Showing 6001 words to 9000 words out of 95753 words
Chapter 3 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
abun na manya ne, Mimi Allah ya dubi maraicin ki, idan kika shiga gidan nan
kar ki manta damu don Allah."
Cike da mamaki nake kallon su, ina mamakin son kud'in su lallai a duniya idan kayi kudi ka
wuce komai Mimi tun kafin ta shiga gidan sun fara magiya.. Kallonsu kawai nake suna zolayar
Mimi ita kuma tana wani sinne kai, cikin zuciyata nace "Kin had'u da aiki babba Mimi.
*********
K'arfe goma da kwata mun fito cikin shiri kamar wasu taurari Munnu nan tazo mu tafi tare,
munyi bala'in kyau mussaman ma ni suffa da b'oyayyan kyau na yau sun futo a zahiri saboda
abunda bana yi shi nayi wato kwalliyar fuska, kamar wata Queen haka na zama muna sanye
da material dinmu Wanda aka yi mana dinki duguwar Riga mai tattara daga baya daga gaba
kuma yayi sama anyi masa wani irin yanke gege da gefe dogon hannu ne yayin da rigar ta
kasan pitat gown ne gaba d'aya rigar take tayi matse ni tam!! Nishi ma da k'yar nake, gani da
manya breast da uban hifs Sai da na sanya yari da sark'a na sannan na kalli mudubi, ni kaina
nasan nayi kyau sosai, Munnu da Mimi suka saki baki suna kallona, nace" Meye wai!? Munnu
tace." Anya baza ki cire kayan kuwa ba kinga yanda suka matse ki, ke gaki tubar kallah." Nace"
lallai Munnu wallahi ko Umma yau baza ta hanani futa da kayan nan ba.Mimi tace" sai ki sanya
hijabi idan muka je can ka cire,amma dai kin San gurin ya hada samari da 'yan mata duk
budurwar da take da saurayi zata gayyace shi yazo gurin." Nace" Mimi ina ruwana wai don
Allah Ku k'yaleni mana." Ganin raina ya b'aci ya sa suka k'yale ni. Umma na zaune s rumfa tana
kule-kulen ta muka futo takalemu a tsanake tace "kunyi kyau tamkar wasu amare,amma ke
Asma'u meye kika sanya hijabi."?
Nace" Umma dinkin ne ya matsani shine nace"idan na shiga cikin 'yan uwana mata sai in cire."
Tace" haka yayi to Ku kula don Allah Ku tsare mutumcin Ku ana gama taro ku dawo gida kar Ku
tsaya kad'e-kad'e da raye-raye." Muka ce insha Allahu."
Muna shirin futa daga gidan wayar Munnu tayi k'ara ts dauka a nutse tare da kashe muryar ta,
kasa kunne nayi cike da mamaki jin tana ambatar sunan Shamsu. Ni da Mimi muka kalli juna. Ji
mu kayi tana fadin"Eh ka shigo da motar yanzu zamu futo." Sukayi sallama, dukaninmu muka
kalleta cike da mamaki nace"Munnu yaushe Shamsu ya dawo kuka kuma jone wa." Murmushi
tayi tace" shekaran jiya ya dawo da k'arfin sa, Wallahi aurena zai yi domin aranar da ya dawo
ma Baban shi yazo gurin Babanmu baku ga kayan da ya kawo mun ba, wannan hayaniyar da
muke ciki ce ta hana ni fada muku."
Ni da Mimi muka Ce"Toum Allah ya sanya alkairi lallai alk'awarin Allah ya cika. " dariya Munnu
tayi cike da farin ciki muka futa daga gidan. Samari na bakin titi suka bimu da kallo kamar wasu
mayu.
Wata had'adadiyar mota na hango a fake gefan titi Shamsu na zaune a mazaunin dravar tare da
wani Wanda ban gano fuskar shi na, suna sanye da wata masifaffaiyar shadda wagambari hade
da hula damanga sunyi kyau har sun gaji. Ganin zuwan mu gurin yasa Shamsu futowa da sauri
ya bude wa tauratowar shi motar yana fadin" Girman kujerar ki ne." Hararasa nayi tare da tab'e
bakina nace"Haji Shamsu Ashe zaka dawo ai na dauka muma yaudarar tazo kanmu." Dariya
yayi yace." Inaaa!! Baby Asma, Ai Munnubiya ta daban ce cikin mata, tab'e bakina nayi
nace"Allah yasa da gaske kake."
