Showing 87001 words to 90000 words out of 95753 words
Chapter 30 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf
futowa titi aka fara wata irin iska mai k'arfi abubuwan hawa sai gudu suke akan titi duk
yawanci motocin gida ne da kyar na samu a d'an sahu Wanda ya rage mutum d'aya a ciki na
shiga aikuwa kamar almara ruwa ya kece kamar da bakin kwarya,ni da nake gefe ruwa ya fara
duka na, kafin kice me na jike jagab, ta karewa nayi ina tsoran kar ruwa ya taba baby sai ta fara
motsi tana k'ananun kuka, gaba na ya fad'i jijjigata nake yi INA so tayi shiru yarinya kamar
wacce ake zugawa ga feshin ruwa sai dukan fuskata yake, kamar zanyi kuka nace "Don Allah
kayi sauri babyna na Kuka."! Mai dai-dai ta yace." Hajiya ai ina ganin parking ma zanyi saboda
ban San iya inda ruwan zai tsaya ba, domin karfinsa yayi yawa sai ya tsagaita sai mu tafi." Kafin
ince komai ya tsayar da 'Dan sahunsa, nace"Na shiga uku ni Asma'u nayi da na sani tawowa da
na hak'ura na zauna na kwana gidansu Munnu zai fi min, tausayin baby nake ji jin yadda take
sakin ajiyar zuciya tana baya sai kyarmar sanyi jikinta yake yi, ni da ita duk mun jike matan dake
a dai dai ta na kalla naga sai hirarasu suke yi babu abunda ya dame su, su kadai ne single
babu wacce take da yaro Karami balle tayi fargaba. Sai da aka dauki 30minutes ana ruwa mai
k'arfi sannan ya tsagaita sai wata irin iskar sanyi ta soma kadawa, a lokacin naji Baby ya fara
atishawa sakkota nayi ina duba jikinta, naga jagab duk da dabarun da nayi mata sai da ta Nike
hatta da gashin kanta, kuka take so tayi ta kasa sai sakin atishawa take, hawaye na fara
sharewa kana na rungume ta tsam! A jikina Ina fadin"Duk nice na jawo miki babyna."!
Jagab! Muka shiga gida muna d'igar ruwa Umma na gani cikin ruwa ta dinga min fada "Shin
baza ki bari gobe idan Allah ya kaimu kya dawo ba, ko kuwa gidan su Munnu din bak'on ki ne.?
Ko tausayin k'aramar yarinya bakya ji sai kinje kin kwaso mata mura da da tari ko." Fada sosai
Umma take min, ni kam hankalina na gurin baby wacce take ta motsi majina har ta fara zurara a
hancin ta, kayan jikinta na cire mata da sauri na sanya mata Pampers na sanya mata kayan
sanyi masu kauri kudindine ta nayi. Umma tace"Bani itanan mu gani." Mik'a mata ita nayi, ina
tsaye da jikakkun kaya ban damu da In cire su ba, duk da nima hakan take kamar baby kwata
kwata bana son dukan ruwan sama Shikkenan zazzab'i da mura zai kama ni. Robb Umma ta
dinga Mirza mata k'irjinta da bayan kunnen ta, da tafin kafarta sannan ta Goya ta.
