Showing 36001 words to 39000 words out of 95753 words
Chapter 13 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
min hira. Mamakin ta kawai nake, nace ta kashe waya ta
kashe babu kara bare tayi min magiya kan in karb'i wayar kamar yanda ya bukata, lokotan baya
idan taga ina mishi wulakanci haushi take ji amma banda yanzu. Kwanciya nayi gefan ta ina
lumshe idona sama-sama naji muryar narse na shigo tana tashina, na bude idona Wanda suke
cike da bacci ina kokarin mik'ewa zaune.
Mimi tace" Ki k'yaleta mu kwana tare domin ko a gidama a tare muke kwana." Nurse ta futa
bata kara magana, sama-sama muke yin hira da Mimi bacci yaci karfina ban San sanda ya
kwashe ni ba.
Shida shaura na Safiya na tashi lokacin har masu bada magani sun shigo dakin sun bawa
Mimi wacce take zaune dungurgur taki yin bacci saboda tsabar farin ciki, mik'ewa nayi ina
hamma idona cike da bacci nace." Mimi shine baki tashe ni ba ko? Kinga na rasa sallah
asubah."
Murmushi tayi tare da fadin "Asma'u naga a gajiye kike gashi kince bacci kike ji shiyasa na
kyaleki kiyi hakuri." K'wafa nayi kawai na sauka daga gado toilet din dake cikin dakin na shiga.
K'arfe takwas dai-dai likita ya shigo ya gama aune-aunen sa kan Mimi kuma yaji dad'i da ya
duba yaga yanda ta kwantar da hankalin ta, nan ya rubuta sallama hade da kara tausar Mimi
sosai kan ta kiyaye ta daina saka damuwa a ranta. Nima kuma yace." Mu dinga sanya ido
ankata sosai muna guje b'acin ranta.
9:00 am mun futo daga asibiti da bamu shigo da kaya komai ba amma zamu futa dasu
niki-niki a hannu muna futa harabar asibitin wata shirgegiyar motar *Siyana* mai dauke da
tambarin *A&A mai nasara* sabuwa dal! Ta shigo gurin, Dravar shi ne ya futo da sauri muka
hada ido dashi. Saurin kauda kaina nayi daga kansa
Ya k'araso gurimu hade da zubewa gaban Umma yana gaishe ta ta amsa a sake, Ummansu
Munnu ma ta amsa ita da aunty Hauwa, sai ya mike hankalinsa na kaina yace." Ranki ya Dade
oga ne yace in zo in kaiku gida."
Cikin zuciyata nace shi kuma ko wa ya fada masa anyi sallama oho! Shiru nayi masa, aunt
hauwa naji tana fadin"Aikuwa mungode dama yanzu muke tunanin a dai-dai ta nawa zamuyi
damu da kayan mu." Na muka nufi motar kowa na fadin albarka cin bakinsa.
Duk yawan mu damu da kayanmu motar sai da ta dauke mu, hat guri Yayi saura doh-doh
yaja motar muka tafi gida, Mimi ta sake sosai ina jinsu suna hira da Munnu ban tanka musu ba.
Goma shaura muka Isa gida Har ya danyi kura saboda rashin mutane a gidan kwana biyu
kawai, ni da Aunt Hauwa muka fara aiki Ummi da Mimi kuwa na rumfa daga inda muke muna jin
yanda Umma take rarrashin Mimi da kalamai Masu dad'i da kwantar da hankali.
******
Yau Kwana ki biyar kenan da bud'e sabon company me zaman kansa a jahar kano company
*A&A mainasara* ya amsa sunansa sosai ya samu daukaka domin an fara gudanar da harkoki
yanda ya kamata kullum a cike yake da baki daga garuruwa daban-daban sun shigo d'aukar
kaya. Hakanan Sauran company sa na waje suma komai ya kammala harkoki ake sosai da sosai
Allah ya shiga al'amarin.
