Showing 9001 words to 12000 words out of 95753 words

Chapter 4 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

ta
mike tsaye sannan ya nufi massalaci, motsin Umma Naji a tsakar gida tana alwala da sauri na
koma na zauna, domin bana son na futa mu had'u. Mimi ta futa ta barni,, ko minti biyu ba ayi ba
kira ya shigo wayar Mimi, daga inda nake in hangowa *Heart beat* sunan da nagi kenan, cikin
zafin zuciya na dauki wayar na kashe! A fili nace"Aikin banza da wofi asubar fari za'a damu
mutane. " wani kiran ne ya kara shigowa na kashe da sauri,, A'a wani kiran ya kara shigowa na
kashe, sai da ya kira sau bakwai ina kashewa, yana kiran na takwas din ne kawai na kashe
wayar gaba d'aya.
Nashi b'angaran sakato yayi da wayar a hannu lokacin da ya kira suka fad'a masa cewar an
kashe wayar ma gaba d'aya, tunani ya shiga yi anya Mimi zata kashe masa waya kuwa? Why!!!
Me yake faruwa ne.? Jefar da wayar yayi kan bed ya yunk'ura ya tashi zaune kwalin sigari ya
dauko ya bata wuta ya fara fesawa cikinsa hayak'i da sanyi safiyar na, da sauri kuma ya dauko
wayar tare da nemo numbar rambow bugu guda tayi ya dauka baki na rawa yace."good
morning sir." Bai amsa ba yace." Meye labari ina fatan ka yi aikin da na sanya ka."? Rambow
yace." Yes sir Ashe ma ba d'an gari bane yazo bak'unta ne dan barno ne wato mai duguri." Da
babbar murya yace."kaje Sanar dashi cewar inji ya bar garin nan kafin in k'araso idan ba haka
ba sai da uwarsa ta haifi wani Wallahi. "!!!! Rambo ya tsorata jin furucin oban gidan nasa, ta
yaya zai iya zuwa ya fad'awa mutumi haka, amma duk Dan a zauna lafiya yace." Insha Allahu
zani yanzu." Kashe wayar yayi yana huci!!!


Mimi ta shigo a tsanake ta shimfid'a dadduma ta tayar da sallah, futa nayi daga dakin nima
domin dauro alwala. Bayan ta idar Da sallahr ne sai ta dauki wayar kawai ta ganta a kashe
alhalin a kunne ta bar ta. Kunnawa tayi tana zargin Asma'u cewar ita ce zata kashe mata waya.
Aikuwa ko minti biyar ba ayi ba, kira ya shigo wayar tana dubawa taga *Heartbeat* wani
murmushi ta saki had'e da kwanciya kan katifar tana lumshe ido ta d'aga wayar. Tare Da
fad'in"Assalamu alaikum."
Sama-sama ya amsa murya a kaurare! Yace." Had'a ni da wannan yarinyar." Dai-dai lokacin
dana shigo dakin kenan ina jin komai tunda a hands free wayar take.. Cikin tsawa yace." Ko ba
kyaji ne."!! Mimi ta tsorata mutuka, muryar ta na rawa tace"Wace yarinyar."? Kai tsaye yace."
Asma'u. " jin ya anbaci sunana yasa na zabga tsaki da k'arfi don yaji, aikuwa yaji lokacin da tayi