Futa nayi jikina duk babu kwari, har yanzu da ragowar ruwa kadan kadan yake sauka d'akinta
na shiga na kwabe kayan jikina pant fa breziyya ta duk sun jiki jagab suma sai da na sanya
sabbi, sannan na dawo rumfar Umma na shafa Robb din duk jikina, can k"uryan dakin ta na
shige na k'udindina jikina ina jin shigar zazzab'i. Sama sama naji muryar Umma tana fadin
"Yarinyar nan zazzab'i ya kamata ga k'irjinta yana harbawa duk da cewa dare bai yi ba sosai ki
kira Mujahid a waya yazo ya kawo mata magani duk ke kika jawo mata." Futowa nayi jikina
lullub'e da zanin gadon Umma saboda sanyi da nake ji nace"Umma har dani za'a kawo wa
magani domin nima zazzab'i har ya rufe ni wallahi." Umma tace." Ai kema kin San kanki
ganganci ne kawai." Handbag dina dake yashe a gefe INA dauka ina kokarin fito da wayar naji
duk abunda ke ciki ya jike har wayar, na dauko ina gogewa abunka da babban Abu ina
kunnawa ta kama, numbar Mujahid na fara kira... Ya dauka a nutse muka gaisa na fada masa
halin da ake ciki. Take yace gashinan zuwa. Kashe wayar nayi na mike har zan shiga daki na
dawo ina lekan fuskar baby dake bacci a bayan Umma kanta na taba da hannuna naji zafi
rad'au! Gefan Umma na zauna zuciyata duk babu dad'i Jahid kawai nake jira ya zo. Cikin daran
Mujahid ya kawo mana magunguna ya fada min yanda zan bata, Cikin ikon Allah da na bata
maganin zazzab'in tsakanin 15mintus zuwa 20minuts zazzab'in ya sauka sai dai majinar da
take zuba har yanzu. Maganin na kwanta baby kam a gurin Umma ta kwana domin tunda na
sha maganin bacci me nauyi ya dauke ni, Ko da safe wayar Jahid ce ta tashe ni, yana tambayar
jikin Baby dalili shima Amjad tun asubah ya kira shi a waya shi ya dauka ma ko har ya samu
labarin abunda ya faru yake fad'a masa a jikin da sauki Amjadu ya shiga mamaki sosai ya kira
wayar Jahid din ne a matsayin sa na mskusanci ga Asma'u ya sanya ta ta maida baby gida
kafin ya dawo domin shi yayi alk'awarin bazai kara kirararn ta a waya ba kawai yaji yana masa
wata magana. Bai nuna bai sani ba sai yayi shiru kawai yana sauraron Jahid, shi kuma ya
cigaba da cewa "Hakane da ma idan ruwan sama ya daki k'ananun yara zasuyi ta fuskantar
wannan matsala kafin jikinsu yayi k'wari gobe insha Allahu nake so na auna ta sosai saboda ina
gudun nimonia ganin yanda take Jan numfashi da kyar."!
Take ya fahimci inda maganar take wato ruwan sama ne ya doki sweet heart dinsh, babu
walwala a tare dashi yace." Jahid idan na fahimci maganar ka kana so kace min ruwan sama ya
tab'a lafiyar baby Aysha hakane ko.'? Jahid yace." Eh mana ai na dauka ka sani kaima maganar
zakai min." A kaurare yace." Inso in ce dakai ka sanya Asma'u ta mai damin yarinya gida sai
naji wannan mummun labarin daga bakinka Asma'u taje ta dauko min yarinya ba tare da yadda
ta ba shine dalilin kiran da nayi maka, gaskiyar magana Mujahid Dan dai Kaine ina ganin
girman ka a idona amma da sai na dauki mataki kan Asma'u tunda abunda ta shirya min kenan
kan wane dalili zata futa da k'aramar yarinya ruwa ya dake ta, kaga irin sakacin da nake fada
maka ko, ita bata rike kanta ba taya ya zata iya rike wani."!! Ya k'arashe maganar tasa a zafafe!
Jahid yace." Gaskiya bata kyauta ba gani bata gayamin haka ba, amma kayi hakuri don Allah
komai ka gani tsautsayi ne amma tabbas bata kyauta ba. " Cike da takaici yace." Yau kwana
biyu rabona da in ji sweetheart nayi kewayar jiya babu yanda banyi da yarinyar nan ba ta bani
ita muyi hira ta kashe min waya, ni da yarinya ta." Jahid yayi murmushi tare da fadin"Sai kace
Wanda zakayi hira da babban mutum ka kwantar da hankalin ka zaka dawo ka yadda
sweetheart dinka cikin koshin lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke yace." Insha Allah karshen watanan
zan dawo zan je Umara insha Allah." Jahid yace." Alhmdullahi kayi mana addu'ar zaman lafiya
ni da Asma'u da samun zuria mai kyau kasan karshen wayan aka sanya lokacin d'aurin
auranmu." Amjad yaji wani irin fad'uwar gaba ta rikito masa zan can yazo masa a baza ta!
