Showing 84001 words to 87000 words out of 95753 words
Chapter 29 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
kuwa sun
hada baki da mahaifin sa, har anje gidan su Asma'u ankai kud'in aure da sadaki lokaci kurrum
ake jira kuma kullum suna tare domin shakuwar su ta yanzu tafi ta da waya kullum babu dare
babu rana haka suke yi.
****
Watan Amjadu Biyu a chana komai ya kammala nan ya wuce Ingila domin can ma akwai
bukatar yaje din domin duba company shi da ganin irin cigaban da aka samu. A shkekarar
kullum suna tare da granny a waya maganar guda ce Babu Aysha tayi kaza kaza wani lokacin
sai dai granny ta kashe wayar ta kyaleshi ko kuma ta kara wayar bakin baby Aysha tayi ta
gwalantu shi kuma yana kyalkyala dariya sai Granny ts karb'i wayar sannan zai ce da ita wai
tana fad'a masa ne tayi missing d'insa sosai. Granny tsabar haushi sai ta kashe wayar tana
fadin'Kai da ita kuka San wannan."
****
Muna a dai-dai sahu nida Munnu tace"Ke Wallahi yau sai munje gidan Young millionaire mun
dauko baby Aysha ta kwana biyu a hannun mu tunda kince ai mahaifin nata bayanan ko."?Nace
" Bayan nan yayi tafiya lallai Munnu ke 'yar rigima ce ni kam babu ruwana Wallahi. " Munnu
tace"Ki sa wasa ki gani, mai a dai-dai muje Jambulo." Aikuwa Mai a dai-dai ta ya Karya kwana ,
nace "Munnu sai dai in ki shiga ke ni kam bazan shiga ba." Tace"Wallahi sai mun shiga tare
"Dariya NASA Nace " Zakiyi kaffara kuwa. Muna isa Munnu ta biyashi kudinsa muka tsaya bakin
gate din, take masu gadi suka bude mu din ba bakin bane a gidan, Jan hannuna take wai dole
sai na shiga ganin kar abun ya zama da zargi yasa na bi bayanta gabana na fad'uwa ni yanzu
Sam bana kaunar abunda zai hada ni da guy nan tunda yace s k'yale masa 'yar sa to sai a
k'yaleta domin a zauna lafiya.
Granny da Iyami na zaune a parlor suna kallon shirin dadin kowa tashar Arewa24 muka yi
sallama. Granny ta amsa tana fad'in "Lale maraba da manya baki lallai yau Baby Aysha na da
baki domin dai nasan domin ita kuka zo gidanan." Murmushi nayi na zauna Cikin kujera a nutse
muka gaisa sosai tace"Shikkenan saboda babu Aisha sai Ku yanke zumunci damu har Umman
taku ma ai wallahi bata kyauta ba." Hakuri na dinga bata INA fad'in"Bana samun lokacin zuwa
ne saboda makaranta. Granny tace" Yau watan baby Hudu a duniya ace kuna a matsayin
iyayenta babu Wanda yazo duba ta ai gaskiya naji haushin wannan Abu." Mu dai hakuri muke
bata, sannan muka gaisa da Iyami dake kallon tana dariyar durmarmu d Granny tace"Iyami
Kawu musu abunci." Duk da ina jin yunwa sai da nace "Granny a koshe muke Wallahi."
