashe da ita..... Waya ta dake hannun Hafsa na karba INA dubawa naga
5miscall daga Jahid, kiram shi mayi, aikuwa tana daf da tsinkewa ya dauka muka gaisa a nutse
yace." Ganinan zanzo daukar ki zamuyi hotuna da abokaina." Yana gama maganar shi ya
kashe wayar .... Tsoro ne ya shiga zuciya ta nace"Allah yasa kar Jahid ya taba ni tunda yanzu
yaga an d'aura aurenmu. Sama-sama muke hira dasu Alina Umma ta leko dakin tana
fad'in"Asma'u kizo ki daukar muku abunci mana." Maryam ce ta mike da sauri tana fadin"Gaba
Umma mu meye aikin mu, amarya guda dama yanzu nake cewa bari in zo in daukar mana
towon d'aurin aure. " Umma tace"Nima abunda na gani kenan. Dukanin Ku babu bare a gidan
nan duk yan gida ne." Marya ta bi bayan Umma tana fadin Wallahi kuwa.'' Ina kallonsu sun rufu
kam abunci suna ci suna shewa cikin farin ciki, sai suka bani sha'awa sosai ko wace mace tana
farin ciki da ranar auranta ni kuma na tsinci kaina da bakin ciki komeye dalili oho. Wayar Jahid
CE ta katse min tunanin da nake yi yace." Ki fito ina jiran ki amaryar mu." Sam ban fahimci me
maganar shi take nufi ba, na miike Alina tace"Ko inzo in raka kine."?
Gyad'a kaina nayi kawai na barsu a dakin. Dakin Umma na shiga tana cikin Uwar daki ita da
jama'a. Tana ganina tsabar abunda take yi jiki a sanyaye ta k'araso inda nake tsaye, Umma duk
a tsorace take tana gudun kar Asma'u ta tsinkata cikin jama'a. A hankali nace"Jahid ne ya kirani
a waya yanzu wai inje zamuyi hoto da abokansa." Jim! Umma tayi na minti biyu tace"Anya
Asma'u akwai dacewar hakan kwa
"? Sunkuyar da kaina nayi tace" Kije tom ban san manufarsa ba amma ki cire wannan yalolon
mayafin na jikin ki tunda kinga irin yadin dake jikin ki kamar Net gashi kinyi dinki matsatsatse
kamar jaraba idan da hali ma kin sauya kaya kawai. In babu hali to ki sa mayafi babba tunda
kinga gurin da zakuje ba shi kadai bane." Nace"Insha Allah Umma." Wata shegiyar liffaya na
zare cikin ledar ta fara kal mai golden d'in stones a jikinta tana da manyan zanen fulawa Umma
da kanta ta nad'a min a jikina na rike k'aramar pose dina mahadin takamin dake k'afafuna, na
futa daga gidan a nutse. Shi kadai na gani jingine a jikin motar sa, yana sakar min murmushin
sa nima na mayar masa bude min motar yayi na shiga na zauna shima ya zauna mazaunin sa
ya kunna motar muka bar gurin. Kallona yayi da Murmushi a fuskarsa yace." Amaryamu kinyi
kyau mutuka Wallahi." Nace"My Jahid kenan Ina maka fatan alkairi a rayuwar ka." Gyada kansa
yayi yana jin wani Abu cikin zuciyarsa yace." Alkairi Allah ya dauwama a duk inda kike Asma'u.
" Ameeen ameen mijina " abunda nace kenan cikin jin kunyar sa.
Shi kam Jahid draving yake yana addu'a cikin zuciyarsa kan bala'in son da yake wa Asma'u
wacce a yanzu ta zama mallakin wani
Ganin mun dauki hanyar Jambulo yasa nace"Jahid ina zaka kaini ne."?yace." Gidana mana kin
San abokai da 'yan uwa sun had'a min walima k'arfe shida na yamma shine na dauko ki ki
shirya a gabana idan anjima zan sanya a dauko kawayen ki." Cikin takaicin sa nace"Jahid
wannan bayi bane fisabillilahi a ina zan zauna har a wa hudu yanzu." Ya bata fuska tare da
fadin''ki zauna gurin granny mana wani abun ne."! Nace"Jahid kasan bama shiri sosai da mai
gidan me zai sanya in zauna masa a gida. " yace." Baya gari Amjad ki kwantar da hankalin ki
" shiru nayi masa ganin ransa kamar ya soma b'aci a zamana dashi na fuskanci baya son
ja'inja."