Tunda na fara magana abokin Shamsu yake kallona ina kallonsa ta wutsiyar ido tsaki naja a fili
na tsani kallo wallahi.
Munnu ta shiga ta zauna Mimi ta zauna nima nashiga sannan Shamsu ya koma gurin zaman
shi hade da kunna motar muka tafi.
Shamsu sai janmu da hira yake yana fad'in"Ai duk naji labari lokacin da na tafi har daku ake
cewa dama yaudarar Munnu nake yi humm yanzu Asma baby kina ganin zan aikata haka
kuwa."
Nace"sosai ma kuwa Shamsu namiji ne fa kai hunm halin Ku sai Ku."Abokinshi ya juyo yana
kallona tare da sakin murmushi yace." Baby Asma wasu mazan ne suka bata wasu amma
abokina da gaske yake." Tab'e bakina nayi nace" muna da labarin fa duk 'yan Matan da ya
yaudara sun kai goma. " Shamsu ya rike baki yana dariya tare da fadin" duk sharri ne wallahi,
karya suke min." Mimi tace"Babu sharri nan gaskiya ce mu dai don Allah kar ka kara guduwa
domin wancan karon sai da mukayi jiyyar ta" suka kwashe da dariya shi da abokinsa.
Munnu sai mintsina take wai in daina surutan da nake yi ina jinta na kiyin shiru.
****
Lokacin da muka Isa guri ya soma cika sosai aka kawata gurin gurin malamai daban da iyayen
yara wajan dalibai daban, muma wajan mu daban wajan manyan baki daban .. Masu hotona da
vedio baza su kirgu ba, saboda ko wacce da nata,muma mun dauki namu can muka tadda shi,
MA kad'a sun fi su biyar suna gefe suna jiyar taro ya watse a fara shagali. Ko wane class da
gruop d'insu da kuma irin kalar ankon su, ko wacce tana wace wannan.
Mai girma principal ya bude taro da addu'a tare da yi mana nasiha sannan yayi wa 'yan matan
da aka kusa bikinsu a cikinmu addu'ar zaman lafiya Wanda basu da mazaje Allah ya kawo
musu, hakanan Wanda suke shirin cigaba da karatu Allah ya bada sa'a.
Haka Malamai suka dinga mik'ewa suna jawabi tare da addu'a, taro ya tashi guri ya hautsine
kowa da ta wagar mutanan shi, da kawayen shi sai d'aukar hoto ake hade da vidio,
Ina gefe tare da jama'a ta domin wasu ma ranar na fara ganinsu duk ya wancin su maza ne,
tuni na cire hijabina ina yawo yanda na gadama 'yan ajimu sai jana suke dole sai munyi hoto
duk inda na sanya kafa abokin Shamsu nan yake sauke tasa ya zame min jele, haka na dinga
shiga cikin abokan da samarin 'yan ajinmu muna hoto wasu nayi da waya wasu nayi da Camera
man. Abun mamaki ni kadai jama'a suke ja lallai sai sunyi hoto dani, haka Alina ma duk gabar
da muke da ita sai da tazo ta jani cikin a bokanta maza da mata mukayi hoto wasu daga
cikinsu na fiddo wayoyinsa nayi min.
Mimi ce tazo ta jawo ni da k'arfi tana fadin" meye haka kike yi don Allah ki daina ratsa maza
kina shiga tsakiyar su baki San suba
Fuzge hannu nayi INA fadin "Kinga Mimi yau rana daya ce daga ita babu wata ki k'yaleni." Mimi
ya rabu dani ta koma gurin Munnu da sauraynta
Duk ankon da mukayi sai da muka sanya su Shadda ce karshen sawa. Waiiiii!!! Fitina! Lokacin
Dana futo cikin shadar idanun jama'a kamar ya cinye ni, ni kaina sai bayan na futo a haka
Nazo ina da na sani dinkin fitat ne iya cibiya Sam rigar bata da hannu gashi ta matse ni, siket
din yayi d'an, kwankwaso na kamar zasu yi magana da kyar nake cire k'afa ta saboda yanda ya
matse ni.