tsaki! Sai ya mike da sauri jikinsa na wata irin tsuma! Kamar Wanda ya sha tsumin 'yan bori ya
kwatsawa Mimi tsawa tare Da fad'in "Bata wayar naji ta a kusa dake."!!
Ganin yanda yake kurma wata irin tsawa ne yasa na fasa tada sallahr raina a mutukar b'ace na
karb'i wayar da take Mik'o min murya sama-sama nace" ta bani wayar meye."!! Tsaye ya mik'e
da sauri cikin hargagi yace." Budurwar 'yan daudu yarinya mai aji da kamun kai!! Budurwa me
lasisi a jahar kano, duk naga abunda kikayi jiya, ki sani kamar a gabana komai ya faru!
Wallahi-wallahi ki kiyayi haduwar mu dake sai kinyi mugun raina kanki!! Ni zaki zubar wa da
mutumci...... Katse shi nayi kafin ya k'arasa maganar tashi nima cikin hayaniya nace" Kai!!!!
Malam wai me ka dauki kanka ne? Meye ya shafe ka dani? Meye alakar ka dani da kake
wannan ihun! To bari kaji naji dad'i da ka gani ka sani jikina ba irin na ko wane lusarin namiji
bane irin ka mai aikata sab'on Allah yanzu nayi maka nisa! Kuma tab'a min jiki da kayi kwanakin
baya na barka da Allah ehe!!! Ita ma Mimi addu'a nake mata Allah ya tsare ta daga sharrin
k........."ShautUp Your dirty mouth."! A zafafe! Tsorata nayi amma saboda taurin kai yasa nace"
Ank'iyin shiru d'in duk abunda na fad'a gaskiya ne ai Mtssss." Na buga wani irin tsaki had'e da
jefawa Mimi wayar a cinyar ta. Ji nayi yana fad'i" Ok zamu had'u ne zaki San Wanda kike
wannan rashin kunya wallahi sai kin maimata min duk abunda kika fad'a kuma, kiyi gaggawar
korar wannan mummunar saurayin naki bak'i me kamar alade irin ki, idan ya sake Nazo sai na
b'adda shi a duniyar nan."!!
Mimi tayi sakato da waya a hannu bayan ya kashe nu kuwa tada sallah ta nayi raina a mugun
b'ace!
Wani irin tunani take a zuciyar ta, wannan tashin hankali da guy nan yake yi na lafiya ne kuwa?
Anya ba son Asma'u yake ba? Take tambayar kanta, in kuwa hakane babu shakka rayuwar ta
tana cikin garari domin baza ta iya had'a miji da Asama ba, gashi duk duniyar nan babu namijin
da take so kamar sa, tana ganin sai da ta mutu babu aure.
Wayar ra dauka tana neman numbar sa, bugu guda ya dauki wayar, cikin siriryar muryar ta
tace"My kayi hak'uri don girman Allah nasan ranka yanzu a b'ace yake, babu shakka Asma'u
bata kyauta ba."
Ajiyar zuciya ya sauke a kashi d'ari na damuwar sa kashi casa'in ya ragu , yaji dadin maganar
Mimi yace." Momyna 'yar uwarki bata da kirki wallahi kanta rawa yake yi, ki rink'a yi mata fad'a
kinji ko."

Mimi tace"Kullum kuwa cikin fad'a muke yi da ita Sam! Asma'u bata son San gaskiya, wallahi."
Ina ji ina sallahr lallai Mimi har sunyi sabon da zata dinga kai suka ta a gurin shi.sauri nake in
idar muyi wacce zamu yi da ita.

Ina jinsa yace." Kar ki biye mata da duk abunda zata yi miki na rashin mutum ci domin na lura
tashan balaga take, idan tayi ba dai-dai ba ki yi mata fad'a koda zakuyi doke-doke da ita kuwa."
Mimi tace." Insha Allahu kar ka damu." Yace." Zan dawo gobe ko jibi kiyi min kwalliya me kyau
sannan ki turo min pictures dinki ta whatsp zan gani." Cike da kunya tace" shikkenan ka bude
data zan turo maka." Sallama sukayi Mimi tana saki murmushi daga ni tana cike da farin ciki.

Ina idar da sallah ko addu'a banyi ba nayi kan Mimi da masifa nace "Mimi kin Dade baki kai