Yace." Jahid yaushe aka sanya rana babu labari."! Jahid yac."Wallahi my friend abun yazo a
bazata kuma a kurararn lokaci Dan har yanzu hankalina ba a kwance yake ba dalili Momyna
bata kaunar auramu da Asma'u, shine nake cikin wani hali shaf na manta ban fada maka ba."
Cikin dakiya da kokarin danne damuwa yace." Na tayaka murna Aboki amma INA baka
sha'wara cewa ka bi umarnin iyaye domun Neman albarkar su, ina ganin tunda Momy tace bata
so kayi hakuri mana ka bari."! Jahid yace." Wallahi nayi kokarin hakan na kasa INA yiwa Asma'u
wani irin so Wanda nakasa gane irin shi ka tayani da addu'ar Neman zabin Allah." Girgiza kansa
yayi yana jin wani daci Cikin zuciyar sa yace." Insha Allah zan sanya ka a addu'a. " Jahud
yace." Nagode my Aboki. " Amjad yayi murmushi tare da fadin. " ka kula min da baby please
kuma ka sanya ta ta Mai da ta gurin granny yau INA son muyi hira da ita please. " Jahid dariya
kawai yake masa sukayi Sallama. "
***
Babu laifi Zazzab'i ya sauka daga kaina sai baby ce take fama sosai Jahid da yazo kafin ya tafi
gurin aiki ya fada min duk yanda sukayi da Amjad din na dinga mamakin rashin kawaici irin
nashi nace"Insha Allah Jahid ko baka fada bs yau din nan zan mai da masa yarinyar gida nagaji
da wannan gorin wallahi,." Jahid yace." Baki fahimce shi bane shima yana da tasa manufar
shiyasa ." nace "Jahid Dan dai abokin ka ne kake kareshi dariya yayi min tare da fad'in"Ya jikin
baby dim nace DW sauki kam hancin ta ya daina yoyo sai dai zazzab'i"Yace shima zai sauka
Insha Allah." Godiya nayi masa shi kuma ya tafi tare da jaddada min in mai da baby gida nace
insha Allahu." Ko da na fadawa Umma abunda mahaifin. Baby yace a kanta sai tace aikuwa
baza a maida ita gida tana cikin wannan yanayin ba, Sam baza a fita da ita ko ina ba
kasamcewar akwai sanyi a gari har yanzu kuma da akwai sauran hadari, shuru kawai nayi ina
jiran Abunda zai biyo baya.
****
Duk abunda yake yi k'arfin hali yake tunda yaji labarin d'aurin auran Jahid da Asma'u ya nemi
nutsuwar sa ya rasa hak'ika al'amarin yazo masa a bazata! Kullum ta Allah kokarin sa ya yakice
yarinyar daga rayuwar sa, abun ya fassakara duk abunda yake mata yana sane yake mata
domin ya kuntata matane suyi fad'an da zai ji tafi ta a ranshi gaba daya amma dake yarinyar
taurin rai ne da ita taki yadda suyi fada da ita sha fa yanzu gani yake babu yadda za'ayi ya auri
Mimi daga baya kuma ya aure Asma'u a da dai yayi niyyar ya hadasu ya aura dalilin son da
yakewa Asma'u, sai bayan ya auri Mimi ne ta koya masa sonta kyawawan haleyen ta suna
burge shi, a wannan zamanin dai samun mace kamar Mimi sai an tona... Yini yayi yana tunanin
Abu d'aya. K'arfe goma na dare dai-dai ya jira granny dake shirin kwanciya, ta dauka suka gaisa
Yace. " Granny bani baby Aysha ko tayi bacci ki tashe ta kinji."" Cike da mamaki tace." Wai kai
baka da lokacin kiran waya ne sai dare."? Yace." Time din nake da sukuni ki bani sweetheart
please."Ya wani marairaice murya. Tsaki yaja tace." Wace baby kuma wacce take gidan
kakaninta." Tashi yayi da sauri yace." Me kika CE Granny. "!? Cewa nayi baby na gidan kakanin
ta, yo ko tans gurina kana tunanin zan tashe ta daga bacci saboda shirmen ka." Kashe wayar
sa yayi ba tare da ya tsaya ya gama sauraron Abunda granny take fada ba.