Sanye yake da wani yadi mai masifaffan kyau da tsada ni kam sai ince ma a jikinsa na tab'a
ganinsa milk coulor ne mai sharashara anyi masa dinki boda yayi amfani da singlet black kana
ganin shatin ta, bai sanya hula ba taje lafiyayyar sumar sa yayi wace take bakkirin sai shek'i
take, ya gyara sajan sa kamar ko da yaushe ya feshe jikinsa da turaran shi na ko da yaushe,
takalmi mai gidan ya tsa ya sanya a fararen k'afafun shi, blck ne sunyi masa kyau ba kad'an ba,
hannunsa daure da agogon shi, na zallar fata fad'ar kudin shi ma b'ata wa ne, komai na Amjadu
colour ne domin bai fiye amfani da Abu gama gari ba.
A nutse ya futo hannunshi rike da wayoyin shi, kana kallonsa zaka fuskanci akwai damuwa a
tattare dashi Dan dai jarumin namiji ne me b'oye damuwar sa. Harabar gidan ya futa, Doh-doh
da Rambow suna tsaye kamar dogarai suna ganinshi ya futo Rambo ya nufi inda yake shi kuma
doh-doh ya fara kokarin futo da mota.
Wayoyinsa ya karb'a yana yi masa barka fa futowa a dakile ya amsa masa ya wuce shi kuma
ya bi bayan sa, motar ya bude masa ya shiga ya zauna shi kuma ya zaga ya gurin zaman shi,
motar ta futa daga gidan.
Sai da sukayi nisa sosai Doh-doh yace." Oga ina muka nufa."? Zaman shi ya gyara tare da
Dan ya mutse fuskarsa yace." Muje gidan granny ko." Doh-doh yace." Angama sir."
Wayarsa guda ya karb'a gurin Rambo ya fara laluben numbar jiya yaji mugun haushi
abunda tayi masa ta sanya Mimi ta kashe masa wayar wato bata buk'atar tayi magana dashi
abunda yarinyar take ya soma b'ata masa rai, Sam bai saba ganin wannan shariyar ba a gurin
'yan matan da suke son shi, amma yana ganin dole zai rage zak'ewa a kanta ko zata gane
muhumamcin sa.
Cikin ikon Allah da ya kira wayar itace ta dauka muryarsa shi a cunkushe ya amsa mata
sallama minti biyu tsakani yace." Kina jina ko."?
"Umm." Abunda tace kenan. Yace." Munyi waya da dector d'azu an baku sallama shine na turo
Doh-doh ya dauke ku a mota babu wata matsala ko."?
"Ummm."! Nace. Haushin yanda take masa yaji Umm da Umm sai kace wata kurma, k'aramin
tsaki yaja yace." Yanzu zanje in dauko granny zata zo ta duba Momyna."
Sama-sama nace"Sai tazo." Kafin na an kara ya kashe wayar a fusace.! Tab'e bakina nayi nace
"Kai ka sani kuma.
Umma na fad'awa zuwan kakar shi ta tashi ya fara shiri aunt Hauwa na shirin tafiya gida
Umma ta hana ta wai ta tsaya su tab'i bak'uwa sosai a ka gyara gidan duk a ka kauda
kayayyakin sana'ar Umma dasu ke rumfar tamu kamar su kalazinr galan din mai robibin magi
da su d'aurikan busassan kayan miya rumfar tayi tas da ita Umma ta shimfid'a tabarma ta zauna
jiran zuwan su.
Wani irin kamshi ne ya bugi hancin mu kafin muji muryar dattijiwar matar cike da nutsuwa da
kamala tayi sallama.
Umma ta amsa mata tare da fadin"Sannu da zuwa maraba lale shigo ciki Hajiya."