Hararata tayi tace"Wato kinanan da halin ki na cutar kai ko? Dubi bakin Ku a bushe kice min a
koshe kuke ai nasan daga makaranta kuka dawo." Shiru nayi kawai domin nasan dukanin
abunda zan fada Granny ba yarda zata yi ba. Munnu tace"Ina baby Aysha ne? Domin munzo
aba mu aronta." Granny tace"Yanzu kuwa tayi bacci wallahi ai kun fi k'arfin abaku Aron ta idan
ma kyauta kuka je a baku za'a baku ita kyauta." Munnu tace"Granny da gaske nake wallahi
zamuje da ita ta kwana biyu sai mu dawo da ita." Granny tace "Nima ai da gaske nake." Iyami
ce ta shigo da k'aton tire cike da nau'ikan abunci da abunsha ta aje kan dogun tebur din da
yake gabanmu. Granny tace "Iyami maza hada kayan baby Iyayenta zasu je da ita su ta kwana
biyu." Iyami tace"To Hajiya amma fa zamu sha kewa da yawa." Granny tace"Zamu huta da
rigima dai kinga zamuyi bacci harda munshari musamman ke." Dariya muka yi harda Iyami ta
nufi wani daki da sauri tana fad'in "Baby Aysha rigima kenan. Sosai muka saki jiki muka ci muka
koshi mana hira da granny Cikin barkwanci ni kam Allah-Allah nake a fito da baby Aysha na
ganta. Aikuwa sai ga Iyami ta fito da ita a kafadar ta daya hannun NATA kuma k'aramin akwatu
ne. Ni da Munnu rige-rige karb'ar ta mukayi Allah ya bani sa'a ina karb'ar ta na manna mata
kiss a kumatu ina dariya ganin yanda take motsa bakinta tana tsotsar hannunta, da alama
yunwa take ji. Granny tace" oh! Oh oh!! Wai meye amfanin abunda kuke yi ne, kuyi ta tsotsar
kumatun yarinya shima haka wancan sakaran yake yi, mata har bakinta tsotsa yake." Ni da
Munnu muka dariya nace"Ni kam sumbatar kumatun ta kawai nayi granny gaskiya Iyami ta iya
raino naji dadin ganin baby Aysha haa duna granny kamar ba bakwai ni ba."
Tana dariya tace"Yanzu zata nuna muka halin nata na k'uya Iyami kadai ta sani saboda ita take
bata abunci ni kaina wani lokacin sai taga dama take yarda dani." Aikuwa sai ta fara tab'e baki
tana so tasa kuka, rungume ta nayi ina rarrashin ta, granny kuwa sai dariya take mana, Iyami ta
shigo da fidar ta da sauri ta sanya mata a baki ta kama tana tsotsa sosai, Dan kanta ta cire
bakinta sannan ta fara daga hannu wai zataje gurin Iyami aikuwa Munnu tace"Baki isa ba kuwa
kin bar hannunta da sauri ta karb'a ta a hannuna ta dauki towel dinta ta goya ta a bayan ta,
mik'ewa nayi da sauri Iyami ta mik'o min duk abunda zamu bukata nata, nace "Granny zamu tafi
gida." Tace"To Ku gaida min Ummanku da kyau kuce ta kyauta." Nace insha Allah kuwa. "Har
waje Iyami ta rako mu tana d'agawa baby hannu ita kuwa sai dariya take bangala mata tana
daga bayan Munnu." Ganin rana ta kwalle nace dama zanga su Rambo da sun kaimu gida.
Wata zuciyar tace min lallai Asma'u kina da samun shiga. Ni kaina dariya nayiwa kaina. A
dai-dai sahu muka shiga nace"Munnu muje gida yau Umma taga baby inyaso sai ki tafi da ita
ko."? Munnu tace "Shikkenan muje.""' Wasa nake ma baby daga bayan Munnu ita kuma sai
bangale min baki take, nace"Laa Munnu kinga har ta soma hakori wallahi. " Munnu tace"Da
gaske ne." Nace sakkota ki gani.' Aikuwa ta fara kokarin saukota tana dubawa, Kuka ta fara yi
da alama tafi son goyon nace"Munnu mai da ita bayan baki ji yanda nake jin zafin Ku kanta
Cikin raina ba." Kokarin mai da ita take, naji kira ya shigo waya ta, hankalina na can gurin
rarrashinta ban duba waye me kiran ba na d'aga wayar hade da sallama.
Kukan Sweet heart dinshi ne yayi masa sallama, ranshi ya kara b'aci a fusace! Yace." Wai ke
wace irin mayya ce ne? Meye alak'ar ki da baby da zakiji har gida ki dauke ta, OK naji kamar
alamu kuna cikin abun hawa ne ana min gwajab-gwajab da yarinya tana kuka na rashin sabo.