Ko da muka shiga cikin gidan babu kowa a gurin sai masu gadi da karnuka da suke kwance sai
dai na lura da karuwar motoci a gurin, kai tsaye part din Amjadu muka nufa har shi Jahid din.
Cikin rashin sanin komai na shiga ciki. Amjad Granny Iyami Baba Rakiya da wasu mata uku
suna zaune a parlor suna hira. Sai a lokacin kunya ta kamani nayi kamar in koma da baya.
Baby dake jikin iyami ta tsandare da ihu!! Wanda ya sanya shi bude limsassun idonsa ya mike
da sauri hankalin sa na kan babyn dake zillo dole sai ta sakko tazo gurina. Granny tace da
Iyami ta sake ta, aikuwa Iyami na sakin ta ta rarrafo dasauri ta kamani ta mike tsaye da sauri na
dauke ta hade da rungume ta tsam a jikina, baby Aysha ta dinga kyalkyala dariya tana kallon
Jahud dake tsaye kusa dani yana kallon abun mamaki.
Kallo guda yayi musu ya koma ya kwanta kan doguwar kujera da yake kwance lumshe idonsa
yayi yana haskon fuskar Asma'u a ganin da yayi mata yanzu, tunani yake yi shi dai iya sanin sa
sao dare ake kawo amarya tom ita me ya kawo ta gidan shi da rana tsaka. Jahid ya karasa cikin
parlor sosai suna gaisawa da granny cikin mutumci yace." Granny ga alk'awarin mu nan na
kawo miki har gida kin gane dai manufata duk Wani Abu da zai biyo baya mai sauki ne." Granny
tace"Ka cika d'an halak kuwa ubangji Allah yayi maka albarka ya raba da sharrin duniya."
Yace." Ameeen ya rabbi Bari in shiga gida akwai abokanan mu dake jirana, Asma'u zata zauna
nan zuwa anjima. " gyada kai kurrum granny tayi domin ita San ya fad'i hakane kawai amma
aikin gama ya riga ya gama. Duk abunda yake faruwa a gurin yana jinsu, yayi bakam! Hancin
sa ne yake shak'o masa daddad'an kamshi Wanda ya gaura ye parlor gaba daya wato k'amshin
Asma'u kenan. Jahid yazo ya wuce ni ba tare da yace min komai bsla ya futa, kallo na bishi
dashi cike da mamaki! Lokaci guda fad'uwar gabana ya tsananta jiki babu k'wari na k'araso
gurin su, granny ta mike Da sauri hade da rike hannuna muka nufi wani bedroom
Kallo ya bisu dashi har sai ds suka shige, sannan ya mike zaune hade da dafe kansa yana
tunanin irin zaman da zasuyi da Asma'u a cikin gidansa. Gefan gado ta zanar dani ta zauna
muna fuskantar juna da ita, a nutsu tace"Aminci Allah ya tabbata agare ki yarinyar kirki."
Hannunta ns rike sosai Nace "Tare dake granny, jikina na bani akwai wani Abu ni kam na kasa
fahimtar inda maganar Ku ta dosa ke da Jahid." Granny ts girgiza kanta take naga k'walla ns
zubo mata. Tafin hannuna na sanya na goge mata INA kallonta cikin mamaki nace"Granny don
girman Allahu ki Sanar dani meke faruwa."? Kai tsaye tace",Sanar dake abunda yake faruwa ya
zama dole domin an shiga Hakkin ki, mun so kanmu da yawa, to amma ni ina ganin gata akai
miki Wanda ko bayan babu raina zaki gode min da wannan alkairin da nayi miki, ina so kiyiwa
magana ta kyakyawan fahimta." Nace"Insha Allahu." Granny ta gyara zaman ta sosai ta kwashe
dukaninin abunda yake faruwa tsakanin Jahid da mahaifiyar sa da yanda Granny taje har gida
domin ta nusasshe da ita ta ci mata mutumci da yanda suka yanke hukunci ita da Jahid din kan
auran ta ya koma kan Amjadu domin ta kula da baby Aysha........... Tun kafin granny ta karasa
maganar ta hawaye suka wanke fuskata ina mamakin wannan yankan kaunar da suka yi min
yanzu Abunda Jahid zai min Kenan? Yaudara kiri-kiri Innalillahi, Jahid ya munafurce ni, yayi min
abunda ban taba tsammani ba, ni tunda Amjadu ya auri Mimi a rayuwata ban tab'a kawowaa zai
zama mijina bs shine babu Neman shawara babu komai suka yanke min Wannan hukunci
kamar wata 'yar tsana. Idan Momyna ta hana shi auranena CE masa akayi Neman kai nake yi
da kaina kawai zai sanya a d'aura min aure da Amjadu Wanda a halin yanzu muke buga tsaka
dashi saboda rashin jituwa ta yaya zaman aure dashi zai yiwu..... Hawaye kawai nake zubarwa
ina kallon granny nama kasa cewa komai. Take itama naga ta fara share hawaye tace"Hak'ika
ba'a kyauta Miki ba Asma'u amma kiyi hak'ura Insha Allah zakiyi alfahiri da Wannan auren." Ina
Kuka Nace " Granny Yanzu meye ma'anar kawo ni gidanan bayan an San Abunda akayi min.