suka ta gurin sa, ba ki fad'i abunda ya fi haka a gurin shi ba damuwa ta bace, kece yake gaban
ki da har idonki ya rufe a kansa kika kasa fari da bak'i aikin banza aikin hofi ina kara dai tunasar
dake cewar kiyi hattara ki kula idan ba haka ba ke zai kai ya Baro....Wannan karon Mimi bata
k'yale ni ba, itama a fusace ! Tayo kaina tare da fad'in" duk abunda zaki fada ki fada ke ya shafa
kowa rai yayi wa dad'i ba kamar me shi ba ne Asma'u kije kiyi abunda kike so kuma wallahi kar
ki sake ki kara zagina domin uba bai fi uba ba. " Kanta nayi zuciya ta namin zafi nace" Sai nayi
RAYUWAR ki ce ko tawa dake dashi da Yaya Aminu kusa tsinken tsire ku tsikare n......Ban
k'arasa ba naji saukar Mari! Da sauri na dafe fuskata ina kallon Wanda yayi min haka, Umma ce
tsaye tsakiyar dakin ranta a mugun bace tace" Tsokane mata ido zakiyi ne Mara kunya."? Shuru
nayi hade da sunkuyar da kaina kasa ta cigaba da cewa." Duk rashin mutumcin da kikayi ina
jinki, ina ce Mimi ta girme ki da har kike tsaye kanta kina nuna ta da d'an yatsa kan ta fada miki
gaskiya." Mimi tace"Umma kiyi hakuri don Allah." Tace" ke zan bawa hakuri Mimi da kike
k'okarin nusar min da ita, duk da rashin mutumcin da take miki." Mimi tace"Umma wannan duk
abunda ya shafe mu ne, dama mun saba fad'a haka." Cike da tausayi take kallon Mimin ta rasa
wace irin zuciyace da ita, tace." Ba irin wannan fad'an kuka saba ba. Ke kam zuciyar ki tana da
sanyi ina addu'ar kar Allah ya kai gidan me mata ki sha wuya domin kishiyoyin ki zasu raina ki
wallahi." Shiru Mimi tayi. Ita kuma Umma ta kama hanyar futa,
D'an juyo wa tayi tana kallon katifar mu, waya ta gani tamfatsetsiya cike da mamaki
tace"Wannan wayar waye a cikin Ku."? Shiru mukayi dukanin mu.Cike da zargi da tuhuma
tace." Ba tambayar Ku nake ba."?
Baki na rawa Mimi tace"Tawa ce Ummah." Cikin mamaki tace "Mimi yaushe kikayi magana
babu labari." Yanda Umma ta fad'i maganar kai tsaye ya tabbatar mana da cewar Hankalin ta ya
tashi. Da sauri tace"Mik'omin wayar nan." Hannu na rawa Mimi ta mik'a mata, ta karb'a had'e da
fucewa daga d'akin. Shuru muka yi dukanin mu, yanzu na daina jin taikacin komai nayi kwanciya kawai a zuciya ta
nace"Ke ma abunda ake min a gidanan yazo kanki sai kiji in da dad'i baya na juya mata ina
lumshe idona babu abunda ya dame ni, injita ta kwanta itama jikinta duk yayi sanyi.

K'arfe takwas dai-dai naji hayaniyar Ya Aminu a kaina rumtse idona nayi da k'arfi ina fadin"Ya
Aminu Dan bala'i ne wallahi.

"Ke Mimi tashe ta kuzo rumfar Umma ina Neman Ku." Yafad'a cikin daga murya. Futa yayi ita
kuma tafara tashi na, tsaki ns buga ina kara gyara kwanciya ta, tace"Nasan dai kina ji tom Ya
Aminu ne kin san dai halinsa.
Nace"Kije ke ni kam babu inda zani." Mik'ewa tayi tana fadin "Taurin kanki ne yake jawo miki
komai.

Ina jinta ta futa, minti biyu na mike nima domin tsoro ne ya shige nasan halin Ya Aminu bai k'i ya
shigo ya dake ni da sanyi safiyar nan ba.

Ina shiga dakin Umma na yadda Aunt Hauwa har tazo suna ta mai da magana, zama nayi
gefan ta muka gaisa hannun Islam na jawo INA fadin " Baki je makaranta ba yau."? Aunt ta kalle
ni tana nazari tace"Ke kuma waye ya fasa miki gefan fuska." Kwallah ce ta taru a idona nayi

shiru hade da sunkuyar da kaina.