Wayar Asma'u yake kira, busy yau ma tana waya da wani, zuciyar sa kamar tayi bundiga ya
jefar da wayar kan bed d'in ya dafe kanshi da duk hannunwan shi biyu.
*29/11/2019*
*BABBAN YARO*
*MALLAKAR_BINTA UMAR*
*68*
Yafi Rabin a wa a Zaune a gurin sannan ya mike Cikin mutuwar jiki ya shiga toilet alwala ya
dauro ya fito yana hada hanya, dadduma ya shimfid'a ya fara sallahr nafila cike da Neman zabin
Allah domin shu kanshi al'amarin sa tsoro yake bashi. Komai ya da gule masa lokaci guda,
bayan yayi idar ya jima yana rokon Allah ya kawo masa dauki a rayuwar sa, yaji wani sanyi cikin
zuciyar sa, kwanciya yayi kan daddumar bacci ya dauke shi mai nauyin gaske. Ni kam bayan mun gama waya da Jahid tunani na fad'a mai tsayi zahiri dai gashi mahaifiyar shi
ta nuna bata kaunata karara ko yanzu sai da ya kara fad'a min irin artabun da suke bugawa da
ita kan Dole ya janye maganar saboda ta samu labarin kai kud'in da akayi a family lokacin da
taje gidan buki suka dinga yi mata Allah ya sanya alkairi, sai abun yayi ta bata mamaki sai daga
baya ta fahimta, shine tasa akai kiran sa, ta kare masa tanadi har tana ikirarin zata tsine masa
in har bai janye maganar ba, duk yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta na lura Jahid
idonshi ya rufe a kaina baya tsoron Abunda zai je ya dawo, dole in Sanar da Umma halin da
ake ciki, yanzu jikina ya fara sanyi da al'amarin hak'ika ina son Jahid tsakani da Allah kuma
bazan so ya fad'a cikin halaka ba, tunani na gwara ya hak'ura kawai domin ya samu albarka
iyaye da wannan tunane-tunanen nayi bacci kwata-kwata na manta da Wani Amjad da
damuwar shi. Da safe duk na warware wa Umma abunda yake faruwa tace"Asma'u dama ni
tuntuni sai DW nace ki hak'ura da yaron nan tunda uwarsa bata so kika k'i, kuma kin san halin
Kawun Ku ba kirki ne dashi Yanzu in wata magana ta sake faruwa zasu har gida su ci mun
mutunci ne ki jawo tashin hankali ya kare a kaina da ban ji ba ban gani ba." Shiru nayi wasu
zafafan hawaye na zubo min duk ja rasa wane tunani ma zanyi.. Karar waya ta naji a dakinmu
da sauri naje na dauko ina duba baby dake bacci cikin kwanciyar hankali, INA dubawa naga
jahid din ne ya kira sallama nayi ya amsa murya babu dad'i ya Dora da fadin"Asma'u duk
abunda kike ki aje don Allah ki mai da wa da mutumin nan yarinyar shi, wallahi yai shi ya tashe
ni daga bacci dama ga shi da kyar na samu ya dauke ina fama da damuwa."