Maza ki mai da ita inda kika daukota tun wuri."! Hannuna ne yake rawa bakina na motsi na rasa
abunda zan ce masa, Munnu dake kusa dani duk taji abunda yake cewa, hannu ta mik'a min
wai in bata wayar , domin in fidda kaina a gurin shi nayi saurin bata wayar ta karb'a a nutse
tace"Yallab'ai barka da rana." Jin muryar da bata Asma'u ba ya amsa da " Barka dai wacece
ke."? Munnu ta tsorata jin muryar sa a kausashe!! Tace." Munnubiya ce, dama umm! Dama....
Babanmu ne yace muzo humm nazo in d'aukar masa baby Aysha yana so ya ganta.......... Sam
bai gane Abunda take nufi domin shi har ga Allah ya mance da Kawun Mimi wato babban su
Munnu, yace." Ke! Bana son shashanci dallah!Ku mai da min da yarinya wato wayar ta baki
domin Ku shirya karya ni sa'anku ne."!? Cikin tsawa ya fad'i maganar! Nan Munnu ta kara
daburcewa tace"Da gaske ne kayi hakuri Wallahi an turo ni daga gidan profesor Muktar
Gyaranya ne ni 'yar shi CE" sai da ta fadin sunan Profesor Muktar sannan ya tuna da Mutumin ,
kashe wayar yayi ba tare da yace komai ba .Munnu ta kalleni tana dafe k'irji tace"Bala'i wannan
guy anyi masifafe irin sune suke rigima da matayen su akan 'yaya gaskiya yana do son "yaya
tab!!!!!!!
Girgiza kaina nayi ina tunanin abunda zanyi na huce takaicin abunda guy nan yake min aka
'yar Mimi wai ni yake kira da mayya lallai duniya. Ji nayi wasu hawaye na kokarin zubo min.
Cikin zuciya ta nace zaka cigaba da kirana da wannan sunan indai akan baby ne. Nafi maye ma
maita! Umma taji dadin ganin baby sosai ta karbe ta ta rungume ta sosai a jikinta tana kallon Munnu
tace"Ki bar min ita ta kwana a gurina gobe sai ki zo ki dauke ta ki kaita can gidan NAKU."
Munnu tace"To Shikkenan, haka tayi mana sallama cike da jin kunyar Umma.
****
Amjad Kuwa bayan futar Su Asma'u ne ya kira wayar granny domin ya ji gwalatun babyn shi
dama baya minti ashirin bai kira waya ba, kawai granny tace masa wai su Asma'u sun zu sun
tafi da ita, a lokacin ji yayi kamar ya bar Abunda yake yi ya dira najeria ya yaga yarinyar
saboda rashin zuciyarta har granny ma sai da ta fuskanci b'acin ransa dama ta saba indai akan
baby ne rufe ido yake yayi kamar bai San mutum ba shiyasa Iyami take takatsatsan dashi,
kashe wayarta tayi ta k'yale shi shine fa ya kira Asma'u a waya ya sauke mata rashin mutumci,
ya Riga ya saba da baby kullum kafin yayi bacci sai sunyi hira Sam bai ji dadin wannan Abu ba,
Dan dai kawai yana ganin mutumcin Mutumin ne.
****
Kwata kwata na mance da rashin mutumcin da guy yayi min, hidimar baby kawai nake yi yini
Abu daya. Don har gidan aunt Hauwa mukaje da ita wai lallai sai na bar mata ita naje bazan iya
ba. Ko sallama banyi mata ba na futo daga gidan.
Misalin goma na dare na gama lallab'ata tayi bacci na bude data muna hira da Mujahid, kira ya
shigo wayata, ina dubawa naga numbar k'asar waje ne sai nayi mamakin waye zai kirani da
wannan numbar ne. Cikin sanyin murya nayi sallama, nashi b'angaran yaji wani irin fad'uwar
gaba jin muryar ta da alamun bacci ta kashe masa jiki, gyaran murya yayi yana kokarin dai-dai
ta nutsuwar shi, yace." Ki duba na miki magana ta whstsap ki bani amsa yanzu."! D'iff! Ya kashe
wayar mik'ewa zaune nayi da sauri ina kara duba numbar, tabbas shine domin numbar irin ta
d'azu ce da ya kira lokacin muna a dai-dai sahu. Messages na fara dubawa Aikuwa na ga nashi
can k'asa, ni ban ma San sanda ya shigo ba, girgiza kaina nayi kawai na bude ina dubawa.