Tuni suka yo kaina suna ihu!!! Wani Dj ya saki wak'arnan ta *Hamusu brekar wato shimfidar
fuska* Filin na nufa sauran k'awayenmu suka rufa min baya, rawa sosai na dinga *wakokin
gwanja kamar ni na rera su* mussaman wak'ar shi ta *d'akin bak'uwa dudu bak'ar ashana* ai
ina bala'in son wak'ar nan na zage ina rawa tare da sauran 'yan ajinmu Mimi ma da Munnu sun
shigo filin ana yi da su.
Alina ce tazo ta ja hannuna wai inzo muyi sallama da abokanta, muka nufi bakin get, kamar
walkiya naga gilmawar motar guy nan ta futa daga gurin. Abunda yasa na gane sunan shi dake
bayan motar kuma na shiga cikin kusan sau biyu. Mamaki ne ya kama ni, mutumin da baya gari
me ya kawo shi gurin nan. Sama-sama mukayi sallama dasu na koma ciki ina tab'e bakina.
******
System d'in shi a kan cin yar shi yana dubawa Anthony na gefan shi yana waya cikin yaran na
chana.
Sak'o ne ya shigo yana dubawa yaga rambow ne, pictures ya fara gani kusan guda Dari suna
shigowa, da sauri ya bude yana dubawa, ji yayi zaman gurin ya gagare shi a sabili da abunda
ya gani cikin loptop din shi, babu shiri ya mik'e da sauri ya shige wani had'addan bedroom hade
da sanyawa kofar key ya zauna gefen bed hannu na rawa yake duba hotonan wani irin gum!
Yana tsatstsafo masa a saman goshi
*3/NOVEMBER/2019*
[11/4, 11:56 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*
*39*
Yarinyar yake gani cikin maza ko ta ina, ga sassan jikinta a bud'e ko duk motsin da zata yi kana
ganin saman breast dinta ga sunan a waje hankalinsa bai k'ara Tashi ba sai inda yaga ta shiga
filin rawa tana juyi ana mata watsin kudi, wani uban ihu!! Ya kurma hade da jefar da loptop din
ta fad'i kasa ta gangara can bakin kofa, mike wa yayi a zafafe! Ya kai wa bango duka da
hannunshi!! "Ni wannan yarinyar zata tozar ta. ? Da k'arfi ya fad'i maganar, kaiwa yake yana
kawo wa a dakin, a fusace! Yaje ya dauki wayar sa, yana lalubar Mimi, bugun duniya yayi tak'i
shiga, jefar da wayar yayi ta fad'i kasa, dafe kansa yayi dake mugun sara masa, fuskar guy nan
kawai yake hangowa Wanda yake nanikar yarinyar duk inda ta sanya gaba shine ya fi kowa
zak'ewa, shifa idan ba idonshi ne yayi mishi gizo ba sai yace kamar yaga ya rungume ta, wani
irin ihu ya kurma!!! Hade da sanya hannunsa biyun yana dukan katifar dake kam bed din sai
kace wani mahaukaci, da sauri Anthony ya shigo domin yaji ihu!! Cin karo yayi da lopot bakin
kofa a kife, cike da mamaki ya sunkuya ya dauko ta yana gyarawa, k'araso wa nan ma yaga
wayar sa a jefe.. Ajiye loptp din yayi kusa dashi ya dauki wayar yana dubawa dake mai hade da
batir ce kunna wayar yayi ta kama abunka da abu matsada nan take ta kama.