Cikin sigar rarrashin granny tace" Dole s kawo ki gidan auran ki ko ba yanzu ba, kwai da mun
yanke wannan sha'awar ne da Yayarki Hauwa dashi kanshi Mujahid din domin yin hakan shine
zai kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya ba tare da jama'a sun fahimci abunda yake faruwa
ba, kinga wani zai iya fada miki haka cikin gidan Ku babu shakka
Zaki shiga fargaba da tashin hankali a lokacin Wanda hakan zai jawo hankalin mahaifiyar ki ya
tashi har jama'a su fuskan ci akwai matsala saboda haka da yardar Allah kin shigo gidan auran
ki zaki zauna a karkashin mijin ki kamar yanda ko wace mace take yin biyyayar aure." Kuka na
fashe dashi sosai nace"Granny idan akai min haka ba'akyauta min ba, shikensn sai kace wata
'yar tsana ni akwai abunda zanyi a gidanmu yanzu
" granny tayi murmushi Wanda iya kadai ce tasan ma'anar sa tace." Duk abunda zakiyi a
gidanku ba kamar nan gidan ba, domin nan shine gidan ki halak malak sai kin fi sakewa kiyi
yanda kike so saboda haka ki kwantar da hankali ki insha Allahu kome kike manta a can nasan
zasu kawo miki shi har gidan ki." Kwata-kwata bana son yin jayyaya da tsohuwar yasa nayi
mata shiru kawai ita kuma ta mike da sauri tana fadin "Bari inzo yanzu." Tana futa na kwanta ka
bed din hade da fashewa da Kuka mai tsananin gaske, Wannan wace irin kaddara ce ni
Asma'u. " Baby Aysha dake wasa can karshen gado ta rarrafo ta yaye jikina tana kallon yanda
hawaye suke tsere a kumatuna. Cike da tausayi ns rungume yarinyar a jikina Mimi ns tuno
lokacin naji kamar in bita in huta da wannan rud'un na duniya. Kuka sosai nake yi mai futar da
sauti.!Cikin wannan hali suka shigo suka same ta. Amjad daga bakin kofa ya tsaya ya soka
hannunwan sa cikin aljuhu fuskarsa babu walwala ko ta kwabo kallon su kawai yake yi yayin da
yake jin kukan ta yana masa wani irin zafi a zuciya. Mamaki yake sosai ko kukan me take yi
idan hakane shima sai ya Dora hannu aka yayi ta kuka ko ya samu sassauci Cikin zuciyarsa
tunda dai bata fishi jin ciwon abunda ya faru ba, don dai Jahid ya wuce komsiba gurin shi
shiyasa kawai yayi masa shiru domin har yanzu shi da si magana ta fatar baki bata had'asu ba
sai dai ido kawai. Granny ta karasa gadon ta dauke Baby daga jikinta tana kokarin mikar da ita
zaune, tace"Kiyi hakuri Asma'u ki tashi zaune ga Mijin ki ya shigo ina so in hada Ku guri guda in
muku fad'a kukan bashi da amfani kuma INA me tabbatar miki da cewar kukan nan da kike yi
zai zama alkairi a rayuwar ki." Jin Granny tace ga mijinta ya shigo ya sanya fad'uwar gabanta ya
tsananta tana tsoron ta kalleshi wai a matsayin miji domin ta lura da kallon banzan da yayi mata
tun farkon shigowar ta gidan.... Shi kam Amjadu a zabbaban kamshi turaran Asma'u da ya
d'umame dakin shine ya same shi yana nema ya sanya shi cikin wani yanayi.....
*2/12/2019*