Yaya Aminu yace." Nine nan! Na fasa mata idan kuma tayi min gaddams kan abunda zan
tambaye ta yanzu to bakinta zan fasa mata har sai hakori ya futa." Kallonsa nayi cike da rashin
tsoro, cikin tsawa yace." Ki fada min a ina kika samo wannan tafkekiyar wayar me uban tsada
kin San kuwa kud'inta,? Nasan wayar taki ce, Mimi ta rufa miki asiri ne kawai kamar yanda ta
saba." Mimi na kalla dake wasa da hannunwan ta nace"Abunda kike zo kika CE musu kenan."?
Da Jan ido ta kalle ni, nace"Kiji tsoron Allah Mimi." Murya na rawa tace"Umma me nace tunda
Nazo gurin nan." Umma tace"Baki ce komai ba zargi take." Ya Aminu na kalla fuska a hade
nace" Waya ta Mimi ce don haka ita zaka tuhuma bani ba, yanda ka ganta nima haka na ganta.
"










*4/November/2019*
[11/4, 5:49 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*


*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*



*40*




Yaya Aminu ya kalli Mimi cike da mamaki domin bai tab'a tsammanin faruwan hakan daga gurin
ta ba, a nutse yace." Hakane Mimi."? Gyda kanta tayi tana k'ara sunkuyar da kai kasa, aunt
Hauwa tayi karaf tana fad'in"dama baku San da wayar a hannunta ba."? Umma tace"Bamu sani

ba Wallahi sai yau" aunt tace"To ai ko lokacin da suka je gidana da wayar a hannunta yau
kwanansu Uku kenan." Umma ts tsare Mimi da kallon tuhuma tana fad'in" Ki fada min gaskiya
Mimi wannan wayar ta wacece tsakanin ke da Asma'u. "Mimi tace" Wallahi Umma tawa Ce."
Tace" waye ya baki ita." Shiru tayi, da k'arfi Ya Aminu yace." Ba tambayar ki ake ba."
Cikin inda-inda tace"Amjadu ne." Dukaninsu jikinsu yayi sanyi Mussaman Aminu Umma
tace"Kina nufin yaron nan mai company ko me."? Aunt tace"K'warai kuwa Umma wai sonta
yake yi shine ya bata waya." Umma tace" Ni abunda na kasa fahimta a nan shine, shin da ke da
ita Asma'u wa yake so a cikin Ku? Ke ya baki waya mai tsada ita kuma ya bata KUDI da kaya
dukanin Ku akwai alamun tambaya a tare daku."

Aunt tace"Shine maganar wallahi nima kaina ya kulle sosai." Hannu Ya Aminu ya mik'a tare da
fad'in"Bani wayar." Mimi ta mik'a masa wayar jikinta a sanyaye . tashi yayi ya futa ranshi a
mugun b'ace!

*********
Yinin ranan haka yayi shi babu dad'i ko da suka futa da Anthony ma shi kad'ai ya dinga
zurga-zurgar sa, sai sa komai ya kammala sannan suka dawo gida.

Wanka kwai yayi ya futo parlor inda Anthony yake zaune yana aiki da loptol firji ya nufa ya
dauko ruwa na gora ma sanyi tsiya yazo ya zauna kan kujera hade da bud'e ruwan ya fara
tuttulawa cikinsa.
[11/4, 5:34 PM] .: Ko da wasa bai kara kallon pictures din nan ba, yana ganin idan ya k'ara
kallonsu zai iya had'iyar zuciya ya mutu. Wayar shi ya bude hade da bude data ya shiga whatsp
yana dubawa, Alina ya ga ta turo masa da pictures, domin kwana biyu baya d'aukar wayarta ko
ta kira, ko wancan karon ma da yaje birthday din ta cin sa'a tayi. Yana bude wa gaban shi Yayi wani irin bugawa ganin da yayi Asma'u tsakiyar 'yan iskan abokan
Alina sunyi hoto*innalillahi wa'inna ilahi rajun* shine abunda ya furta ya mik'a zaune sosai zufa!!
Na keto masa hotonan yake dubawa sosai lallai yarinyar tayi nisa, shi a ganinshi kamar jarabar
ta ce ta sanya take shiga cikin maza ko zata rage wa kanta damuwa amma idan ba haka ba
mace d'iyar Hausa Fulani tayi irin wannan d'inki Wanda dashi babu maraba da tsirara ta dinga
keta maza, lokaci guda yaji zuciyarsa tana wani zafi tare da muguwar tsanar yarinyar, gani yake
shine ya cuci kansa kwanaki baya da ta kawo masa kanta har gida, da ya sani ya biyawa kansa
bukata tunda ita bata tausayin kanta.