Zama yayi kusa dashi cikin harshen turanci yake tambayar sa." Dago kamshi Yayi yana
kallonsa da idanunsa Wanda suka kad'a sukayi mugun ja!! Hannu ya mik'a masa alamun ya
bashi wayar, da sauri Anthony ya mik'a masa wayar, Numbar Mimi ya kara kira is switch up,
cikin sauri ya nemo numbar Rambo, bugun farko ya dauka, bai saurari maganar da yake masa
ba, yace." A ina guy nan yake? I wiil kill you!!!." Rambo ya tsorata jin muryar Oban gidan shi, na
wani irin rawa!! Yace. " Sir ban gan..........kafin ya karasa maganar ya katse shi cikin wata irin
razananniyar tsawa yace." Rambo!! Ni kake fad'awa baka gane ba, Dan ubanka me ka turo min
Yanzu."!!! Rambo yace." Sorry sir Wallahi ban San dai a ina yake ba, a tare dai suka zo gurin
cikin mota.... Yace." Kafin safiya ka bunkito min a wani guri ya ke shi Dan gidan uban waye, sai
na kashe shi."!!!!! Rambo yace." An gama sir insha Allah... Katse wayar yayi yana wani irin haki!
Shiko Anthony ya dauka irin mutanan sa Wanda suka sanyo shi a gaba wato abokan a dawar
sa, sai ya dafa kafad'ar sa yana rarrashin sa da kalamai masu sanyi.
Gyad'a kansa kurrum yake yana tunanin irin hukuncin da zai dauka kan yarinyar da shi kanshi
guy...wani irin rad'ad'i da zugi zuciyarsa take masa in da yake jin kamar ya Dora hannu aka yayi
ta kurma ihu ko ya samu sassauci,, cikin maza don rashin nutsuwa ko wane namiji yazo ya jata
kamar tinkiya ta bishi tana murguda masa mazaunai hade da gantsaro masa nonuwa duk Rabin
nonuwan ta a waje da ta d'aga hannu hammata a waje
*Ya ilahi!!* abunda ya fada kenan da mugun k'arfi, Anthony ya mike da sauri gami da bude kofar
dakin ya futa.
Minti biyu ya dawo hannusa rike da wata bak'alar kwalba wani Abu mai kyali a saman ta, bude
wa yayi da sauri ya mik'a masa, cikin harshen turanci yake fadin "karb'i ka sha wannan zaka ji
sassauci a zuciyar ka." Giya ce Anthony yake mik'a masa a zuciyarsa yace." Asma'u bata Isa ta
sashi ya fara shan giyaba ko da zuciyarsa zata yi bundiga sai da ya mutu da bakin cikin ta.
Kauda kansa yayi yak'i karb'a, Anthony ya aje kwalbar giyar da sauri ya Ciro kwalin sigari hade
da leghtar ya kunna guda ya mik'a masa, aikuwa da sauri ya karb'a ya fara bata huta, duk guda
zuk'a biyu yake mata ya shanye, tas!! Ya shanye kwali guda Anthony ya mike da sauri ya futa
domin dauka masa wata, shi zufa kawai yake lokaci guda yaji wani irin sanyi-sanyi a jikinshi
alamun zazzab'i ya kama shi. Kwanciya yayi rigingine kan bed din yana sak'e-sak'e cikin
zuciyarsa
*********
Kwata-kwataKwata-kwata ma ni mantawa nayi da naga Rambo cikin jama'a na koma muka
cigaba da sabgar mu, har lokacin da taro ya watse.
Ana kiran sallahr Magariba muka shiga gida, nida Mimi Yaya Aminu da Umma na tsaye da
alama magana suke, kafin in an kara naji duka ko ta ina!! Ihu! Na kurma ina fadin "Yaya Aminu
me nayi maka kake dukana." Fad'i yake "Asma'u gwara in kashe kan inga abun kunyar da kike
k'okarin jawo mana banje gurin party Ku ba, amma ina da labarin dukanin abunda ya faru so
kike ki futa zakka a jikinmu Asma'u Ashe 'yar iska ce ke ban sani ba,."!!! Ya k'arashe maganar
cikin tsananin b'acin rai!