Nima cikin damuwa nace"Jahid ka kwantar da hankalin ka dama yau nayi niyyar mai da ita
saboda Umma tace a k'yaleta ne yasa saboda sanyi jiya amma insha Allahu yau zan mai da ita
Nima na huta da jaraba." Kashe wayar nayi a fusace! Ban saurari maganar shi ba. Hakan ce ta
kasance bayan sallahr la'asar Munnu tazo gidanmu nan muka tafi domin mai Da baby kamar
yanda nayiwa Jahid din alk'awari munnu tq kalleni cikin damuwa tace"Asma'u fyskar ki ta nuna
alamun damuwa tabbas da Abunda yake damun ki."! Girgiza kaina nayi nace"Tabbas Munnu
abokin kuka shi ake gayawa mutuwa nan na kwashe duk abunda yake faruwa na fada mata har
irin rashin kunyar da nayi Monye Jahid din sai da na fad'a mata. Munnu ta dinga mamaki daga
bisani tace"Wallahi wasu masu kud'in haka d'abi'ar su take Sam basa son talaka kiri-kiri ta zo
har gida ta ci muku mutumci saboda zubar da girma yanzu kuma idan mukayi aura kuka Tara
zuria tace me? Da aure da mutuwa duk na Allah ne mutane ne basa ganewa wallahi." Nace"Ke
wace shawara kike gani." Tace"Kawai ki cigaba da nan zabin Allah idan da Rabin auran Ku
za'ayi dashi amma ko da wasa kar ki nuna masa kin karaya domun kinga shima yana daurewa
gashi saboda ke ya bujerewa mahaifiyar sa." Da wannan zancan muka isa. Babu walwala a tare
damu muka shiga, Iyami da Granny na zaune a parlor kamar ko da yaushe ta amsa mana
sallama a sake Iyami kuwada saurin ta ta k'araso gurin mu tana fadin "Oyoyo baby kokarin
daukar ta take yi nayi saurin kwantota ta dauke ta tana cilla ta sama, yarinyar ta gane ta sai ta
fara yi mata dariya. Zama mukayi a nutse muka gaisa da granny dake tambayar mu Umma
nace" Tanan k'alau tace ma a gaishe ki da kyau kafin tazo." Granny tace"Ina amsawa
nima...Iyami kawo musu abunci." Tafad'a tana kallon Iyami dake wasa da baby Granny ta karb'i
baby ta nufi kicin, cikin zuciya ta nace yau kam baza muci abincin gidannan ba wallahi Mik'ewa
nayi Munnu ta mike granny ta bimu da kallo tana fad'in"Za'a kawo muku abunci kun mik'e."
Nace"A koshe muke Wallahi." Cikin nazari tace" kamar akwai abunda yake samun Ku kun shigo
babu walwala kinji sakewa Lamar yanda kuka saba, yake kawai nayi nace"granny kenan babu
komai wallahi mu dai mun tafi sai mun sake zagayo wa." Hanyar futa muka nufa Abun kamaer
almara babyta fashe da kuka tana d'ago hannun ta! Granny tace"To maza Ku dawo Ku tafi da
ita gashinan tana kukan rabuwa da Ku
" gaba nayi cikin zuciyata nace yarinyar nan ko kukan me zata yi bai same ni ba wallah" Munnu
CE ta koma da baya ni kuwa tuni na fuce da sauri, ina jiyo kukan ta har waje, ko da Munnu taje
kin yarda tayi da ita sai kuka take yi Granny tace"Asma'u take nema ba ke ba. iyami ta kwalawa
kira tana fadin "Bazan iya da wannan rigimar ba zo ki dauke ta yarinya k'arama da gane
mutane." Iyami ta shigo da sauri ta dauke ta tana rarrashin ta, Munnu tace "Asma'u baby ta
gane ki sosai wallahi har nayi sha" awar Dadyn ta ya Baki tunda kuna kusa in Allah yayi nufin
auran ki da Mujahid." Murmushin takaici nayi nace"Munnu kenan, nasan ko mutuwa zanyi bazai
bani ba, kar ki so kiji yanda nake jin zafi a zuciyata jin kukan da take yi." Munnu tace"Allah ya
kyauta masa amma gaskiya na lura guy nan ya sanja hali da ba haka yake ba." "Hummm!
Munnu kenan dole yayi abunda yake so tunda gonar sa a ka shiga kuma yana ganin ya wuce
komai na rayuwa shiyasa." Munnu tace"Wallahi maganar ki gaskiya ce Allah ya kyauta." Nace
"Ni Abunda yake damuna Abu daya ne aurana da Jahid wallahi yanzu abun tsoro yake bani ina
jin tsoron abunda zanje in Tarar."! Insha Allahu alkairi zaki yadda ke dai ki cigaba da yin
addu'a.'a" nace "Nagode Munnu." Da Wannan hirarar muka isa gida.
*******
Amjad zaune a harami ya d'aga hannunwan sa sama sai kwararo addu'a yake, yana zubar da
hawaye ni kaina ya mugun bani tausayi, ya kai Rabin awa cikin wannan halin kana ya shafa