_Ki turo min numbar wannan k'awar taki ina so muyi hira da Sweetheart_
Abunda ya rubuta kenan. Na karanta ya Kai sau goma da gayya na kashe data ta ganin yana
online nasan ni yake jira. Cikin rashin sa'a kuma Jahid ya kirani a waya ganin na rufe data
yace." Ko bace zakiyi ne naga kin rufe data gashi ni kuma ban gaji Da jin muryar ki ba."
Nace"Nima haka my Jahid muyi hira mai dad'i aikuwa muka dinga hiraramu ta soyayya
Amjad nashi b'angaran yana sauraron yaga ta turo masa da numbar Munnu kawai sai yaga ta
rufe data kuma gashi ta ga sakon bashi,ranshi a b'ace " ya fara kiran wayar ta a karo na biyu .
wayar taki tafiya sai ace masa busy ya kira ya kai sau goma busy jifar da wayar yayi kan bed
din da yake kwance yana Jan wani mutsiyacin tsaki tare da mamaki dawa take yin waya tsawon
wannan lokacin..........................
*28/11/2019*
[11/29, 9:22 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*
*67*
Mun fi rabin awa muna hira da Jahid a waya sannan yayi min sallama tare da fad'in"My Wife
insha Allah, kiyi bacci mai dad'i kuma kiyi mafarkin kina gidana da yardar Allah." Cike da kulawa
nace"Insha Allah Jahid zan kwana mana addu'a ni da kai." Sosai yaji dadin kalamai na cike da
farin ciki ya kashe wayar......Mik'ewa nayi nima na futa domin wani irin futsari ne ya kulle min
Mara, tsakar gidan shuru Umma ta juma da yin bacci, ina dawo wa na tadda baby ta farka tana
cilla k'afafu daukar ta nayi da sauri don kar tayi min kuka, ruwa na fara bata sha ina kokarin
bata madarar ta naga ta zura k'aramin ya tsanta a baki tana tsotsa bacci ya dauke ta, ajiyar
zuciya na sauke na gyara mata kwanciya na kwanta kusa da ita, bacci ya soma fizgata naji
shigowar kira waya ta na manta ban kashe ba, idona a lumshe na dauki wayar ina dubawa tsaki
naja kamar in kashe wayar sai kuma wata zuciyar tace dauki kiji me zai miki." "Hello." Abunda
na fada kenan kamar me ciwon baki,, sama-sama naji shi yana fadin"Ke ni kika rainawa hankali
na miki magana kin share ni, kuma na kira wayar ki kina waya Lokaci mai tsayi! Nace "Ki turo
min numbar Munnubiya ko." Kamar wani Ubana haka yake min magana da masifa! Cikin sigar
kuntatawa nace"Ni fa duk ka dame da wani surutun ka, bani da numbar Munnu ko ina da ita ma
bazan bayar ba, ba dai a kan 'yar kake min wannan hayaniyar ba Tom sha kurumin ka baby
Aysha na gurina yanzu ma ta farka daga bacci na bata ruwa tasha, ka cigaba da kirana mayya
a kanta wallahi dad'i nake ji, maganar da wa nake waya bai dame ka ba, mutum na son yayi
bacci an dame shi."!! Kashe wayar nayi gaba ki d'ayan ta, wani irin sanyi naji cikin zuciyata na
mayar masa da Martani Nasan yau da kyar in zai iya bacci.