Umma naga tayi shigewar ta daki ranta a bace babu abunda tace kan irin dukan da yake min,
kuka na fashe dashi INA fadin" wallahi Allah ba zai barka ba sai ya saka mi... Wani irin mari ya
galla min tare da fadin" a gidan uwarki sai ya hau dukana da kafafunsa ina karewa tare da fashe
wa da kuka. Mimi na tsaye tana kallonmu daman abunda take guda kenan shiyasa tun farko ta hanani, ganin
yanda yaya Aminu yake dukana ne yasa Mimi shahada taje ta rungume ni sosai itama tana
kuka tana tayani bashi hakuri, amma saboda rashin imani na Aminu ko kallonmu baiyi ba ya
dinga duka yana fadin "Ai dama bakinku daya, wato ke mai tausayi ko? Asma'u zata Kai ki ta
baro.!!! Sai da yayi mana lilis sannan ya kyalemu.
Da Jan jiki muka shiga dakinmu ko wacce tana shararar hawaye Mimi tace" Tun farko abunda
na hango kenan, amma da yake kedin me taurin kan tsiyace kika ji, kika dinga shiga cikin maza
saboda rashin kamun kai, wallahi Kiyi wa kanki fad.... Katse ta nayi a fusace.! Nace"Mimi kiyi
min shiru ki k'yaleni inji da guda d'aya mana.""" Itama a fusace! Tace"bazan k'yale ki ba Wallahi
ai dama gaskiya ce bakya so sai kije kiyi tayi." Mik'ewa tayi ranta a bace ta fara cire kayan
jikinta.
Ni ko zama nayi ina duba jikina inda Ya Aminu ya FASA min wani gurin ma har fatar ta kwailaye
gefan bakina ya fashe hannu na NASA na shafo jinin , a fili nace " Allah ya Isa Wallahi bazan
tab'a YAFE wa, duk abunda nayi ai ba akaina farau ba, ballanta na ma banyi komai ba tunda dai
ba kamani a kayi gidan karuwai ba ina zina ko ina cacah,tsabar mugunta da rashin tsoron Allah
yayi mutum yawo aikin banza da wofi"!! Da k'arfi na karasa maganar domin ya Aminu yaji na
dauka yana gidan, Umma ce ta d'aga labulen dakin tace" Yayi miki kyau! Asma'u wuyan ki ya
Isa yanka kiyi ba dai-dai ba kice baza'ayi miki fada ba, lallai kin cika, kuma kin kai munzali
Yanzu kin kara tabbatar min da cewar aure kike so bari gobe tayi da kaina zai wanke kafafuna
naje gidan Kawun Ku Yunusa muyi magana gwara in aurar dake tun kafin ki jawo min abun
kunya."
Da sauri na mike na Isa gurin hade da rike mata kakafu ina kuka tare da bata hakuri ina
fadin"Umma wai me akace muku nayi a gurun party nan ne, Umma ki lura dani wallahi bazan
tab'a zubar da mutumci na ba da kima ta ta 'ya mace, Umma ki yafe min kina kallon yanda Ya
Aminu yake duka na kamar zai kashe ni." Umma ta fuzge k'afafunta ta futa daga dakin ba tare
da tace komai ba
Bakin kofar na zauna ina kuka Mimi tazo ta tsaya a kaina tare da fadin "Bani waya ta,aikin
kawai kin karar min da chaji a banza da hotunan ki, kin San ba wuta ake kawo wa ba"Wani irin
kallo nayi mata ina gyad'a kai cike da takaici nace" Ki duba wayar ki cikin jakata gata can a
tsakar gida. " tsallake ni tayi ta futa, daga dakin. Chaji taje ta kai domin bai zama lallai su kawo mana wuta ba,
Ranar ko abuncin dare hanci ba, haka na kwana da cikina tsabar bakin ciki ya hanani bacci sai
juyi nake.
*****
Kamar yanda ta kwana tana juyi to shima haka ya kwana yana murk'ususu zuciyarsa Sam!
Babu dad'i ga uban zazzab'i da ya kwana dashi, ko da asubah ma a daddafe yayi sallah Yana
jira gari ya waye musu a can , time din ko wace k'asa daban yake
K'arfe Biyar na asubah mun tashi Ya Aminu ne ya tsaya a kanmu har sai da yaga ko wacce