Granny ta shiga ta zauna kan tabarma fuskarta cike da farin ciki da annushuwa, suka gaisa da
Umma cikin mutumci, aunt Hauwa ta gaishe ta hade da dauko mata Lemo mai sanyi hade da
ruwan roba Wanda aka siyo mata shi mussaman, Granny ta bude ruwan tasha tayi hamdala,
sannan ta kalli Umma cikin barkwanci tace. " Nazo duba kishiyoyina ne, kafin a Kai min su mu
fafata da juna."
Dariya Umma tayi tace." Aikuwa dai, dole suyi miki ladabi domin shi kanshi uban gayyar da
bazar ki yake taka rawa ba a raba hanta da jini kuma da tsohuwar Zuma ake magani."
Dariya Granny ta sanya tace." Ai ya juya min baya kwana biyu baya ta tawa kullum bashi da
zance sai na kishiyoyina kin ga kuwa dole inyi kishinsu." Umma tace"In ya gama d'akinsa ai
dolen sa ya dawo gurin ki." Dariya suka yi a tare aunt Hauwa ta mike tare da fadin "Bari a kira
miki su Ku gaisa wai kunyar ki suke ji."
Granny tace." Wane irin kunya? Suna jin dai tsoron su hada ido dani tun kafin su shiga humm
zasu aure min miji ai dole su b'oye je ki kira wo mun su." Aunt Hauwa ta futa tana Dariya tare da
mamakin halin grnay kamar sun saba mata Mai fuska da fara'a gaskiya tana da kirki.
Tun lokacin da naji sallamar matar gabana yake fad'uwa har yanzu narasa ko ta menene aunt
ta shigo tare da fadin "Sai kuzo Ku gaisa da ita ko." Mimi tayi s'aurin mikewa tana gyara hijab
dinta ko jira na bata yi ba tabi bayan aunt Hauwa cike da mamaki nake bin ta da kallo ina
mugun mamakin azarb'ab'inta da rashin kawaici lallai Allah mai mutane sai ga mutum yana Abu
shi a ganinsa ba komai bane.
Muryar Umma naji tana k'wala min kira na amsa da sauri na dauki zurmemam hijabi na
sanya na futa da sauri Mimi na zaune kusa da ita sai faman sunkuyar da kanta take tana
murmushi nayi sallama granny ta daga kanta tana kallon Asma'u fuskar ka a sake tace" Zo nan
kema ki zauna mu fahimci juna daku domin bana don Ku kwace min mijina."
Babu yabo babu fallasa naje na zauna kusa Da ita kaina a kasa na gaishe ta, ta shafa kaina
tana fadin"Sannu Asma'u d'iyar arziki Allah yayi muku albarka gaba ki d'ayan Ku, Allah ya baku
hakuri. Zama da juna kuyi ta hakuri da Mijinku domin wani irin mutum ne shi muskili kuyi hakuri
da dabiun shi, gaku 'yan gida daya nasan baza a samu wata Matsalar ba ta fannin kishi tunda
'yan uwan junane Ku, Ku rike junanku da amana kunji ko Allah yayi muku albarka."
*12/November/2019*
[11/13, 7:59 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA
CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO
MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA
SAI TA CI SHI*
*50*
Umma tace." Ameen suma ameen Hajiya ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu wata
b'araka da taza faru a tsakaninsu zasu zauna lafiya tunda Allah yasa sun hada miji gasu kuma
'yan juna, komai zai zo da sauki. "
Granny tace." Masha Allahu to Allah ya tabbatar mana da alkairinsa, hira tsakanin Umma da
granny ta mik'a sosai ba tare da sun gane ba, ni bar dakin cike da kunya, Sai ga Mimi ta biyo
bayana kwanciya tayi kusa dani hade da lumshe idonta, murmushi nayi ina kallonta cikin
tsokana nace." Mimi amaryar Amjadu Alherin Allah."