Aikuwa sakato yayi da waya a hannu yana kallon abun kamar almara baby Aysha na hannun
Asma'u wato duk kauce kaucen sa yarinyar nan sai da taje ta dauko mata sweetheart, yasan
halin Asma'u farin sani bata munafurci yasan da gaske take, shifa yanzu babu wacce yake jin
haushi sai granny domin yana ganin itace ta bada fuskar a dauko masa 'yar sa, da kyar bacci ya
dauke shi yana tunanin maganganun da Asma'u ta dankara masa. Abunda yafi tsaya masa a
ransa shine tunanin da wa take waya, yasan dai idan da 'yar uwarta mace take waya baza su
kai kusan a wa guda ba, wata zuciyar tace masa ko Mujahid ne? Take ya yardar wa zuciyar sa
shi din ne....... Cike da tunani. Ta da mafarkin sweetheart d'insa yayi bacci. Ko da safe ma da ya
tashi babu kuzari a jikinsa har abokansa suka gane, nan yace musu baya jin dad'i ne kawai, yini
yayi a kwance yana kewar gwalantun baby kuma yayi alk'awarin bazai k'ara kiranta a waya ba
balle ta kara fada masa magana shifa Yanzu neman hanyar da zai yi nesa da ita yake saboda
alak'arsu da Mujahid.
Da safe da kyar baby Aysha ta yarda da Umma lokacin da zan tafi skull ma sai Goya ta Umma
tayi ta shige da ita daki don kar taga futata ko gilmawa ta ta gani zata fara zillo idan kuwa ban
dauketa ba sai ta sanya kuka.
Koda muka had'u da Munnu a skull cewa tayi wai kunyar Umma take ji baza ta iya zuwa ta
dauki baby ba, sai nace ta bari zan kawo ta insha Allahu. Bayan sallahr la'asar na fito tsaf dani
baby na bayan Umma a goye ta sauko ta, ina kokarin sab'ata a kafad'a Umma tace"Ki Goya ta
akwai sanyi- sanyi hadarin nan ya zama sanyi, towel din na karba na Goya ta sosai na saki
hijab kana nayi wa Umma sallama, gidan su Munnu na nufa kai tsaye.
*****
Ummansu Munnu tayi farin ciki sosai ta karb'i baby ta goya ta tam a bayan ta har sai da tayi
bacci ta tashi sannan ta sakko da ita, tace " Ya kamata a gwada bata abunci fa." Dariya nayi
nace"Ta isa cin abunci yanzu."? Tace"Bari ki gani." Wake ta Mirza ta sanya mata a baki Aikuwa
baby ta lamushe ni da Munnu muka dinga dariya, Ummansu Munnu tace"Yaran yanzu da
wayon su ake haifar su, gashi dai daga laluba mata wake ta lamushe, haka Ummansu Munnu
tayi mata kusan sau biyar sannan ta k'yaleta ta bata ruwa, kuma Allah ya taimaka bata yi kuka
ba, sai bayan magariba Babansu Munnu ya dawo gida, ya dauki baby Aysha yayi mata addu'a
hade da sanya mata albarka yayi mata addu'a sosai da sosai kana ya sanya k'aramin yaron shi
yaje kanti yayi mata siyayya sosai kalolin biscuits iri-iri Ummansu Munnu tayi ta dariya tana
fad'in "Irin wannan siyayar akai wa kishiyata alhalin gani a zaune ba'a min ba, dadin abun dai
cin abunci ma ni na koya mata." Baban su Munnu yace." Da kin sani Baki koya mata ba ai."
Mudai dariya kurrum muke musu, hira muke da Munnu sosai wacce ta dauke min hankalina sai
da Ummansu Munnu ta leko dakin tana fad'in "Asma'u ko anan zaki kwana ne ga hadari nan
yana had'owa." Agogo na kallah da sauri naga tara shaura da sauri na mike INA fad'in "A'a
wallahi Yanzu zan tafi." Baby na dauke wacce ta Dade da yin bacci na Goya ta da sauri na zura
hijab na fito wani bakin hadari na gani a gabas Nace"Munnu Allah ya kiyaye ni da dukan ruwa."
Tace "ameen dai amma ni shawara ta ki bari sai gobe kawai kya tafi." Ko kallonta banyi ba nayi
hanyar futa ina sallama da Ummansu dake Uwar daki.
Ina