Pictures da Mimi ta turo masa yake dubawa, du Rabin su ita da Asma'u ne sai wannan
budurwar da ya tab'a ganinsu tare wato Munnu, kayansu iri d'aya haka ma Dinkin su iri daya to
wai me yasa d'inki a jikin Asma'u yafi nuna tsaraci. Shi kadai yake WANNAN tunanin, wata
zuciyar tace masa ai duk tafi su ciki ta ko wane fanni.. Fuskarta yake kallo kamar zai lashe ta,
har kara zomming din pic din yayi dai-dai ita yana kare mata kallo, ajiyar zuciya ya sauke tare
da fadin"Zaki gane Baki D's wayo yarinya, wani pic din ya bude ,sai da wayar ta kusa fad'uwa
daga hannunsa, ganin guy nan shi da ita suna kallon juna kamar masu kallon love. Ji yayi duk
duniyar tayi masa zafi, ya kalli Anthony da jan ido cikin turanci yace." Gobe zan wuce najeria

Tunda komai ya kammala anan."
Anthony ya gyad'a kansa gami da cigaba da aikinsa

Mik'ewa yayi da sassarafa ya shige bedroom din, kan wata duguwar kujera ya zube hade da
dafe kanshi, yana cije lips din sa tunani kawai yake wane irin hukunci ya kamata yayi wa
yarinyar nan.
[11/4, 5:47 PM: *****
Kwanan bakin ciki da damuwa yayi a ranar, washe gari kuwa da wuri ya gama sallamar duk
Wanda ya dace, ya bar amanar komai a hannun Anthony ya nufi k'asar sa ta gado wato Najeria.

Sha biyu dai-dai jirgin su ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu kano, su Rambo na gefa suna
ganin saukowar sa suka k'araso da sauri Rambo ya karb'i wayoyinsa shi kuma doh-doh ya
karb'i 'yar jakar sa. Suka nufi mota.

Satar kallon fuskar sa suke ganin fuskar ogan nasu kamar Wanda aka aikowa masa da
mutuwar iyayensa, Tunda ya shiga motar babu Wanda ya kula a cikinsu har suka isa gida. Get
Man yana ta d'aga masa hannu tare da fatan alkairi ko kallonsa bai yi ba Doh-doh na gyara
parking ya bude motar ya futo ba tare da ya jira rambo ya bude masa ba.
Kai tsaye ciki ya nufa suka rufa masa baya, nan parlor suka aje masa wayoyin shi hade da jakar
shi, suka futa da sauri.
Yana shiga bedroom dinshi ya fada toilet Wanka yayi ya futo ko mai bai shafa ba, parlor ya futo
masifa na cin sa, zama yayi hade da kiran Rambo a waya domin yaji meye labarin guy nan
yana ganin ta kanshi zai fara.






*4/November/2019*
[11/5, 11:28 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*




*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*

*41*




Rambo ya shigo cike da Ladabi yace. " Sir g... Gurin zama ya nuna masa Rambo ya zauna
jikinsa a sanyaye saboda yanayin da ya ga ogan nasu ya bashi tsoro. Cikin dakakkiyar murya
yace." Wannan guy ya bar garin nan ko kuwa."? Rambo yace." E to jiya da na ga gilmarsu a
mota shida abokina sun wuce can Titin rimin gata, ina kyauta ta zaton can masaukin sa, yake."
Mik'ewa tsaye yayi hade da goya hannunsa a baya, ya kalli Rbow da jajayen idonsa yace." Kaje
kazo min dashi, nan." Rambo ya mik'e jiki na rawa ya futa daga d'akin. Shi kuma ya cigaba da
kaiwa da kawo wa cikin parlor
Rambo da doh-doh sun jima a tsaye suna tattauna maganar kafin Rambo ya shiga mota ya tafi,
yanda suka tsara shine baza su biyewa Ogansu ba, zasu yi masa dabara ne kawai saboda
suna ganin a yanda yake kan dokin zuciya zai iya kashe guy nan kamar yanda ya fad'a.
*Amjad* yafi a wa guda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login