Bude idonta tayi tana kallonta fuskarta dauke da murmushi nace." Ko ba haka bane."? Girgiza
kanta tayi tare da fadin." Ni amarya ke kuma Uwar gida ko."? Nace." A ina na zama Uwar gida
ke amarya kuma ke Uwar gida. " mik'ewa zaune tayi ta rike hannuna tare da fadin "Yanzu
kakarshi take fada cewar k'arfe biyar zai dawo ya dauke ta, wane irin Abu zamu tanadar
masa."?
Nace." Mimi duk abunda kikayi NIYYA ki bashi domin ki faranta masa kuma kinyi dabara
hakan zai k'ara jawo hankalinsa gare ki." Tace." Me zan bashi yanzu."? Dariya na sanya hade
da fad'in "Idan baki da abunda zaki bashi in yazo to ki bashi labari mai dad'i da wannan
sanyayyar muryar taki." Dariya tayi hade da bani hannu muka tafa, haka dai na dinga biye wa
Mimi da duk abunda zata ce min akan Amjadu kuma bana bata shawarar banza.
K'arfe shida shaura kira ya shigo wayar tata lokacin tana band'aki tana wanka, Kin dauka nayi
don na duba naga shine, motsin ta naji bakin rijiya nace"Mimi yi sauri kizo ana kiran waya. "
aikuwa sai gata ta shigo da sauri hannunta na digar ruwa ta karb'i wayar daga hannuna. Kallo
na bita dashi. Wata irin murya da ban Santa da ita ba naji tace." Hello." Daga bashi bangaran
naji muryar shi sama-sama yace."Momyna kuna ina ina ta kiran waya kusan sau biyar babu
wacce ta dauka a cikin Ku." Muryar ta a sanyaye tace." Ni ina wanka ne."
"Asma'u fah."! Yafad'a babu sauki a muryar shi,kallonta tayi sai kuma naji tace." Gatanan. "
yace." Ok kina nufin kice min tana ganin kirana taki d'aukar wayar."? Mimi shiru tayi taki bashi
amsa. Shurun da Mimi tayi shi ya tabbatar masa da abunda yake zargi. Tsaki! Yaja yace." Ok ki
fad'awa granny gani Nazo ta futo mu tafi OK." Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayarsa.
Jikinta a sanyaye take kallona nima ita nake kallo nace"Dole ki koyi hakuri fa, kuma kiyi hakuri
da halin shi tunda aure zakuyi ." zama tayi kusa dani tare da fadin"Wai sai ki dinga cewa aure
zamuyi eh aure zamuyi har dake a ciki ai,ko" mik'ewa nayi ina dariya nace." Har dani mana, ni
ai farin cikin ki ne nawa kar ki damu dani." Futa nayi daga dakin ba tare da na saurari abunda
zata ce ba."
Cikin sauri Mimi ta shirya ta futo tana ta zabga kamshi ina zaune kofar kicin ina gyara kayan
miya na bita da kallo sakin fuskata nayi tare da fadin "Kinyi kyau sosai Mimi." Mirmushi tayi ta
shiga Rumfar inda naji grnnay tana sallama da Umma, suka futo a tare Umma sai godiya take
mata, sun kuyar da kaina nayi kasa na cigaba da aikina har tazo kusa dani ta tsaya da
sakskkiyar fuska tace." To ke zan tafi naga sai wani b'uya kike yi ko tsorona kike ji tun kafin ki
shigo kinga 'yar Uwar ki ta saki jikinta mun saba da ita."
Murmushi nayi nace." Ki gaida gida mun gode." 'Yar dariya tayi tare da fad'in"Na ga alama
gudun angon naki kike yi 'yar uwarki tafi ki sonshi." Ni dai ban ce komai ba har suka fuce ita da
Mimi da aunty Hauwa har soro Umma ta raka ta sannan ta dawo cikin gidan.
Yana zaune cikin mota ya hango zuwan su, Mimi yake kallo tun daga nesa taci Uwar kwalliya
abun ya bashi mamaki sosai, yarinyar Da jiya I Yanzu take kwance magashiyan rai a hannun
Allah, amma dubi kamar ba ita ba, abunda bai sani ba shine tunda Mimi taji labarin auransu zai
yi wu dashi da ita ta watsake tamkar bata tab'a cuta ba, har suka k'araso gurinsa yana mamakin
wannan abu .
Murmushi mai k'ayatar wa take sakar masa, Wanda Sam hankalinsa baya kanta yana can gurin
Granny wacce take kokarin shiga mota sai mita take masa, yace." Idan zaman gidan ne bai ishe
ki ba sai ki koma ai ban ce miki dole ba." Tana daga cikin motar take fadin"Wallahi karshen
zamana a wancan gidan yazo domin baza ka aje ni ba sai kace mayya ni daya gida kullum kana
gidin matan ka, nima gidan naka Zan dawo ." dariya yasa yana kokarin futowa daga motar
yace." Sa ido ne zai kawo ki gidana bana Neman ki." Bude motar yayi ya futa yana jinta tana
surutai ya shareta
Fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Mimi yace." Momyna jiki yayi kyau gashi har anyi
min kwalliya mai kyau da burgewa." Mimi ta rufe fuskarta cike da kunya, yace." Kinyi kyau sosai
zan so in ta kallon fuskar ki, sai dai Dole zan bar gurin nan saboda idon Jama'a ina fata babu
wata matsala ko."? Cike da shauki Mimi tace." Babu wata matsala dama ji nayi zuciyata baza ta
iya nutsuwa ba dole sai ta ganka." Murmushi yayi hade da Sosa kansa yace." Momyna kenan
nagode sosai da wannan kaunar ina alfahari dake."
Mimi ta dinga jin dad'i a zuciyarta yau gata ga masoyinta Amjadu Sam bata so yayi mata
sallama ba, taso suyi ta tsayuwa a gurin tana kallon kyakyawar fuskar shi.
Sai dai motar tayi nisa har ta daina ganinta sannan ta bar gurin cike da nishadi.
*****
Labarin auran *Amjadu Young millionaire* ya baza garin kano da ka bude redio zan can kenan
Young millionaire zai yi aure a Sati biyu masu zuwa inda zai auri 'yan gida daya ya da k'anwa
jama'ar gari na mamakin wannan Abu, masu bin kwakwkwafi kuwa sai da suka bunkito ko su
waye 'yan matan da zai aura hade da bunkice 'yayan wane mai kud'in ne ko kuma mai mulki a
jahar kano da sauran garuruwa.
Abun mamaki surutun jama'ar gari sai ya karu wannan gayawa wannan 'yan matan da *Amjadu
Young millionaire* yake nema da aure 'yayan talakawa ne tilis d'aya ubanta ma ba'asan inda
yake ba tun tana jaririya ya gudu ya barta ana zargin ma 'yar shege ce bayan yayi cikin ta ya
gudu daga gari, ita kuma d'ayan ubanta ma'aikacin company ne na madara dake Sharada ya
mutu bashi da ko kwabo bashi da famsho balle garatuti ya mutu bashi da gidan kansa,sai a
company da yayi wa aiki ne suka bar mishi gidan da suka bashi a ro saboda iyalinsa, Duk ana
zargin'yan matan da zai aura 'yayan mace ne." Duk cikin jarida ta gaskiya dokin k'arfe Amjadu
ya karanta wannan labarin. Zufa ce kawai take keto masa ko ta Ina, wani irin kira ya kwalawa
Rambo sai gashi ya shigo farlor da sauri. Jaridar ya mik'a masa muryar shi a sama yace."Kuna
ina haka ta faru. "!! ? Rambo ya karb'i Jaridar yana dubawa hannunshi sai rawa yake yi, shima
abunda ya gani ya tsorata shi, yasan makiyan sa ne suka shirya wannan Abu domin su tozarta
shi, Yace." Sir ka kwantar da